Chapter 44
Chapter 44
saidai 'yan raunukan da Rahma taji, ya sulaiman ya dubata tareda basu magunguna sai gida. Tunkan su iso gidan yacika da dangi, su Rahma suna shigowa dangi suka rungumesu anata kuka, bayan gama murnar ganin juna Rahma tashige d'akinta tayi wanka tayima Nawal. Aka kawo musu abinci sukaci sukasha magani sai barci. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Haba ummi yazakice bandamu da 6atan su Rahma ba?, 'Yar uwatace fa, Dan ALLAH kibar fad'a kadama wani yaji zata gskyne. Oh da k'yarya nakeyi?. A'a ummi nidai bance kina k'aryabafa. Banza ummi tayi da ita, tajuya zata fita. Safna ta marairaice murya ummi toyanzu mikikeso nayi dazai sakaki farinciki?. Kafin ummi tabata amsa sukaji sallamar baseera. Tarisina ta gaida ummi, cikin fara'a ta amsa sannan tafice. Ummi na fita basira tamatso Kusada safna, k'awata mike faruwane wai naga ummi akanki?. Mtsoooww kibari kawai akan 6atan Rahma ne........ Takwashe komai tafad'a mata. Baseera tazunguri safna kefa banzace miyasa bazakice zakije kizauna da ita harta samu lfy ba, daganan basaiki gwada sa'arkiba kema. Kai hakanefa baseera, wlhy banyi wannan tunaninba ma, duk kaina yakulle baya kawo wuta. Aikin 6urrr inji tusa, kinga tashi maza ki shirya. Gudu gudu sauri Sauri safna tashirya kayan dazasukai fiye da sati d'aya, tad'auki duk abinda zata buk'ata ta shirya sanan sukanufi d'akin ummi. Tana zaune da Alana tana wayane da wata 'Yar uwar tata Dan tana bata labarin 6atan Rahma dakuma dawowarsu yau. Tsayawa sukayi harta gama, takalli safna da akwatin kekuma INA zaki da kaya haka?. Ummi zanje gidan Rahma na zauna danna ringa taimaka mata har jikinta ya daidaita, naga baikamata ace anbarta da dangin mijiba tamkar batada kowa. Baki ummi ta washe ta ce, "kai naji dad'i wlhy safna ALLAH yayimiki albarka, aihaka akeso, kuma tahakane zuminci ke k'ara dank'o. Ki gaisheta muma insha ALLAHU gobe zamuzo mu dubasu. ALLAH yakaimu ummi, saikunzo safna tafad'a tana murmushi. To saimunzo, baseera kigaida mutanen gidan. To ummi zasuji. Safna da baseera suka fito sai gidansu Rahma, sanda suka iso mutane duksun tafi, daga Ammi da inna sai khairiyya da khursiyya suka rage, har k'asa su safna suka durk'usa suka gaida su Ammi. Safna ta ce, " Ammi inasu Rahman?. Murmushi Ammi tayi ta ce, "aii har yanzu barci sukeyi safna, yawajen su Maman taku?. Lfy lau suke Ammi, suma saigobe idan ALLAH yakaimu zasuzo. To ALLAH yakaimu lfy. Inazaku haka da akwati? Ammi tayi tambayar tana kallon safna. Safna tagyara zamanta tana k'ara marairaice fuska tamkar mutuniyar kirki, Ammi dama canayi bara nazo na zauna da ita harta samu k'arfin jikinta, Dan baikamata atakura su khairiyyaba ga bikinsu yana matsowa. Murmushi Ammi tayi ta ce, " lallai kinyi tunani Safna, ALLAH yay miki albarka. Bobo dake bakin k'ofar Rahma yana niyayyar fitowa yatsaya sauraren tattaunawar Ammi da safna. Ransa a 6ace yakalli Ammi suka had'a ido, yaturo baki gaba, murmushi Ammi tamasa tareda yimasa magana da idanu, wai karyace komai. Kauda kai yayi yana d'an sassauta turo bakinsa, shifa wlhy yatsani yarinyarnan, amma shine yanzu za'ace tazauna taredasu mtsoooww yaja siririn tsaki. Takowa yayi ahankali zuwa cikin falon, jin k'amshinsa da takunsa yasaka safna da baseera juyowa, kan ubancan kai, aii ba safnaba har baseera yau saida tashiga rud'ani. Dukda yad'an rame amma k'yawun haibarsa na nan, kuma yak'ara haske sajennan yakwanta luf luf, sai k'amshin turarensa ketashi afalon mai sanyin dad'i, har yazauna Kusada Ammi idon baseera da safna na Kansa, baseera ta ce, "a ranta lallai dolene safna ta haukace,” Ashe haka guy d'in ya had'u masha ALLAHU. Bobo yay d'an guntun tsaki Dan baya son kallo, ganin bazasu daina kallonsaba shikuma sun gundureshi, saiya katsesu dafad'in yakuke?. Dandanan suka dawo hayyacinsu danjin saukar muryarsa mai ratsa jiki da 6argo. Cikin in ina suka gaisheshi, ya amsa da lfy, tamkar yanda yasaba. Khursiyya da khairiyya suka fito saga kichin bobo ya kallesu, harkun mammala abincin?. Ya Abdulmaleek ai yau abinda kafiso muka dafa zakacidai ko?. Murmushi yamusu tareda gyad'a kai kawai. Suma dariyar sukayi suna mai farincikin ganin yayansu yau acikin farinciki, khairiyya ta CE, " Yaya tunda aunty Rahma tadawo yanzu saika Dage dacin abinci kayi k'iba. Harara bobo yasakar musu yana fad'in Ammi wlhy yarannan sun rainani. Ammi da inna suka tuntsure da dariya, inna ta ce, "Abdulmaleek aiko kura da 'ya 'yanta take wasa a daji, ammi ta ce, " wlhy kuwa inna. Ammi takalli su khairiyya ta ce, ''kutaso heebba mutafi gida hakannan ko?, tunda kungama aikin, fuska suka shagwa6e, khursiyya ta ce, "Ammi wai kina nufin harda mu?, harararsu ammi tayi hardaku mana, tunda ga safna nan tazo kukuma basaiku koma gidaba, dama ga hidima fall cikinku, dasafe saikuringa zuwa ko?. Su saima yanzu suka kuladasu safna dake zaune. Ammi takallesu tareda fad'in kuna 6ata mana lokacifa gakuma Deriver yana jiranmu. d'akin Rahma suka shiga sunata zum6ura baki, haryanzu su Rahma barci sukeyi abinsu. Hibba dake barci suka d'akko suka fito, suna son yarinyar sosai, yanzu haka komai NATA Yakoma d'akinsu, har anmaida mata suna Autar Ammi. Har mota safna da bobo suka raka ammi. Bayan su Ammi sun tafi shima bobo ficewarsa yayi batareda yasake ko kallon indasu safna sukeba. Suma cikin gida suka koma suka Shiga d'akin Rahma wadda har yanzu suna barci. Suna nan zaune har aka kira magriba baseera tamik'e zata tafi, bayan Safna tarakata k'ofar gida tashiga adaidaita, baseera tana k'ara jaddada mata karfa tayi wasa da damarta, tayi k'ok'i kimai ta aiwatar yanda yadace. Safna ta ce, " karkiji komai insha ALLAH zanyi k'ok'ari. Okey sainajiki k'awar rai da rai. Dariya safna tayi ta ce, "hakane my sweet baseera, suka tafa mai adaidaita yaja suka wuce. Safna tana Shiga gidan ta Tatar Rahma ta tashi, tayi farinciki daganin 'Yar uwarta danhaka ta rungumeta, aunty safna yaushe kikazo?. Tun d'azun Nazo kina barci ya jikin?. Da sauk'i saidai jikina yana ciwo tayi maganar tana yatsine fuska, to sannu auta cewar safna, kai kawai Rahma tad'aga mata. Ta ce, " aunty safna yasu ummi?. Suna nan k'alau suncema a gaisheki gobe zasuzo, tom ALLAH yakaimu lfy, Yakuma naji gidan shiru?. Kowa yatafi saini kad'ai, Nima zan zauna anan ne harki samu sauk'i. Lah da gsk?. Eh mana safna tafad'a tana murmushi, Rahma tana juya baya safna ta galla mata harara. Itakam rahma dabatasan tanayiba ta rungumeta tanamai farincikin faruwar hakan. Bayan anyi sallar magriba bobo yadawo gidan, kaitsaye d'akin Rahma yanufa, har yanzu suna zaune da safna suna hira, safna tana hirarne kawai amma jitake tamkar ta shak'e Rahma tamutu. Sallamarsace tasakasu d'agowa suduka tareda amsawa, suna had'a ido da Rahma yay mata murmushi, ya jikin? Yafad'a cikin sassanyar muryarsa, Rahma tai k'asa da kai sannan ta ce, "da sauk'i. To Alhamdllh, kinyi sallah ko?. Rahma ta girgiza kai alamar a'a. Miyasa?, kobak'yayine?. Girgiza kai Rahma tasake yi cikeda kunya, mik'ewa tayi tashiga bayin. Harta Shiga bobo yana binta da kallo, saida tashige sannan yajuya yafita. Safna tabishi da kallo zuciyarta na suya, jibi Dan ALLAH yama nuna tamkar baisan da ita ad'akinba, tayi k'wafa da fad'in zakazo hannuna ai. Na CE, " hummm. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Yau kwanan su Rahma 2 da dawowa, dangi kam kullum sunata tururuwar zuwa dubasu damusu jaje, A6angaren bobo kuwa kulawa yake basu ta musamman, dai dai da abinci saiyace shine zai bata abaki, itakuma taita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83