Chapter 11
Chapter 11
ya ce, ''masha ALLAHU, gsky amaryar auta ta had'u....... Isowarsu ta k'atse masa tunani, yayinda gaban Rahma keta fad'uwa azatonta Ya Hamzane angon, kanta na k'asa aunty Ruk'ayya tasakata amotar. Wani k'amshine da sanyi suka bigi hancinta, tashak'a talumshe ido azuciyarta ta ce, ''oh ALLAH, wannan wane irin k'amshine?. K'ok'arin gyara zama tayi saitaji ta dunguri mutum, dasauri tajuyo ta kallesa, yana zaune ak'ame kamar wani jinin sarauta, saidaifa k'amshin amaryar tasa ta narkar da zuciyarsa, saiwani lumshe idanu yakeyi, ahankali yajingina bayansa da kujerar ya lumshe ido. K'irjin Rahma sai dukan uku uku yake, jitayi wani sabon zazza6i yana neman rufeta, dukda kallon fisha tayima angon nata ta tabatar ya had'u masha ALLAHU. YA Hamza dake tada mota ya ce, amaryarmu ykk?. Muryar Rahma na rawa ta ce, "ina yini. " lfy lau, ya fara hidima?." Alhmdllh tayi maganar ahankali. Tad'an kalli gefen Bobo ta ce, ina yini. Dukda yagane dashi take amma yay shiru. Takuma cewa ina yini, sai asannan ya amsa da lfy, ykk?. Kasa amsashi tayi, sai kawai tayi k'asa da kanta tana wasa da zoben hannunta. Sunkusa isa wajen faty d'in Bobo yatashi zaune sosai, wata leda yad'akko agefensa yazaro rafar 'yan 200 guda hud'u yad'ora saman cinyarsa. Rahma data k'urama zonen hannunta ido saikawai taga mutum ya d'oro hannunsa saman cinyarta, gabanta ya ce, "wani Rasss!, fos d'inta yazare data d'ora saman cinyarta ta d'ora hannunta akai. Tabud'e idonta ahankali daga rintsewar datayi, Fos d'in yabud'e yaga 'yan 50 rafa biyu sai wayarta, wayar yaciro yasaka kud'in daya ciro aleda yasa a fos d'in maida wayar yayi zai rufe fos d'in amma tak'i shiga dan tacika dayawa. Ciro wayar yakumayi yarufe fos d'in yad'ora mata saman cinyarta, wayarta kuma yasaka cikin aljihun suit nasa, nufinsa idan sunje angama taron talik'a kud'in saiya bata. Itadai Rahma batace masa k'alaba Dan batasan miyayi da fos d'inba. Har gaf da d'akin taron ya Hamza ya faka, yafito yabud'e musu k'ofa, asanyaye Rahma tafito, duk kunya ta isheta tasaba duk inda zataje saida k'aton hijjab, amma yau gata kod'an gyale babu, sauk'intama Rigar bubuce kuma tabud'e bata matsetaba. Su yaya Ishaq suma fitowa sukayi daga motarsu, suma kayansu iri d'aya dana ya Hamza. Suma sun yaba da amaryar k'anin Nasu sai masha ALLAHU suke jerowa. Ya Hamza yashiga d'akin taron yasanar da MC amarya da ango sun iso. Aiko nanfa yafara kayayato, falon taron yay tsit anzuba ido aga amaryar Bobo d'an gayunnan maiji da kansa. Ahankali Bobo yatako har zuwa gaban Rahma data duk'ar dakai k'asa kamar ace ar ta gudu. Ahankali ya ce, "bismillah muje. Jerawa sukai suna tafiya ahankali har cikin wajen, bayansu kuma su ya Sulaiman ne suka take musu baya. Tunda suka shiga wajen taron jikin Rahma yay sanyi, Dan ita irin mutanan ne masu tsoron shiga mutane, dandanan tafiyarta ta sauya, sai wani sassarfa takeyi. Raf raf raf raf!! d'akin taron yad'auki tafi lokacinda Rahma ta hard'e taigaba kamar zata fad'i, da sauri Bobo yaruk'o hannunta yana fad'in ezeee madam. Ajiyar zuciya tasauke danjin bata fad'iba, a u okey?, yafad'a yana kallonta. Kai tad'aga da sauri. Tom kiyi ahankali plzz karki ji ciwo. Ngd tafad'a tana kallon k'asa, to muk'arasa ya nuna mata hanya. Ahankali suka taka zuwa inda aka tanar musu, sunbirge mutane gsky saidai mak'iyi, kowa fad'i yake sun dace da juna, Ammi saijin dad'i takeyi Dan harga ALLAH Rahma tashiga ranta. Suna zama DJ yasaki wak'ar because, i luv u. Wannan wak'ar Bobo ce dayake bala'in so sosai, ya Hamza yabada wak'ar asaka Dan Bobo. Aikuwa sai sakin lallausan murmushi yakeyi danjin dad'in wak'ar. Masu hotuna kam sai aikinsu suke, itadai Rahma kanta yana k'asa tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren Bobo. Bayan wak'ar tak'are aka fara gudanar da abinda ya tara mutane. Ammi tayi bayani da godiya ga d'unbin mutane dasuka halarci mother's Night d'in, sannan taima amarya da ango fatan alkairi. Rahma taji dad'in bayanin ammi itada danginta, wannan kad'ai ya isa yanuna mata dangin mijin nata suna sonta. Ankira amarya da ango filin rawa, shuru sukayi kamar bazasu tashiba, kowa da abinda yake kitsawa a zuciyarsa, saida mc yasakeyin magana sannan suka mik'e ahankali. Afilin rawar suka tsaya k'ik'am babu mai motsi balle rawa, itakam Rahma dama bata rawa da dadai safan ce kam wannan gwanace. Bobo yafiddo rafar kud'i yafara lik'ama Rahma idonsa k'yam akanta, itakam kanta na k'asa, Dan danan guri yad'au ihu da tafi, jiki a sanyaye Rahma itama tabud'e fos d'inta danufin d'akko 'yan wazo d'inta saitaga kud'i dayawa. d'agowa tayi ta kalli bobo, shikuma yad'aga mata gira kuwa, da sauri tamaida kanta k'asa, yamatso da bakinsa wajen kunnenta cikin muryarsa mai taushi da laushinnan ya ce, "ko bakisone?. Ajiyar zuciya ta sauke itama ahankali ta ce, " ngd sosai". Hak'k'ine akaina aii yafad'a idomsa agefe kamar bashi yayi maganarba. Batace komaiba itama tazaro kud'in tafara lik'a masa gashi yamata tsawo, amma ahaka taringa masa lik'i ihun mutane da tafi yak'aru, masu hotuna da video sai haskasu sukeyi. Ammi ta taso itama ta rungume Rahma tana saka mata albarka, tafara lik'ama Rahma 'yan dubu dubu, (abin na manyane masu karatu), Bobo ma yakoma lik'ama Ammi sai murmushi yake saki itama Ammi haka, Rahma kam kanta ak'asa itama tana lik'ama ammi. Su yaya sulaiman ma suka taso, dandanan gurin ya kaure da lik'i kamar ba'asan ciwon kud'iba, k'awayen ammi da danginta duk suntaka rawar gani, hakama dangin Rahma ba'a barsu abayaba, kai wannan taro ya k'yatar masha ALLAHU. *_(can na hango Aunty bilyn Abdul tana lik'a 'yan naira 5π€£ππ€, ba ruwana kartajini)._* _karfa kuce nina fad'aπ€Έπ»ββ_ Sai k'arfe 11:30pm taro yatashi lfy, kowa yafara k'ok'arin tafiya, Rahma duk barci yacika mata ido, cikin mota take zaune tana jiransu bobo sugama sallamar bak'i shida yayunsa, saida kuwa suka gama sannan suka shigo, yanzu kam wani d'an uwansu bobone zai maidasu ba ya Hamza ba, su ya Hamza matansu suka d'auka da yaransu sukayi gida. Rahma ta kifa kanta kan cinya harta fara barci, kallonta kawai yayi baice komaiba, shifa koma sunanta bai saniba, bai tada itaba har sukaje gidan. Yay shiru yana tunanin yanda zai tasheta. Lukman ya kallesa Bobo kona baku gurine?, a'a malam wane kabamu guri gida zata shiga, ita barcima takeyi. To ka tada ita dare na k'arayi shabiyu saura fa. Daurewa yayi yad'an ta6a bayanta, ko motsi batayiba, yakuma d'an bubbugawa, firgigit ta tashi da addu'a abakinta, tad'an kallesa, shima idonsa na kanta, munzo yafad'a akasalane. d'auke kanta tayi tabud'e motar, saida safe tafad'a cikin muryar barci, harta rufe motar Lukman ya ce, "haba malam aii ka rakatadai kasani kotanada magagin barci. d'an tsaki bobo yayi shima yafito, harta fara tafiya yad'an hanzarta ya cimmata, dama ita kad'ai mai gadi yake jira Dan haka k'ofar abud'e take. Dariya Lukman yashek'e da ita, sai Bobon Ammi yafad'a harda dukan sitiyari. Har k'ofar falonsu yarakata, saida takama k'ofar zata bud'e sannan ta ce, " saida safe. ALLAH yakaimu yafad'a yana juyawa. Amota yasamu Lukman yashiga gaba suka wuce gida suma.......... _masoya I luv u._ [11/12, 2:17 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ» β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* βπΏ _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* *_"dolene na gaisheku Nice Hausa novels, mungode sosai da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83