Chapter 15
Chapter 15
saitake mamakin halin Abdulmalik, yana cikin damuwa amma bazaiyi aureba sai ammasa ta k'arfin tsiya, shidai halinsa daban acikin 'yayanta, ALLAH ma kad'ai yasan tun yaushe yake acikin wannan halin. Afili kuma saita girgiza kai tana fad'in kidafa masa to dare nak'arayi. Bayan fitar Ammi Khursiyya tadafa Lipton tanata mita, ta matsa masa lemon tsamin sanan tasaka a k'aramin tire tafice zuwa d'akinsa. Akwance tasameshi rufda ciki, sanye yake cikin kayan barci. Yaya gashi tafad'a tana ajiyewo. Baice mata k'alaba bare ya d'ago. tajiye tafito cike da haushi, babu yanda za'ayi yasaka ka aiki kaimasa yaymaka godiya bayan kagama, duk cikin yayinyunsu shine halinsa da ban, duk masifar ya ishaq yafi yaya bobo sauk'i. Shikam kobayan fitarta yakai Monti Biyar sanan yatashi zaune yana matse fuska. Dukda turirin da shayin yakeyi saboda zafi, haka yayta shansa yana cije le6e, yana gamawa wata zufa tafara karyo MASA adukkan sassan jikinsa. Kwanciya yayi ahankali yana sauke numfashi, bayan wani lokaci yasamu nutsuwar sarayar ciwon nasa. Kwanciyarsa yagyara barci yay a won gaba dashi. *_washe gari_*. K'arfe 10:30am aka fara gudanar da sisters day aharabar gidan, masha ALLAH komai tayi k'yau, yaudai basuga idon bobo ba, yana d'aki kwance barcinsa yaketa kwasa na gajiya. Sisters day kam yabada ma'ana, amaryama yau tasha k'yau, su khairiyya sun raba k'yaututtuka taro yatashi lfy. 2:00pm aka gabatar da walima, mutane suka fara kama gabansu, wasuma bak'in sun wuce tun safe, wassu kuma sai gobe idan ALLAH yakaimu. Rahma dum jikinta yayi sanyi tunda aunty ummy tashigo tace ta shiraya da angama sallar isha'i za'a mik'ata gidanta. Kallo ihsan dake zaune Kusada ita tayi, ihasan wai ina wayatane?, kwana biyu wlhy bangantaba nazata tana wajenki. A'a wlhy wayarki bata a wajena, amma bari akira muji. Kiran wayar suka farayi.... Bobo nazaune ad'akinsa yana danna laptop yaji wayar Rahma dake caji tana wringing, kamar bazai dubaba saikuma yamik'e yad'auka. Ana d'agawa ihsan tamik'ama Rahma wayar tana fad'in and'aga. Cikin sanyinta ta ce, "Assalamu alaikum. Lumshe idanunsa yayi danjin sassanyar muryarta. Wa'alaikissalam ya amsa cikin nutsuwa. Gabantane yafad'i danjin murayarsa, taganeshi sarai amma saita dake ta ce, " Dan ALLAH wanene?. Jin haka shima saiya basar ya ce, "kema wacece?. Mai wayarce, Dan ALLAH ya akayi tazo hannunka?. Murmushi yayi tareda shafa gemunsa na gayu, ya ce, " mijinkine, nasamu wayar ahanunkine kuma. Ajiyar zuciya ta sauke, muryarta nad'an rawa ta ce, "to shikenan. Yanke wayar yayi kawai yana murmushi shima. Ihsan dataji komai bata Neman k'arin bayani dantaji komai. Screen d'in wayar yadasama ido, photon Rahma ne ajiki da Safna, sunyi masifar k'yau ahoton. Tunda wayar tazo hannunsa baita6a tunanin dubataba, Dan tunda ya ajiye baibi takantaba, yau yaji tanata kukan k'arewar caji shine yasaka mata cajin. Yad'an lumshe idon yabud'e akan wayar, kowacece wannan kuma?, yafad'a aransa. K'ila yayartace, (wadda tace bata sona kenan?) Afili yay maganar, bakinsa yata6e yana k'arema safna kallo, tabbas tafi rahma k'yau, amma Rahma tafita kwarjini da fuskar kamala. Bakinsa yak'ara ta6ewa yamaida wayar a caji. Hawowa gadon yayi yacigaba da aikinsa. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Bayan Sallar isha'i Rahma tagama shiri cikin kyakykyawar Shiga ta material siket dariya, tayi k'yau sosai kuwa, sai tashin k'amshi turare takeyi. Haka wasu k'alilan daga cikin danginsu, dakuma su aunty Rasheeda sukai mata rakkiya had'ad'd'en gidan Bobo dayasha gyara tamkar sabo. Idonta na rufe tanata sharar kuka, da tunanin gamonta da ango yau, koyaya zai k'ar6eta kuma?, dukda yanuna mata kulawa awajen taron bikin hakan baya tabbatar mata dazata samu kulawarsa ayayin zamansu. Dan zai iya yuwuwa yayima iyayensa biyayyane kamar yanda itama tayima nata biyya...... Da wannan tunani su aunty Rasheeda sukaimata sallama harda su ihsan suka tafi. Kuka sosai tashiga rabzawa harda shashsheka, tana tausayama kanta da rayuwarta. Amma tana rok'on ALLAH tazama mai hak'uri da juriyar biyayya ga ALLAH da MANZONSA, dakuma iyayenta. Zamewa tayi ta kwanta tana cigaba da kuka maiban tausayi da tsuma zuciya. .*......*.......*........*.....*. A6angaren Bobo kam yana d'akinsa harya kwanta hankalinsa kwance. Ammi takalli agogon falon karfe 9:53pm amma har yanzu Bobo bai fito yatafi gidansaba. Mik'ewatayi ta haura saman Dan gidan mutane sun ragu sosai. Kallon mamaki tabisa dashi. Shima yad'ago yana kallonta, Ammi na lfy kuwa?. Lfy lau, mikakeyi har yanzu baka tafiba?. Cikin mamaki ya ce, "Ammi ina kuma zani?. Gidanka mana. Gidana kuma?, Ammi canakefa sai gobe?. Harararsa tayi, cikin d'an fad'a ta ce, " tunda d'azu su Rasheeda suka dawo daga rakkiyar matarka, amma kananan zaune, katashi katafi gidanka anbarta ita kad'ai, nasan tanacan atsorace. Bata jira amsarsaba tafice afisace. Ajiyar zuciya yasauke yana turo baki gaba kamar wani k'aramin yaro. Haka yatashi ya canja kaya kamar zaiyi kuka Dan haushi. Farar shadda yasaka sai maik'o takeyi, yad'ora jar hula da silifas ja mai k'yau, turare yafeshe jikinsa dashi, sannan yajawo jakar lop-top d'insa yasaka duk abinda zai iya buk'ata na 6angaren aikinsa, yakashe kayan wutar d'akin yafito sai zabga k'amshi yakeyi. Ammi yatarar afalonsa tana jiransa, ganin ranta ad'an 6ace yasa yasaki fuska, cikin murmushi da zolaya ya ce, "Ammi na nayi k'yau. Itama fuska tasaki tana kallonsa, ta ce, " masha ALLAHU Mukarram d'ina kayi k'yau sosai, ALLAH yaymaka albarka kaji, yabada zuri'a tagari, ya albarkaci wannan aure. Biyayyar dakake mana ALLAH yasa kaima 'ya'yanka suyi maka. Ammin Ammi na ngd sosai da addu'arki gareni, bari naje wajen appa namasa sallama ina baby mutafi?. A'a ita ba yauba, sai bayan sati d'aya tukkuna. Ammi saboda mi?, cikin shagwa6a yay maganar. Dariya ammi tayi ta ce, "shagwa6a66ena sai angama amarci tukkuna, idan d'iyata tagama hutawa da gajiyar biki saikazo kad'auki Nawal d'in. Shike nan ammi, amma....... Katsesa tayi da fad'in kaga jekayima Appanku sallama dare nak'ayi. Haka yahak'ura yanufi d'akin Appa, bayan sun gaisa yaymasa nasiha sosai da saka masa albarka sannan yafito yatafi. Mota yashiga yabar gidan cike dakewar iyayen NASA. Awajen wani gasa naman kaza ya tsaya, yasayi guda biyar sai k'amshi sukeyi, yasayi kayan fruit dayawa yanufi gidansa zuciya acinkushe da tunani kala kala........... *_" Alhmdllh. inaga 'yan uwa yakamata mudakata anan sai bayan sallah, gobe idan ALLAH yakaimu kowa zai nemi k'unshi da k'itso babu time d'in karatu, jibima haka ga aiki tunda daren sallah ne, Dan haka muyi hak'uri zuwa bayan sallah idan ALLAH yakaimu lfy."_* _ina muku barka da sallah, inakuma baku hak'uri da godiyar had'inkai da kuka bani, ngd sosai, inaga ni anan zan barku Dan bayan sallah zan koma gida, gashi wayata ta lalace bana charting yanzu, dasai nacigaba damuku, dama da wayar aunty Billy nake typing d'in, amma ina rok'on ALLAH yasa tacigaba damuku, dukda naga tanada aiyuka agabanta._ _Na rok'ar muku ita sosai akan taringa muku typing d'in ko babu yawa sosai, Dan wlhy buk d'in yahad'u sosai masu karatu, shiyyasa Nima narikice nahau yimuku copy, lagwadar labarin nagaba, Dan akwai cakwakiya sosai acikin Novel d'in, kardai nacikaku da magana ALLAH yasa tayi muku._ _Wanda na 6atamawa Dan ALLAH ya gafarceni nabarku lfy._ *_taku Marak'isiyya ibraheem musa._* Luv u oll. By βπ»βπ»βπ»βπ»masoya, ALLAH yahad'amu da alkairinsa. Ngd. Aunty bilyna gareki, Dan ALLAH kicigaba da gashiππ»ππ»ππ»ππ»plzzz. [11/12, 2:21 PM] mrs bilkisu: π©π»βπ»typing........ β£ *_ABDUL-MALEEK_*β£ _β’{BoBo}β’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* π€ *_Assalamu alaikum, ina mik'o muku sak'on barka da babbar sallah, ALLAH ya maimaita mana, muga ta bad'in bad'in bad'ad'a, saidai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83