Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Wasukam kishine yacika zuciyarsu, Dan sundad'e suna nuna masa so yana basarwa saboda jin kai, wasukam har iyayensu saida sukai masa talla amma ya ce, "kai kasuwa. Cikin gidan yashiga Dan soyake ya d'auro alwala, babban falon k'asa cike yake dam da mutane, yanashiga suka hau tsokanarsa wai angon k'amshi angon k'amshi." " aransa ya ce, "za'a gogudai". Haka yagaida wad'anda zasu iya jinsa ya haye sama d'akinsa bayi yashiga yad'auro alwala yafito, su aunty Sameera ma duk sunshigo ciki. Yazo zai fita Ammi ta ce, " mukarram!. "na'am Ammi ya amasa yana juyowa, k'arasowa tayi Inda yake takama hannunsa suka fito. Wani d'an lungu tajashi ya ce, " Ammi lfy dai ko?. Lfy lau mukarram dama tambayarka zanyi d'azu kuwa kaje gidansu amaryar taka?. Gefen wuyansa ya sosa, afuwa ammi, wlhy abubuwane sun mana yawa. Kanta ta girgiza haba mukarram ya inamaka kallon mai hankali amma kanason 6ata wayonka?, babu dad'ifa, iyayen yarinyarnan bazasuji dad'iba ace bakaje gidanba tunda aka fara maganar aurennan, shin kai zakaso ayima su khursiyya hakane?. A'a wlhy ammi bana fata, amma Dan ALLAH kiyi hak'uri nayi kuskure, insha ALLAHU zan bata hak'uri anjima idan munje mother night. To shikenan ammadai Baka k'yautaminba, Bahaka nasoba. Tom kiyi hak'uri Dan ALLAH. "Ya wuce." Yauwa ammi an kar6o d'inkin Nawal kuwa?, wlhy namanta shaf, kuma harda wanda zata saka anjima. Eh khairiyya ta amso d'azu kafin sutafi wajen kamu. Yauwa harnaji dad'i, bari naje sallah ammi har an tayar inagama su yaya sun wuce. To saikun dawo. Masallaci yanufa ammi kuma takoma ciki. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Anayin Sallar magriba Safna ta sid'ad'e tabar gidan, sai gidansu kamal, acewarta bazataje wajen wani mother Night ba, saikuma tana zuwa gidan ta tarar dasu Ameera suna shirin zuwa harda momynsu. Dayake momynsu kamal tasan komai Dan baba abubakar yasanar da ita, (k'anin Abba ne, kuma mahaifi gasu Br kamal abokin aikin bobo) batace mata komaiba itama, safna tashige d'akin Ameera tayi kwanciyarta, sukuma suka nufo gidansu Safna d'in, akabarta itakad'ai agidan sai 'yan aiki. Rahma ta farka bayan sallar magriba, kasancewar tana fashin Sallah saikawai aunty Madeena matar ya muneer tasata tayi wanka. Mai kwalliya tafara aikinta na fente fuskar Rahma. Itadai Rahma bin kowa kawai takeyi da ido, kad'an kad'an saita share hawaye, saida mai kwalliya tamata magana sannan ta tsagaita da kukan aka tsantsara mata kwalliya ta d'aukar hankali. Wani doguwar riga bubu aka bata tasaka, tawani material Orange da d'igo d'igon lemon green ajiki, aka nad'a mata lemon green d'in d'ankwali, sai fashion na 'yankunne da sark'a maid'an tsawo, tasaka bak'ar coka wadda ta manne awuyanta. Yasalam nafad'a yayinda naga amaryar k'amshi tafito ras kamar ba Rahman ummiba, tayi k'yau masha ALLAHU. Fos aunty hafsat tabata, wadda itama takasance lemon green, sannan tasaka takalmi lemon green shima mara tudu. Hummm komaifa yaji ajikin amarya. Ihsan k'anwar Br kamal tamatso kusada ita, kai Rahmana kinyi k'yau wlhy, na tabbata angonnan yaganki saiyace gwamma da akayi, wlhy saikin susutashi. Basma ta ce, "ni tsorima nake karya rikice yace daganan sai gidansa. Duka Rahma takai musu, cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka ta ce, " yan iska kawai, aii dama halinku d'aya. Dariya suka shek'e da ita harda tafawa. *_Bobo_*.......... *_godiya muke masoya, ALLAH yabar zuminci._* [11/12, 2:16 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’» ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _{Bobo}_ _Story & editin_ *_Aunty Bilyn Abdul_* ✍🏿 _Written_ *_Marak'isiyya_* _hak'in mallaka_ *_Aunty Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Bily giro_* *_"wannan page d'in nakine Maman useey alkairin ALLAH yakaimki har gidan baban useey, ni marak'issiya naji sak'onki wajen aunty bilyna."_* Luv uπŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ‘ŒπŸΌ 1⃣9⃣&2⃣0⃣ A 6angaren bobo kam bayan sun dawo daga masallaci aharabar gidan suka sake zama, hira aketayi da barkwanci, saida aka k'ara kiran sallar isha'i sannan suka mik'e, masu sake alwala suka sake, wadda tasu bata karyeba sukayi gaba. Ana idar da sallah suka shigo gidan, shiri suka fara, kowa yana k'ok'ari kada time ya k'ure. Bobo kam wanka shima yashiga, yafito d'aure da tawul fari a k'ugunsa, k'arami kuma yana goge kansa zuwa fuska da wuya har k'irjinsa zuwa k'asa. Wurga tawul d'in yayi saman kujera, yaja kujerar madubi ya zauna, mai yafara shafawa, hardasu farar fauda afuska, yashafe kansa da mai mai k'amshi har zuwa sajensa dad'an gemunsa na gayu, yasa kum yak'ara taje kansa da gemunsa, sannan yay amfani da burosh wajen kwantar da sajensa, yako kwanta luf sai walk'iya yake da tashin k'amshi. Turarurruka yad'auka kala kala yafeshe jikinsa, sannan yanemi guri abikin gado ya zauna batareda niyyar saka kayaba. Atsakar gida kam mutane harsun fara fita, Dan kowa bayaso atafi abarsa, dandanan motoci suka fara d'aukar mutane, kowa ya cakire da kalar kayan dayakeso, manyan iyayene kawai suka saka wani Dan datsetsen less fari tas, suka nad'a Orange d'in gwagwgwaro, masha ALLAHU abin sai Wanda yagani. Su khairiyyama ba'a barsu abayaba, sunci ado da dogayen riguna na lemon green d'in material sunyi k'yau masha ALLAHU, suda matansu ya sulaiman duk iri d'aya suka saka. Nawal ma anshiryata cikin farin less irinnasu Ammi, doguwar riga aka mata, aka nad'amata Orange d'an kwali, yarinyar tafito d'as kamanninta da bobo ya k'ara fitowa. Tare suka shiga Mota da Ammi. Ya Hamza yafara waige waige, cikin Jan tsaki ya ce, "wai mi Bobo yakeyine tun d'azu yafasan saiyaje sun taho da amarya, gasu ammi harsun wuce. Ya is'haq shima yay tsaki ALLAH yaron nan d'an wulak'ancine, Hamza kaje d'akinsa kaga miyakeyi?. Ya Hamza yanufi d'akin Bobo, ya Sulaiman dai baice k'alaba. La'ilah Abdulmalik minene haka?. Bobo dake zaune yana latsa waya yad'ago yana kallon ya Hamza daya had'e cikin Farin Suit sai k'amshi yake. Minayine yaya?. Bansaniba, dallah malam kana 6atamana lokaci katashi kasaka kaya, su Ammi harsun wuce. Baki yaturo kamar wani k'aramin yaro, nikam wlhy ya Hamza barcima nakeji. A'a kakan barci kakeji ya Hamza yafad'a ahasale, wlhy zankira ya Is'haq. Da Sauri bobo yamik'e, yafara saka gajeren wando da bes, ya warware had'ad'd'un Suit lemon green sai d'aukar ido sukeyi. Wandon yafara sakawa da Orange d'in Riga mai dogon hannu, ya tsuke k'ugunsa da belt, ya Hamza yad'auki nektayit d'in green yafara saka masa, shi abumma dariya yabasa, amma baiyi dariyarba gudun kar ya Hamza yasake k'uluwa. Da taimakon ya Hamza yasaka rigar Suit d'in, yafara saka botiran ya hamza na gyara ma kwala d'in. Takalmima saida ya taimaka MASA yasaka, sannan yak'ara feshe jikinsa da turare, yad'auki wayarsa d'aya yazura a aljihun Suit d'in, suna tafiya yana d'aura agogo. Na ce o'o me bobon Ammi sai a slowly. Saida ya Hamza yaga yashiga mota a baya, sannan shima yashiga mazaunin direba Nasiba d'iyar k'anwar Ammi na gefensa. Suma su ya is'haq suka tada mota, suna gaba su bobo na bayansu har anguwar su Rahma. Ak'ofar gida suka faka, ya Hamza yafita shida Nasiba har cikin gidan suka Shiga sukace afito da amrya ango yazo. Gaban Rahmane yafad'i Ra's, jitake tamkar tafasa ihu, kowacce irin tarba angon zai mata ta tanbayi zuciyarta?. Batada mai bata amsa, tana cikin zancem zuci aunty Ruk'ayya ta ce, taso Rahma angonki yazo. Jitake tamkar ta ce, bazataba amma yazatayi. Haka aunty Rukayya takamo hannunta sukayo waje, dama dayawan mutanen sun tafi sai k'alilan suka rage. Kowa yashiga mota amarya kawai akejira. Ya Hamza yabud'e d'ayan gefen da Bobo yake zaune Dan ganin amarya tafito. Azuciyarsa

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});