Chapter 63
Chapter 63
tayi, tashare hawayenta da handky d'in. Gaba tayi yana binta abaya gabad'aya saiyaji tabashi tausayi Dan baiyi tunanin zatayi sanyi dawuri hakaba. Cak safna tatsaya tanabin mutanen Dake tsaye da kallo a harabar gidan d'aya bayan d'aya. Da Rahma suka fara had'a ido, tunda take bata ta6a ganin 'Yar uwarta Rahma hakaba, ta tamke mata fuska tamau kamar batasan miye dariyaba arayuwarta, juyawa tayi da kallonta ga sauran saitaga ya ishaq da matarsa ya Sulaiman da mayarsa ya Hamza da matarsa, wannan ya tabbatar mata sunfitone dazummar tafiya k'ila anata Neman bobo, gaba d'ayansu takula kallon tuhuma da tsana suke mata, k'asa tayi dakanta idonta cikeda hawaye, batason su maidata ruwa, tanason kowa ya fahimceta kuma ya k'aunaceta, juyawa tayi ta kalli bobo, shikam hankalinsa kwance yake, Dan fuskarsa da murmushi ya ce, "oh kunata jirana ko?, bara nama su Ammi Sallama mu wuce....... Baijira amsar kowa acikinsuba yayshige warsa falon. Sum sum safna itama tayi yunk'un tafiya Dan tsorata da kallon tsana dasuke mata kuma harda 'Yar uwarta a ciki, da Sauri aunty Sameera tayi yunk'urin Tarar safna amma sai Yaya ishaq yad'aga mata hannu alamar tabarta. Ganin haka yasaka safna saurin shigewa falon sukaci karo da bobo dake fitowa, kallonta yayi d'an murmushi ya ce, " karfa komai yadameki nida kaina zan warware musu k'ullin kinji. Kanta ta d'aga Dan koba komai taji sanyi tunda bobo yafara nuna mata kulawa, saida safe tafad'a a sanyaye. ALLAH yakaimu yay maganar yana fita, Itakuma tahaye sama zuciyarta na k'ara k'arfafata akan karta bari dalilin wasu tubanta ya ruguje. Koda bobo yafito saiya Tatar ya ishaq nagaya musu karkowa yatada maganar sai bayan biki, suna ganinsa kowa yagyara tsayuwarsa kamar basa maganar komai. Shima bai nuna musu yaji komaiba yabasu hannu sukayi musaBaha kowa yashiga motarsa, hannun Rahma Yakama saita fisge.. Cikin d'an mamaki yakalleta ta kauda kanta gefe, k'ara damk'ar hannunta yayi yatura amota, Duk abinda ke faruwa 'yan uwansa suna kallonsu amma babu Wanda yay yunk'urin yin magana. Yana turata amotar yamaida yarufe, shima yazagaya yashiga suka fice kowa Yakama hanyar gidansa. Tunda suka fice agidan Rahma tafara shashshekar kuka, baice da ita komaiba dukda kukan NATA na ta6a zuciyarsa, tsayawa yayi wajen wani gashin kaza yasaya sannan yadawo motar, gefen Rahma yakalla saiyaga tayi barci, girgiza kai kawai yayi yatada mortar yay gaba. Bayan sun gaisa da maigadi yashiga cikin gidan yay fakin Inda yadace, baitadasuba sai kawai ya d'auki Nawal yakai cikin gidan, yadawo Yakuma d'aukar Rahma, yana tafiya yana kallon fuskarta daduk yayi jurwayen hawaye, lallausan murmushi yasaki ahankali ya ce, "my Nusfulhayat sarakan kishi, Ashe kema rigimammace?,...da wannan tunanin yakaita d'aki itama, yadawo yakwashi tarkacensa yay ciki. Bai tadasuba amma cikin dabara yasauya musu kayansu zuwa na barci, yamik'e yanufi d'akinsa, shima wankan yayi sannan yazauna yaci naman ya k'oshi yad'ora da ruwa mai sanyi, yay hamdala ga ubangiji ya mik'e Yakoma d'akin Rahma. Shima gadon yahaye yakwanta a bayanta tareda rungumeta, hannu yakai danufi shafa fuskarta amma amamakisa sai yaji hawaye sha6e² wasu na korar wasu. Tashi yayi zaune ya kunna fitilar d'akin yana mai kallon fuskarta, yakai tsawon minti 6 ahaka, amma har sannan kukan takeyi kuma idonta arufe ruf. gyarama Nawal kwanciya yayi, itakuma Rahma yad'auketa cak yay waje, duk abinda yakeyi tana jinsa amma tak'iyin koda motshin kwarai. Koda ya direta asaman gado saiya kuma dawowa yakashema Nawal fitila yasake yimata addu'a, Yakoma Inda yabarta anan yatarar da ita, yagirgiza kai kawai yakashe fitilar tareda hayewa gadon. Jawota yayi jikinsa yarungume, cikin taushin murya ya ce, "my Nusfulhayat!. Shiru Rahma tayi kamarma batasan da wata halittaba awajen, yakira sunanta yakai so hud'u amma ko motsi batayiba, ajiyar zuciya ya sauke tareda k'ara k'ank'ameta ajikinsa yana aika mata da wasu sakwanni cikin nutsuwa da kwarewa. K'arfin kukan Rahma ne yak'aru, tad'an fara mutsu mutsu ganin haka sai kawai ya manne bakinsa da NATA........ Hummm saida safenku bobo. Washe gari tunda yadawo sallar asuba bai Tarar da Rahma ad'akin saba, yata6a k'ofar d'akinta yaji gam. Kyaleta yayi yatafi d'akinsa yakwanta. Rahma kam tana zaune tana jinsa, saida taji shiru alamar yakoma d'akinsa sannan tafito tahau hidimar gyran gidan da had'a breakfast, fuskarta dukta kumbura saboda kukan datayi, yanzun haka tana aikinne babu ko d'igon walwala atattare da ita. Bayan ta kammala aikin tsaf tayima Nawal wanka tamata shirin makaranta, itama wankan tashiga, batawani dad'eba tafito, 'Yar kwalliya tayi cikin atanfa zani da riga takama hannun Nawal suka fito falo. Bayan sun hau dinning ta had'a musu breakfast, Nawal ta kalleta cikeda shagwa6a momyna ina papana?. Kallonta Rahma tayi da zummar mata magana saiga bobo yafito cikin shigar gayun zamani ajin farko. Dukda tana fushi dashi ita kanta saida ta yaba, kauda kanta tayi daga kallonsa, yad'an ta6e bakinsa afili ya ce, "gulma. Tana jinsa kuma tasan da ita yake amma ta share kamar batasan yana yibama. Sumbatar kumatun Nawal yayi, itama yabata nasa tayimasa, ta gaisheshi, fuskarsa cikeda murmushi ya amsa, yak'arasa inda Rahma take, muryarta can k'asa ta ce, " ina kwana?. Bai amsaba saida ya sumbaci kumatunta, acikin kunnenta ya CE, "inafata kintashi lfy?, sarauniyar zuciyata. Batako kalleshiba tacigaba da bama Nawal break abaki. Shima baikuma cewa komaiba yad'auki cokali yasaka a abincin nasu yanaci, shayin gaban Rahma yajanyo yafara sha, yitayi kamar bata gansaba har suka kammala suka mik'e. Yauma saida suka fara ajiye Nawal a school sannan yakaita gidan Appa, yanda tashareshi babu magana shima haka ya shareta, saidaifa idan yafaki idonta saiya kunshe baki yana dariyar mugunta, itadai batamasan yanayiba. Agurguje ya gaisa da mutane yafice Dan zuwa office, bayaso ya had'u da yayyensa ko d'aya. Gaba d'aya yinin Ranar haka Rahma tayisa sukuku babu walwala, kuma ko kad'an bata kula Safna bare shiga sabgarta. Dukda Safna bataji dad'in hakaba amma taso ace Rahma ta fahimceta, saidai zatayi hak'uri har shi dakansa ya kwance kullin kamar yanda yagaya mata ajiya. Ammi taso fuskantar wani Abu amma hidimar saukar bak'i ta d'auke hankalinta gabad'aya, saidai dukda haka saida ta tambayi Rahma gameda kumburin fuskarta, sai Rahman tace tayi zazza6ine jiya da daddare. Ammi Tamata sannu dukda bata yarda da abinda taceba, amma tabar komai sai zuwa bayan biki. *_4:15pm._* na yamma aka fara gudanar da kamu wanda ya k'awatar da jama'a, amare sunsha k'yau masha ALLAHU kamar kasacesu ka gudu, dangin angunan sunzo kuma suntaka rawar gani ta burgewa, taron yakasance na mata zallah Dan haka babu su bobo awajen bama su dawo daga aikiba. Can na hango Rahma tasha k'yau cikin doguwar rigar material blue sun nad'a farin d'ankwali, ankone itada matan su ya Hamza, sunyi k'yau sosai dukda dai yau Rahma bata cika walwalaba amma tana iyakar k'ok'arinta Dan ganin tarage damuwar fuskarta. Abinda yak'ara mata dad'ima shine zuwansu Basma da ihsan da aunty Ameera, Anty Naja'atu matar ya Muneer, aunty haleema matar ya Shaheed duk sunzo mata, ganinsu yasakata sakin jikinta tanamai jin dad'in ganinsu. Alhmdllh kamu ya k'ayatar kuma antashi lfy kowa yakama gabansa. Mutane basu ida barbajewaba su bobo suka dawo, rarraba ido yashigayi danson hango matarsa amma yakasa ganinta. K'awayensu khairiyya sai fad'in kai guy d'innan ya had'u sukeyi, wau su khursiyya sumusu jagora wajensa. Khursiyya ta ce, "Ku yanafa da mata wlhy kubari babu ruwana, wlhy ya Abdulmaleek d'an hayak'ine, idanma kuka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83