Chapter 61
Chapter 61
fuskarsa cikeda murmushi, ganin zasu saka rayuwarsa gaba yamik'e ya haye saman benen, aiko suka rakashi da dariya, ya ishaq ya ce, " Hajiya iya kinga kin koreshi?. Isahaqa ai dankar yayi maganane yatashi, nibansan halinwa mai sunan Alhaji yakwasoba?, tunda nake ban ta6a ganin muskilin mutum irinsaba, mifa zan iya k'irga maganarsa mai tsawo danaji atsawon rayuwata, mutum kulum dund'un dunkum, sai murmushi shima idan ya gadamar yi. Dariya aka sakeyi, su ya Hamza suka mik'e suna dariya, suma sama suka haura, cikin dariya da zolaya ya Hamza ke kiran Dund'un Dunkum! Kana inane?. Bobo dake zaune kusada Ammi yaturo bak'i gaba, ammi kingansu ko?, wlhy nasan dani suke. Murmushi Ammi tayi kafin tabashi Amsa su ya sulaiman suka shigo d'akin suna dariya dacigaba dakiran dund'un Dunkum. Ya Hamza ya kalli bobo haba Dund'un Dunkum ya munata kira kaki amsa mana?. Hararsu yayi cikin sigar wasa, ya ce, "halan faratun tsohurcan ce tafad'i sunan nan?. Ammi dake k'unshe bak'i tana dariya ta rankwashi kan bobo, mukarram k'aniyarka wace faratun?.. Uhhhchch bobo yafad'a Dan zafi yana dafe kai, wayyo Ammi ALLAH da akwai zafi. aidama dankaji zafin namaka tayi maganar tana k'ara kai masa wani rankwashin. Da Sauri ya kauce, su ya ishaq suka saka dariya, gefe bobo Yakoma yana turo bak'i kamar wani k'aramin yaro, sai shafa Inda Ammi ta rankwasheshi yakeyi. Sudai su ya hamza dariya suketa masa. Ana cikin haka Appa yashigo d'akin da sallama, duk cikin dariya suka amsa harda ammi, Amma banda bobo dake gefe zaune ya shagwa6e fuska. Tofa dariyarmi kuma akeyi uwa da 'yayanta?, Appa yafad'a yana zama abakin gadon Dan duk su ya Hamza suna ak'asan kafet ne zaune. Bak'i bobo Yakuma turowa ya shagwa6e fuska kamar zaiyi kuka, Appa nifa sukema dariyarnan. Kai kai kowa ya saurara, yazaku tasamin babana a gaba kuna dariya?, haba Ammi harda ke?. Babana zonan naji miya faru?.. Tasowa bobo yayi yazo yazauna kusada k'afafun Appa, yad'ora Kansa bisa cinyarsa, Appa yasaka hannu yana shafa kan bobon dayawani narke kamar yayayye. Babana mikayi ake maka dariya haka?. Appa ba Hajiya iya bace tacemin wai Dund'un Dunkum shine suka tasani gaba da dariya, ita kuma Ammi Dan nacema Hajiya iya 'Yar fara shine tarankwasar min kai, kumafa kaina harya fara ciwo. Shima Appa sunan yabashi dariya wai Dund'un Dunkum, amma saiya gimtse saidai yayi murmushi, yacigaba da shafa kan bobo kaga mukarram d'ina barsu duksai na Rama maka, kowa saimun za6i suna sannan musaka masa. d'agowa bobo yayi yana dariya shima, aii Appa harnama tanadi sunan dazan saka musu sai ranar deener zan fad'a idan za'a gabatar da manyan yayye yakare maganar dayimusu gwalo. Appa yasaka dariyashida Ammi, sukam su ya ishaq kowa ya tsaya da dariyarsa suna hararar bobo Dan sun San zai iya aikatawa sarai. Ya sulaiman ya ce, "haba bobon Ammi garadai kafad'a anan komai ya wuce. Hum'im ban yarda da wayonba a can zan fad'a dankuji ehe. Kaga sulaiman barsa yafad'a d'in , ALLAH yakaimu muma aisaimu fad'a, muce INA yayansu Amarya Dund'un Dunkum. Appa ka gansuko?, bobo yay maganar cikeda shagwa6a. Yanzunkam kowama saida yadara harsu aunty Rasheda dake k'ok'arin shigowa Dan gaida Appa, dama duk suna tsaye tun d'azun sunajin diramar family d'in, kowa sai kunshe bak'i take tana dariya dankar ajisu, zuwa yanzun sun kasa rik'eta Dan haka suka sheke da dariya suduka suna shigowa cikin d'akin. Ya Hamza ya ce, "ALLAH bobo kaji kunya, wai yaushene zaka daina shagwa6ar nan takane?, Rahma kina fama gsky. K'asa Rahma tayi da kanta tana dariya, Dan maganar ya Hamza tabata kunya. Bobo ya kalli Rahma dake dariya tana to she bak'i da hannu, ba k'aramin birgesa tayiba. Safna ma dai yau ba abarta abayaba Dan dariyar takeyi, ba k'aramin birgeta shagwa6aar bobo tayiba. Saida aka tsagaita da dariya su Rahma suka gaida Appa, ya amsa fuskarsa wasai. Mik'ewa su Aunty Sameera suka fara da zummar Fita su basu waje. Appa ya ce, " a'a INA zakuje kuma?, kuzauna ayi hirar zumunci asamu ladan juna, komawa sukayi suka zazzaauna cikeda kunya da k'aunar sirikan nasu masu kamala da dattako. Hira aka cigaba dayi cikin farinciki har aka kira sallar magriba kowa ya mik'e mazan suka wuce masallaci, sukuma kowa yayi alwala sukayi agida. Basu dawoba saida akayi isha'i. Safna dake la6e ajikin motoci tayi saurin rik'o rigar bobo. Da Sauri yajuyo dansan ganin waye?, ganin Safna yasashi saurin zare ido, ya maida kallonsa gasu ya ishaq yaga babu Wanda yajuyo harma sun shige falo, hamdala yayi azuciyarsa dabasuga aika aikar da Safnar tayiba. Juyowa yayi yana kallonta fuska a gimtse ya ce, "sakarmin Riga. Babu musu tasaki Dan gizagon fuskarsa yabata tsoro, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ta ce, kacika "alk'awari. Yagane mitake nufi amma dukda haka saiya yatsine fuska ya ce, " alk'awarin mi?, ke nifa kin addabawa rayuwata. Safna ta marairaice fuska saiga hawaye sharrrr, ta ce, "bobo kana wulak'antani saboda ALLAH ya jarabceni da Sonka ko?, pls ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wlhy sonka zai kasheni Abdulmaleek, bana iya barci, Sonka yana neman haddasa k'iyayya tsakanina da 'Yar uwata, Dan ALLAH karda kayadani Abdulmaleek wlhy Sonka zai halakani, inasonka INA Sonka fiyeda son dAnakema kaina..... Takasa k'arasawa saboda kuka dayaci k'arfinta. Shikam tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa yanzu tafara basa tausayi, jiyayi zuciyarsa tana shawartarsa daya taimaketa koda da nasihane k'ila tagane ta farka daga nannauyan barcin daya d'auketa. Yad'an lumshe idanunsa yabud'e akanta, kinga tashi yafad'a cikin muryarsannan mai dad'i da amo. Safna ta tashi tsaye tana share hawayen fuskarta. A can ciki kuwa saida su ya sulaiman suka zauna sannan sukaga babu bobo. A'a INA Abdulmaleek ya tsaya?, cewar ya ishaq. Kasansa shida baba mai gadi yanzu haka yana can. Ammi ta ce, "Rahma jeki kira mijinki yazo yaci abinci tukunna saiya tafi suyita hirar. Akunyace Rahma tamik'e, zata fita Appa yafito shima daga d'akinsa, ya kallesu ya ce, " a'a INA mukarram d'in?. Gashi can antafi kiransa wajen baba mai gadi. To Aida kun k'yalesa babu dad'i suna hira kuma akatsesu, shima bazaiji dad'iba malam salen, daga yau kar a k'ara haka kunji?. Insha ALLAHU Appa baza'a sakeba suka had'a baki wajen fad'a. Rahma kam tana fita domin kiran bobo, harta kusa tsakkiyar gidan saita hango safna da bobo tsaye safna tana masa murmushi, badai ta hango fuskar bobo ba Dan ya juyasaiata baya, Dan haka batasan shi miyakeyiba, amma wata zuciyarta tana shaida mata shima murmushi yakeyima safna, tsayuwar sojan badakkare tayi, bata gama farfad'owaba ta hangosu sun nufi hanyar lambun gidan, jitai hawaye nabin kumatunta, yaukam abinda take zargi ya tabbata, inhar bobo da Safna ba soyayya sukeyiba a6oye mizaisasu ware kansu alambu kuma arin wannan lokacin?. Ta share hawayenta tareda cije le6enta da k'arfi, juyawa tayi takoma cikin gidan, ta daure ta ce, "yana tareda baba suna hira awaje. Appa ya ce, " kinga Rahma barsa kawai, idan sun gama yazo yaci abincin. Jinjina kai tayi cikin ladabi ta ce, "to Appa." Amma azuciyarta saitace aibama saiyaci abinciba soyayya zata k'osar dashi, d'akin su khairiya tashige tashiga bathroom tasha kukanta San ranta, zuciyarta sai tafarfasa takeyi Dan bak'in ciki, jitake gaba d'aya yau tatsani bobo dakomai nasa. Haka tasha kukanta, bata fitoba saida taji aunty ummy na kwala mata kira tazo suci
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83