Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

akwai matsala babu Wanda ya aikomin da kai da k'afafu, bare suya.☹😋😂_* 2⃣7⃣=2⃣8⃣ Hon yayi mai gadi yabud'e masa gate, saida yatsaya suka gaisa sannan yay cikin gidan, guri yasamu yay fakin zuciyarsa cike da tunani kala2. Yafito tareda kwasan kayansa yanufi ciki, tafiya yake tamkar bayaso, zuciyarsa cike da waswasi, yaushe rabonsa da gidan nan a rin wannan lokacin?...... K'ofar falon yabud'e yashiga, wani k'amshin dad'i yadaki hancinsa, yashak'a ya lumshe idannunsa sannan yabud'e, bin ko INA na falon yakeyi da kallo, komai masha ALLAH, Iyayen amaryar tasa sunyi k'ok'ari gsky, komai na falon farine da ratsin golden. Hasken fitilun yak'ara yalwata k'yawun falon sosai, ajiye ledojin yayi yad'au jakar lap-top d'insa kawai yanufi d'akinsa. Yazube kayan tareda fad'awa saman gado yana fad'in wash ALLAH na. Yay lamo yana tunani Wanda bansan namiyeba, yakai minti goma ahaka sannan yatashi, harya fara cire ma6allin wuyan rigarsa saikuma yatsaya yana tunani, koba komai yakamata ya lek'a d'iyar mutane, k'ilama bataci komaiba, mik'ewa yayi yafito falon, kicin yafara shiga yad'auki filet da Kofi yadawo falo yasaka kaza d'aya afilet d'in, hakama kayan fruits d'in yazuba awani filet d'in daban, yad'orasu saman babban tire harda ruwa da fresh milk sannan yanufi d'akin. Tiren ya ajiye ak'asa saman kafet d'in dake gefen lafiyayyayen gadon nata, yabita da kallo tana kwance ta takure waje d'aya kamar tanajin sanyi, yad'anyi tsaki yana kauda kansa daga kallonta, "k! Yafad'a ad'an kausashe. Komotsi batayiba Dan bama tasan yanayiba, fuska yak'ara had'ewa yana kuma fad'in " k!! Wai bak'ya jinane?, ganin bata motsaba har yanzu yasashi matsawa Kusada ita daf, ashema barci takeyi yak'arshe maganar da tsak'i. Hannunsa yasa ya bubbuga filon data saka kanta, firgigit ta tashi tana kad'a manyan danunnan NATA masu suffar kwai. Kauda idonsa yay daga kallonta Dan idanunta suna masifar tafiya dashi babu k'arya, ga abincinan kitsashi kici yay maganar yana k'ok'arin ficewa daga d'akin. Ngd, amma nak'oshi, nitsatstsiyar muryarta ta daki kunnuwansa, bai juyoba amma yatsaya, hannayensa cikin aljihu wandonsa ya ce, "wannan yarage kuma naki, yay waje abinsa. (Ni bilyn Abdul nace sabon salo, bobo Yakuma zaka canja mana?, bamuyi zaton hakabafa☹). Itakam Rahma hawaye tamatso takuma komawa takwanta, saida tayi kuka mai isarta sannan ta tashi zaune, afili ta ce, " dama nasan bazan samu farincikiba, duk wata kulawa Daka nunamin awajen taron bikin naganin idon danginane danaka, ya ALLAH ka kawoma rayuwata d'auki, kodan darajar biyayya danaima iyayena, nashare musu hawayensu alokacin dasuke zuba, Nima ALLAH kaji k'aina ka daidaita zamana da mijina yafuskanceni tamkar kowacce mace, takuma rushewa da kuka. (Ayya Rahma tabani tausayi gsky). Sauka tayi daga gadon tad'auki tiren tafito, kicin tanufa Dan saida su aunty Sameera suka Nuna mata ko INA na gidan kafin su tafi, firij tabud'e ta saka komai Inda taga yasaka sauran, tad'auki fresh milk d'in da kofin tafito. ko tsayawa kallon falon batayiba takoma d'aki, saida ta kulle k'ofarta sannan tacire kaya tayi canji Dana barci. Zama tayi bakin gadon tasha fresh milk d'in sosai sannan tashiga bayi tai burosh tadawo tai kwanciyarta bakinta d'auke da addu'ar barci. Shima yana komawa d'aki kayan jikinsa yarage yasaka na barci yahau gadon yazauna, jakar dayazo da ita yabud'e ya fiddo lap-top d'insa yafara aiki. Ganin ba kwanciya zaiba nayo waje nikam Dan barci nakeji sosai. _washe gari._ Da asuba kafin yawuce madallaci saida ya kwankwasa mata k'ofa, saida yaji alamar ta tashi sannan yafice. Jin yafita takoma tayi kwanciyarta Dan har yanzu tana Hutu. Saida gari yay haske sannan bobo yadawo gida, barci Yakoma abinsa Dan yana buk'atar Hutu sosai. *_7:48am_* Rahma ta tashi, wanka tafarayi sannan tagyara gidan tsaf dukda ko ina fes yake amma tak'ak'k'ara gyarawa, tabud'e ko ina da k'amshi, tana k'ok'arin komawa d'aki taji ana kwankwasa k'ofa, saida tad'anyi shiru nawani lokaci sannan. Tanufi k'ofar tabud'e, ganin khairiyya da khursiyya yasata sakin murmushi, hanya tabasu suka shigo sannan tamaida k'ofar tarufe. Itama zama tayi suka gaisa (Dan zasu iya zama sa'anni itada tagwayen Ammin), ta ce, "yasu Ammi?. Lfy lau tanama gaisheki, ga break fast tace akawo muku. ALLAH sarki Ammi mungo sosai. Khursiyya ta ce, " Yaya fa?. Saida tayi k'asa da kai sannan ta ce, "yana barci bai tashiba. Khairiyya da khursiyya suka kalli juna suna dariya, saikuma suka mik'e tomu bari muwuce sai anjima. Kai haba dawuri haka?, ALLAH nazata anan zaku wuni. Rufana asiri wannan mijin naki bayason warigi, khairiyya tafad'a ahankali. Saida tarakasu har bakin k'ofar sannan tajuyo ciki, kwandon abincin ta d'auka takai dinning, ta ajiye komai inda yadace, taje kicin tad'akko duk abinda za'a buk'ata ta ajiye, abincinta tad'iba takoma bedroom taci. Bobo kam ana gado ana kwasar barci, sai 10+ yatashi yay wanka yashirya cikin k'ananun kaya yayi k'yau sosai masha ALLAH, yaci sunan nasa Bobo. Yaji dad'in ganin falon fes dagani kasan yak'ara shan gyara, baibi takan Rahma ba yanufi firij d'in dani danufi d'aukar fresh milk yasha saiyaga abinci, ganin kamar kulolin gidan Ammi yasa yazauna yaci abincinsa yay nak sannan yafice. (Araina nace yadace ace yalek'a yaga yata kwana aii). Rahma tanajin fitarsa, danhaka tarabga tagumi tana tunanin sabuwar rayuwarta ta yanzu. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Asibiti yanufa Dan duba yarinyarnan da akaima fad'e, jikinta yayi kyau sosai Alhmdllh, saidai har yanzu bata magana, tsakaninta da Bobo saidai kallo, tana bashi tausayi sosai Dan yanajinta tamkar Nawal, yasan idan Nawal ce ko cikin 'yayan yayensa ko k'annensa mata biyu wata tashiga irin wannan halin yasan zasushiga cikin tashin hankali fiyema da haka, ALLAH kad'ai yasan itama halin da iyayenta suke aciki yanzu.........jiyowa yayi dasauri danjin an ta6asa, ya Sulaiman ne. Kaikuwa miya fiddoka da sassafennan?. Haba Yaya yanzune safiyar?. Harararsa ya sulaiman yayi, ya ce, "amatsayinka na sabon ango wanda aka kaimar sabuwar amarya jiya baikamatama duk yau aganka awajeba, kai daganan harma sati d'aya. Hummm Yaya kenan, amma yanada k'yau nazo naga jikin yarinyarnan, kagafa tunda aka fara bikinnan bana samun damar zuwa. To aii yanzu kaganta saika koma. Yay...... Hannu ya sulaiman yad'aga masa alamar baya buk'atar jin komai. Bayanda zaiyi haka yaymasa sallama yatafi. Indai tak'aicemuku bayani yau tsawon kwanan amarya takwas bata saka angonta a idoba, sadai taji motsin shigowarsa da fitarsa, ko motsin cin abinci, kulum tana d'aki, inkaga tafito wani Abu zata d'auaka shima saita daidaici baya falon. Aganinta shine yakamata yajata ajiki ya sake mata, tunda shine mai gidan, ita yanzu tamkar bak'uwa take agidan. Shikam yana ganin ita yakamata taringa masa abinda zai sake mata d'in Dan da wannan halin Ni'ima tai saurin cafe zuciyarsa har yake ganin tafi sauran mata............ To masu karatu kuyi hak'uri da wannan yau naje anguwane, Marak'isiyya ta mannamin aiki tagudu. *_luv u oll my fan's_* *_(((S)))......2017._* [11/12, 2:21 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{BoBo}•_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* *_wannan page d'in nakine miss xoxona, inafata kinyi sallah lfy?, ALLAH ya maimaita mana._* _Luv u wujiga wujiga_😂❣. 2⃣9⃣=3⃣0⃣ Kwance take akan had'ad'd'en gadonta Wanda yaji shimfid'u na alfarma, tajuya kwanciyarta zuwa rigingine, idanunta suka sauna kan agogon dake manne a bangon d'akin 3:42am. Ta waro manyan idanunta Dan mamakin yanda lokaci yatafi, afili tafurta kai kenen na kwana banyi barciba?. Taja dogon tsaki da k'arfi, dama da gsk ne idan mutum ya ce, "yakwana baiyi barciba?, gsky itakam tana k'aunar iyayenta, tanaso

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});