Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

Abdulmalik Bobo Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

namijine mai wahalar samu acikin maza, zanta godema ALLAH har k'arshen numfashina da kasancewarka mijina, Nawal d'iyata, tabbas kai alkairine ga rayuwata, hawaye yafara bin kumatunta na dad'i...... Ganin haka yasaka bobo fara bata Sumba ako ina najikinta, saida ya yamutsata San ransa, itakam dukda tsoron dake cikeda ruhinta haka tadake zuciyarta tana kar6ar sak'wanninsa. Rungumeta yayi yana sauke numfashi asarek'e, muyi barci yafad'a ahankali yana gyara mata kwanciya. Shiru tayi kamar tana barcin, shikam bobo mintuna kad'an barcin yay awon gaba dashi, ganin barcinsa yayi nisa tazare jikinta ahankali tamaida masa filo a madadinta. Ficewa tayi domin had'amusu breakfast. Cikin 'yan mintuna ta kammala komai ta gyara ko ina yad'auki k'amshi, abayinsa tayi wanka sannan tadawo d'akinta, mai tashafa tayi 'Yar kwalliya yau harda jambaki tasaka, aiko tayi k'yau tamkar kasaceta kagudu. Siket dariga tasaka na atanfa fara da adon jajayen fulawoyi. Masha ALLAH nafad'a araina Dan babu k'arya Rahma tahad'u. Kum tad'auka tana taje kanta, wani d'an ruwa daya d'id'd'iga asaman gashin yafara tsalle harya sauka akan fuskar bobo. Bud'e ido yayi ahankali yasauke akan Rahma dake tsaye agaban madubi tana faking d'in gashinta da jan ribom. Lumshe ido yayi yabud'e yana murmushi aransa yace masha ALLAH. Itakam dabatasan yanayiba tad'auk'i d'ankwali ta tayi d'auri mai k'yau na zamani, tad'auki 'yan kunne jajaye tasaka sannan takuma feshe jikinta da turarenta. Juyowa tayi danufi fita saitaga idon bobo akanta, hannu tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, shima mik'ewa yayi zaune yana murmushi, yatako ahankali zuwa gabanta, hannunsa biyu yasaka yarik'o k'ugunta, muryarsa anarke ya ce, "beautiful Lady kinyi k'yau sosai, shine kikamin wayau ko?. Girgiza masa kai tayi haryanzu hannunta nakan fuska. Ya ce, " to bud'e fuskar naga kwalliyar tawa ko?, akunyace tacire hannunta, woow my beautiful wife kwalliya namiki k'yau amma bak'yasonyi, todaga yau haka nakeso aringa tsantsaramin wadda zata ringa hanani fita office. Yabata dariya Dan haka tatuntsure da dariya, shima dariyar yayi tareda rungumeta, bayan sund'an sarara ya ce, "to muje nima kimin wankan. Idanu tazaro waje ta ce, ''rufamin asiri." Asirinki arufe yake aii, shima yafad'a yanad'an zaro ido kamar yanda tayi. Murmushi yayi, shikuma yafita yana fad'in tom bara naje nayi my cute, amma next time bazan d'aga miki k'afaba. Murmushi Rahma tayi tareda d'aga hannunta sama tana fad'in ALLAH ngd maka daka daidaita al'amurana alokacin dabanyi zatoba. d'akin tahau gyarawa cikin lokaci k'alilan takammala takoma falo tazauna jiransa yafito. Shima baid'auki lokaci mai tsawoba yafito cikin k'ananun kaya wando 3Β½ da k'aramar Riga tashan iska duk farare tas, yasaka Jan silifas ak'afarsa, sai zabga k'amshin turarensa yake na alfarma. d'agowa tayi tana kallonsa, yasakar mata murmushi itama ta mayar masa tareda mik'ewa, a dinning suka yada zango, tazuba musa abincin tana k'ok'arin zuba nata yarik'e hannunta tareda mata magana da ido. Zama tayi danta fahimci inda yadosa, indai tak'aice muku dakansa yabata abinci itama tana basa, haka sukaci suka k'oshi tagyara wajen suka dawo falo suka zube. Rahma takalli bobo ta narke murya, wai bazamuje gidan AMMIN ba?. Ido d'aya ya kanne mata, ya ce, "a'a yau zamu huta agida musha soyayyarmu my cute. Baki taturo kamar wata bebyn roba. Zamewa yayi yakwanta bisa kujera yana murmushi. Sallamar da akayice takatsema bobo maganar dayayi niyyar yi...... Rahma ta amsa tana maida kallonta ga k'ofa, ta ce, " kushigo. Zeenat da baseera suka shigo da sallama, mik'ewa Rahma tayi taje ta tarbosu cikin farincikin ganunsu, zeenat ta ce, "oh ni Autar ummy amare. Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana fad'in kai aunty zeenat, baseera ta ce, " Yar lukutar ummi kin k'ara kibafa, aunty baseera kema hadake ko?, Rahma tayi maganar cikeda shagwa6a. Dariya sukayi tareda k'arasawa cikin falon, baseera da zeenat suka kalli juna Dan basuyi zaton bobo yana nanba. Zama sukayi suna gaisheshi, baiko kallesuba ya amsa da lfy amma fuskarsa asake, mik'ewa yayi yana fad'in yakuke?. Sukace lfy lau wlhy. Fita yayi harabar gidan danya basu waje, dandanan Rahma tacika musu gaba da kayan ciye ciye, ta zauna suka gaisa. Zeenat ta ce, "nibanji motsin mutuniyarba. Wai aunty safna?. Sukace eh. Lah tana gidansu ya Abdulmaleek aii, a can takwana wlhy. Dama tunda naganku nasan zuwantane tunda Baku ta6a zuwaminba. Dariya sukayi baseera ta ce, " a'a dama gunki mukazo ko zeenat, gyad'a kai zeenat tayi tana dariya. Daganan hira sukashigayi, bayan kamar minti30 suka mik'e tareda alk'awarin suma zasu halarci bikinsu khairiyya d'in. Godiya tamusu tarakosu har harabar gidan, bobo nasaman mota zaune, suka masa sallama sannan suka tafi. Dirowa yayi daga saman motar idonsa akan Rahma, batayi auneba taji yad'auketa cak kamar jaririya yanufi cikin falon da ita. Direta yayi saman doguwar kujera suna dariya, yakwanta tareda d'ora kansa saman cinyarta suna kallon juna, ya ce, "wad'an nanfa daga ina?. K'awayen aunty Safna ne?. Baice komaiba, saima ya kauda zancen da d'akko wani daban................. *_"Dan ALLAH duk masoyina yamin addu'a acikin sallarsa, ALLAH yabiyamin buk'atata ta alkairi, yakuma azurtani da abundana nake buri na alkairi."_* πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ» *_luv you oll_* *_(((S))).......2017_* [11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........ ❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _β€’{πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύ}β€’_ *_NA_* _*Bilyn Abdul*_ _sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_* *_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._* 😭😭😭😭😭😭 6⃣0⃣ Wunin ranar gaba d'aya haka bobo da Rahma suka kasheshi asoyayya da tattalin juna, dukda Rahma tanad'anjin kunyar bobo har yanzu. Ganin shiru basuzoba Ammi takira bobo tana tambayar ko jikin Rahmar ne har yanzu?. Cikin Sosa kai na jin kunya ya ce, "a'a ammi taji sauk'i bamuzoba daine kawai, sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Murmushi Ammi tayi ta ce, " toshikenan ALLAH yakaimu goben tunda dai lfy Alhmdllh, ka gaishemin da ita To Ammi zataji. Rahma dake kwance ajikinkinsa ta ce, "ya Abdulmaleek ko kunya bakajiba Dan ALLAH. Murmushi yayma tareda fad'in kunyar wa zanji?. Ta Ammi mana. Nanma murmushin yasakeyi batareda yace komaiba. .*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Shirye shiryen biki ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro. Rahma da bobo kan sai godiyar ALLAH, soyayyarsu suketa zubawa kamar babu gobe, amma dai baisake mata komaiba Dan yana tausayinta sosai, kuma bobo ba irin fitunannun mazan nan baneba, tattalikam tana shansa, azuciyarta har mamakin bobo takeyi Dan bata ta6a tunanin yanada sauk'i hakaba, ada tana masa kallon muskili masifaffe. Amma yanzun data k'ara kusanci dashi saitaga Bahaka bane, dukda yanada fad'a amma sai anta6oshi yakeyi. Safna kam abin duniya ya isheta, k'iriΒ² Ammi tahanata komawa gidansu Rahma, kayantama ranar gabad'aya bobo yakawomata gidan Ammi, bak'aramin 6aci ranta yayiba dantasan wannan Duk shirin bobone. Yau tunda safe take tsumayensa amma yak'i zuwa gidan kamar yanda yasaba, suna zaune itadasu khairiyya dake had'a kayansu saboda daga gobe shagalin biki zai fara. Kad'an kad'an saita lek'a window d'akinsu khairiyyar Dan daganan ana hangen Wanda zaishigo gidan, ta kalli agogon hanunta tareda yin tsaki. Khursiyya ta ce, "aunty safna lfy kuwa?. Murmushin yak'e tayi tareda wayancewa ta ce, " wlhy ya Abdulmaleek nake jira sonake nakar6i sak'o awanjensa. Su khairiyya basu kawo komaiba aransuba sukace ayya k'ila yanacan yana shan sharafin soyayarsama, kinsan su ya Abdulmaleek sai addu'a, k'ila kuma bazaizo gidanba saiya tashi daga aiki Dan wataran

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});