Chapter 89
Chapter 89
yakeyi a kanki U.A Shuwa a gabanmu fa ya daukeki yayi sama dake kunfi awa biyu kafin ku sauko downstairs Aunty Zarah tayita mita tana cewa harijin banza naga yanda zakayi ai idan ka tafi gurin waccen guzumar daka daukowa kanka" nayita mamaki shine Sa'ud tabani lbrn aurenku da soyayyarku shiyasa nace nasan Aunty Murjanatun mu da Muhd dinta nasan tarihin soyayyarsu amma bantaba tunanin zaa samu masoyan da suke sadaukarwa juna farin ciki kamarsu ba sai gashi banje ko inaba na hadu da wadanda suka fisu" Kallonta Umaimah tayi tace “na shirya bayar da rayuwata fansa akanta bloodyna S Alfah wlh inason Uncle Hameed fiye da yanda nakeson Shurafah" kallonta S Alfah tayi zatayi mgn tayi saurin daga mata hanu tace “karki tambayeni dalili S Alfah wlh bansan dalili ba nidai kawai Allah ya halicci zuciyata da so da tausayin Abu Shurafah ina gasqatashi a dukkan furucinsa da aikinsa saboda na yarda dashi tun bansan kaina ba wannan tausayin shine rauni na bana iya yiwa bloodyna musu kuma bana iya bijirewa umarninsa amma wace Aunty Murjanatu S Alfah?" Kawar dakai S Alfah tayi tace banason tuna wani abu daya shafi Aunty Murjanatu saboda kuka nakeyi har hawayena ya qare abu daya dazan iya fada miki shine Murjanatu da Muhammad masoyan junane wadanda zaa iya sanyasu a tarihin masoyan duniya saboda hatta ajalinsu tare ya riskesu ranar da Muhammad yayi hatsari ya rasu Aunty Murjanatu tanajin lbrn mutuwarsa ta yanke jiki ta fadi tashin da itama ba tayiba har yanzu zuciyarta ta buga tabi mijinta ga kabarinsa ga nata U.A Shuwa bafa basa fada bane sunayi amma ko sunyi wani bayaji tsakaninsu suke sasanta kansu idan kuwa har yayi tsamari to koda ta tafi gda yana zuwa zakaga sun fara tsotse²nsu daga haka saidai ka nemesu ka rasa sun gudu gdansu wlh baa taba shiga tsakanin Murjanatu da Muhammad ba wannan shine abinda zan iya fada miki" Ajiyar zuciya Umaimah tayi tace “ina tunanin nima idan bloodyna ya mutu wlh mutuwa zanyi saboda da second daya banason naga yayi nesa dani ke shekaran jiya wlh ban iya bacci ba amma jiya baccina nayi me dadi tare da mijina" mamaki ne ya cika S Alfah tace “amma ai jiyama a gurinta yake ko?" Kawar dakai tayi tace “yace bazai iya kwana uku ba daya ta samu shima din a daddafe ina tunanin kwana daidai zaikeyi mana" Da wannan zancen suka fara lecturer suka tashi ta shiga motarta ta nufi gda kafin taje gdan ya kirata yakai sau biyar saida tace masa tana gda sannan ya qyaleta. Haka rayuwata taci gaba da tafiya shidai bangaran Hameed abin yanayi masa yadda yakeso amma bangaren Umaimah da Salma baa cewa komai ita Umaimah damuwar jarabarsa ga cikinta ya fara girma shima qaqqarfa irin ubansa sai damunta yake da naushi har ya shiga wata na takwas sannan ga hidimar karatu da ta dauki zafi sun gama level 100 sunyi hutu har sun koma suna 200 level. Ita kuwa Salma kullum sake daura dammara takeyi ta ganin ta kori Umaimah daga gdan badon komai ba saboda an sake jaddada mata matuqar Umaimah tana gdannan to bazata tabajin dadin zama a gdan ba saboda itace zuciyarsu jininsu da komai nasu dayane bazai taba kulata ba balle tasa ran zaiyi wata mu'amala da ita zama takeyi kawai nacin abinci dukiyar da take hange gatanan amma tafi qarfinta saidai kullum idan zai fita zai bawa me gadi 3k ya bata inda ita kuma Umaimah yake bata 6k yace uku na hidimar gda uku na kula da baby's dinsa a cikin wannan lkcn ne babar Salma taje mata Togo gurin amintaccen bokansu shine ya hado mata wani surkulle yace tasan yanda zatayi ta zuba masa a abinci yaci sannan ya hada mata turaren tsafi yace tayi amfani dashi a jikinta Hameed zai kusanceta idan ya kusanceta to mgn ta qare a ranar saiya saki Umaimah tunda ya fahimci sparm din bazai samu ba amma fah asirin bazai dade a jikinsa ba daga lkcn daya saki Umaimah zuwa kowanne lkc zai warware to daganan ita kuma tasan yanda zatayi saboda akwai yuwuwar uku babu zasuyi ya saki Umaimah ya saketa kowa ya huta. Amma saboda toshewar basira haka Salma ta karbi aikin ta fara tunanin yanda zata aiwatar dashi saboda Hameed ko ruwa bayasha a bangarenta dabara ce ta fado mata ranar wata talata Umaimah bataje mkrnta ba saboda cikinta yayi nauyi sosai hakan yaba Salma nasarar shiga part dinta tayi sallama harda fara'arta abinka da mai tsarkakkakiyar zuciya Umaimah bata kawo komai ba ta yunqura zata miqe tayi saurin qarasowa ta kamota tace “wayyoh sannu Ummuh Shurafah wlh banyi tunanin haka Babyn nan yake wahalar dakeba da na rinqa zuwa Ina tayaki aiki to tsoro nakeji kada nazo kiyi tunanin wani abu” tsugunawa tayi a gabanta tace “don Allah kiyi hqr ke ki fahimceni tunda mijinki yaqi fahimtata wlh banida niyyar cutawa a gareku ban shigo gdanku domin na shiga tsakaninku ba ki yarda dani ba Salman da kuka sani a baya bace na canza sosai fiye da tunaninku" Ajiyar zuciya Umaimah tayi zuciyarta da cikakken tsarki tace “ babu komai ni dama ban taba daukan ki a matsayin wacce zata rabani da mijina ba kawai na daukeki a matsayin qaddararmu kuma ni nasan babu abinda zai samemu face sai Allah ya qadarta faruwarsa ki saki jiki dani Aunty Salma banida matsala wlh da zuciya daya nake zaune da duk wanda Allah ya hadani dashi" Murmushin mugunta Salma tayi ta miqe ta zauna a kujera sukaci gaba da hirarsu tanata bawa Umaimah lbr suna dariya tana yima Shurafah wasa.......... *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* [1/30, 1:54 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GU* Miqewa tayi daqyar ta nufi sama tace “inajin marata tana ciwo kwana biyunnan wlh jiya naso zuwa asibiti kuma sai na manta ban fadawa Bloody ba saidai idan ya dawo muje" tana mgn tana hawa sama wani mugun kallo Salma tabita dashi a fili tace “saura qiris” ajiye Shurafah tayi ta tashi da sauri ta nufi dinning din tana dube² tana waiwaye na rashin gsky ta bude warmer Allah ya taimaketa kuwa ta bude ta farfesun naman ragon daya wadatu da kayan qamshi sai qamshi yakeyi ita kanta saida ta hadi yawu ta ta kwanto qullin maganin a habar zaninta ta kunce ta barbada a cikin farfesun ta sanya cokali ta juya tayi maza ta dauke cokalin ta daureshi da maganin a zaninta ta koma ta zauna ta dauki Shurafah taci gaba dayi mata wasa daidai lkcn Umaimah ta sauko dauke da waya a kunnenta ta zauna miqewa Salma tayi tace “bari na tafi naga mijinki ya kusa dawowa kada yazo ya ritsani anan yawwa don Allah wata alfarma kada ki fada masa na shigo wlh nasan rashin mutunci zaiyi min saboda kwanakin baya nace masa inason shigowa yace karna sake na shigo gurinki na dora miki damuwa" Murmushi tayi kawai ita kuma Salma ta fita ta nufi part dinta tana shiga ta fara tsallen murna wannan tarkon ya danu saura na gaba. Kwanciya tayi ba mgnr sallah ita kuwa Umaimah tana fita ta shimfida sallaya tayi sallar magaruba taci gaba da azkar dinta tana zaune ya shigo ta bayanta yabi ya rungumeta yace “ nayi missing dinki bloody bari nayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111