Chapter 1
Chapter 1
An dauko wannan littafi daga shafin www.hausanovels001.com.ng ku ziyarci shafin na www.hausanovels001.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348138892814 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348138892814 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊 ( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_ *GIDAN UNCLE* ( _Love and romantic story_ ) *SHORT AND TRUE LIFE STORY* *MALLAKAR* 👇🏻 *FAUZIYYA TASI'U UMAR* *®FAUZAH* *Wattpad👉🏻 realfauzah* www.fauzahtasiu41.com *~Tsokaci~* _Bance dole ne ki karanta labarina ba saboda haka idan kika zageni keda Allah yanda salon labarin yazo haka zan rubutashi_ . Page One Zaune suke a dinning table gaba daya ahlin gdan guda biyar suna dinner cike da kulawa da tattalin juna yarane guda biyu mata kyawawa sai wata yar matashiyar budurwa da bazata wucce 17 years kyakkyawa ce sosai Mai dirarren jiki duk da a zaune take da alamun bazata cika tsayi ba kuma ba gajeriya bace ba fara bace tass kuma ba baqa ba itadai zaa iya kiranta wankan tarwada tanada murjajjen jiki sosai kuma tanada cikar halitta sosai. Yar matashiyar matar gdan da itama bazata wucce 25 years ba ta kalleta tace “Hameed kamar wani Abu yana damun qanwarka Umaimah fah naga kwana biyu bata da walwala sosai ko kai baka lura da hakan ba?” ajiye cokalin hanunsa yayi dago ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace “bazai wucce tunanin Ummanki ba ko?" Saurin daga masa kai tayi tace “wlh Uncle narasa meyasa duk tsayin shekarun nan da na rasa mahaifana bantabajin ciwon rashinsu ba sai a yan kwanakin nan...” Tayi shiru da mgnr saboda kukan da yakecin zuciyarta yan qananun yaran guda biyu da basu wucce shekara uku da biyar ba suka matso suka rungume ta babbar tace “Aunty Umah ki daina damuwa bamaso kinga har kin rame ko Daddy kaima kaga ta rame ko?" murmushi yayi ya miqe yace “is ok zata daina kuje ku kwanta saida safe mayi mgnr saboda yanzun na gaji yawwa Umaimah ki yomin list na abubuwan da kike buqata nasan dai bakida mai naga kinyi duhu kuma wata yayi nisa qila bakida parts ko?" Qasa tayi da kanta tana murmushi tace “kayy Uncle ka bari banaso ni kunya nakeji” Aunty Sadiya ta miqe ta shige dakinta tana cewa kaidai baka rabo da shirmen yarannan nidai na tafi dakina kuma gsky kada kazo ka dameni bacci nakeji gobe zan tafi Serminer Lagos" ba Hameed ba hatta Umaimah saida ta juya ta kalleta itama juyowa tayi ta kallesu da sauri Umaimah ta kawar da kanta Aunty Sadiya tati murmushi ta garqame dakinta da key. Juyawa yayi jiki a sanyaye ya kalli Umaimah yanajin ciwon abinda Sadiya takeyi masa a gaban Umaimah qanwarsa kasancewar da Abdulhameed da Umaimah abokan wasane da baban Hameed da babar Umaimah uwarsu daya ubansu daya iyayenta sun mutu a wani hadarin mota da sukayi tsakanin Damaturu da Kano ya rage daga ita sai yayarta Jameelah saboda da sabo da shaquwar yake tsakaninsa da Umaimah tun tana qarama yasa da Jameelah taso riqe yar uwarta a lkcn yayi aure sai yace shi yanaso abashi ita ya riqe iyayensa sunso hanashi amma ya kafe yana roqonsu to besamu matsala da matarsa Sadiya ba saboda ita gani take sauqi ne yazo mata zata huta sosai dalilinta kuwa ta fahimci Umaimah irin yaran nan ne masu tsafta da rashin gandar aiki aikuwa sosai Umaimah ta horu da aiki ba rashin ci ba rashin sha babu wulaqanci saidai aikin gdan komai ita takeyi hatta girki da kula da yara idan ta tashi da safe saita fara shirya yaran sannan ta shirya Uncle Hameed ya dabesu ya saukesu a makaranta ita har zuwa yanzu data gama secondary take jiran result. Ajiyar zuciya yayi ya shige dakinsa ya fada toilet yayi wanka ya dawo ya kwanta yanata juyi zuciyarsa tab da saqe², itama Umaimah tana shiga dakin bayan takai yaran dakinsu ta kwantar dasu kwanciya tayi tare da daukan wayarta ta kunna qira'ar shaikh Sulaiman tana sauraro da haka bacci ya dauketa washe gari da wuri ta tashi dake Monday ce ta kama Nihal da Maliha tayi musu wanka tasa musu uniform dinsu ta hada musu abincin su ta zuba musu a lunchbox dinsu sannan ta basu tea sukasha daidai lkcn iyayen nasu suka fito ba daki daya suka kwana ba amma a tare suka fito a gurguje Sadiya tasha tea ta kalli Hameed tace “Uncle ni zan tafi may be zan iyayin sati daya Umaimah ga Nihal da Maliha nan ki kula dasu saboda kinsan akwai sanyi garin koda yake banajin ki” Tana fadin haka ta juya ta fice tana cewa “Bye My love" shidai bai iya cewa komai ba sai kallonta da yakeyi da lulu eyes dinsa da suka canza kala alamun bacin rai miqewa yayi ya dauki jakar laptop dinsa ya zaro kudi a aljihunsa ya ajiye mata a saman dinning din yace “gashi ko zaku buqaci wani abu" a sanyaye tace “mun gode Uncle amma inason idan kun fita zanje kitso" da sauri ya kalleta yace “aa banason yawo kinsani nifa bama nason kitsonnnan gsky” bata dauki komai a ranta ba tace “shikenan Uncle
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111