Chapter 50
Chapter 50
fara doka horn megadin yazo ya bude parking tayi cikin tsananin firgici ta bude ko kashe motar batayi ba ta shiga cikin gdan. A durqushe ta sameta riqe da cikinta tana ta murqususu tare da cije lebe tana hawaye shiga tayi da sauri ta ruqota tana cewa “Subhanallahi Umaimah kada ki mutu don Allah tashi maza tashi mubar musu gdansu Umaimah na yarda maraya bashi da gata a wannan zamanin wannan dalilin yasa na ware kaina saboda kunci da baqin cikin rayuwa ya isheni” tana fadin haka tana hadawa Umaimah kayanta a cikin handbag dinta tare da jan akwatunan kayanta guda biyu dake jingine a jikin bango ta fita da gudu² sauri² ta zuba a motar ta dawo ta dauki wayar Umaiman tare da magungunan ta ta dagota da iyakar qarfinta tana juya kai tana kuka tana komai tasata a mota ta shiga taja tare da zuge baqin glass din saboda gudun kada get man din ya gansu suka fita unguwar Hotoro suka nufa cikin wata hadaddiyar Unguwa me suna Farawa layout suka shiga unguwar ganin yanda Sa'ud taga aminiyar tata tana riqe cikine yasata nufar wani babban asibiti da ake kiza Zeenat clernic and digonostic ta shiga tare da fita da sauri tayima likitocin bayani suka nufo motar aka kamata ranga² aka nufi cikin wani daki da ita suka duqufa aikinsu. Bincike sukayi sosai akanta kafin su gano inda gizo yake saqar tashin hankalin da take cikine ya assasa mata hawan jini me tsanani wanda yayi tasiri wajan lalata cikin dake jikinta yakeson fita amma babu hali saboda haka suka fara qoqarin ceto rayuwarta ta hanya cire mata cikin sannan suka daura mata ruwa tare da neman jini kasancewar kafin zuwansu asibitin ta zubar da jini yafi leda biyu kallon likitan tayi tace “Dr indai akwai abamu mu siya sai nayi muku transfer bamu da kudi cash a hanun mu” bai wani damu ba yaje ya bincika yayi sa'a aka samu laida daya irin blood dinta ya maqala mata tare da rubuta mata magungunan qarin jini Sa'ud tayi musu transfer ta account dinta kamar yanda ta fada masa naira na gugan naira har 140,00 saida aka mayar da Umaimah dakin hutu sannan Sa'ud ta samu ganinta lkcn har tayi sallah take gida ta dawo tana kwance a gadon idanunta a lumshe tayi wani fari ta dashe saboda rashin Isasshen jinin da take fama dashi. Kama hanunta Sa'ud tayi cikin hawaye tace “Sannu bloody kiyi hqr ki daina kukan nan kowanne bawa baya wucce qaddararsa kinji” bude idonta ta rinqayi a hankali harta saukesu tar a fuskar Sa'ud idanunta naci gaba da malalar da hawaye tace “ina Uncle Hameed Sa'ud wanne hali yake ciki ya mutu ko?” kada mata kai tayi tace “yananan Umaimah bazai mutu ba insha Allahu" lumshe idonta ta kumayi daidai shigowar likitan ya fara dubata yace “alhmdllh jiki yayi kyau sai fatan Allah ya mayar dana aika” bude idonta tayi da sauri da tsananin mamaki tace “kamar yafa ban gane ba?” shafa gashin goshinta Sa'ud tayi tace “damuwar da Hajiya ta jefaki a ciki ce tayi sanadin zubewar cikin jikinki Umaimah..." Miqewa tayi a tsorace tace “da gaske ya zube shima Innanillahi wa innah ilaihir raji'un shikenan farin cikin Uncle ya zube meyasa ya zube Dr inason cikina yanzu shikenan nayi biyu babu ba ubansa babushi” Tausayinta ne ya cika zuciyar Sa'ud ta kamota ta miqe tace “insha Allahu komai zaizo qarshe Bloody nasan akwai ciwo a rabaka da mijinka batare da neman shawararka ba amma babu komai akwai Allah kuma Ina tabbatar miki Hameed bazai iya rabuwa dake ba saboda kece kadai zaki iya zama dashi ki biya masa buqata yanda yakeso kuma ya samu gamsuwa dake 💯 saboda haka karma ki wani damu tunda kinji qwari tashi mu qarasa gda kiyi wanka mu nemi abinda zamuci kinji” shidai likitan binsu kawai yakeyi da kallon mamaki “dama matan aurene ku?" Yakasa jurewa ya tambaya kallonsa sukayi a tare Sa'ud ce tayi qarfin halin cewa “eh Hussaina tace am don Allah Dr mace da aka saketa da ciki kuma cikin ya zube matsayin iddarta yake a musulumci?" Shafa kansa yayi sannan ya zauna yace “ma'anar iddah tana nufin tsarkin mahaifa tsarkin mahaifa kuwa shine yin jini bayan rabuwar aure to wacce aka saketa da ciki kinga bazatayi jini ba harsai ta haihu shiyasa iddarta take da wahala bayan ta haihun da zarar ta haihu to iddarta ta cika ko ranar zaa iya daura mata aure kinga kenan a shari'ance matar da aka saketa da ciki tayi bari koda a ranar da aka saketa ne to ita ta tsarkaka wannan shine amsarki a taqaice wallahu wa rasulihi aalam" yana fadin haka ya miqe ya fita tare da basu sallama Sa'ud ta kama hanunta suka fita a sanyaye jikin Umaimah yake ji takeyi dama zata iya mayar da cikinta jikinta jikinta yanzu shikenan ta fita daga sahun matar auren Abdulhameed? Wasu hawaye masu zafin gaske suka gangaro mata da haka suka shiga motar suka nufi cikin unguwar sunyi tafiya me dan tsayi sannan sukayi parking jikin wani dan matsakaicin flat house me kyau saida Sa'ud ta tabata sannan ta dawo hayyacinta ta bude mata qofar ta fito tana daga qafarta daqyar ta nufi qofar da taji Sa'ud din na budewa ta bude mata ta shiga tanabin gdan da kallo wata qofar taga tasa key ta bude nanma Umaimah tasa qafarta ciki wani sanyi da qamshi me dadi ya daki hancinta ta lumshe idonta duk da zuciyarta babu dadi amma taji dadin qamshin ta bude idonta tanabin parlourn da kalloh yayi kyau sosai sai qofofi guda uku da suke a kulle, zubewa tayi a saman kujera tana sauke ajiyar zuciya tanabin parlourn da kallo amma gaba daya hankalinta na wajen Uncle dinta “ko wanne hali yake a ciki?" Abinda ta tambayi kanta kenan. Tana zaune Sa'ud din ta shigo ta cire hijjab dinta tana murmushi tace “tashina kenan daga bacci kika kirani kinga ko rigar baccin ban cire ba na zari hijjab na fita" kawar da kanta tayi gefe saboda batason hayani ko surutu itama bata qara yimata mgnba ta bude daya cikin qofofin ta shiga bata jima ba ta fito ta bude dayan dakin tace “bloody ki shiga ki kwanta kafin na sama mana abinda zamuci nasan zuciyarki tana cike da zargi na da tarin tambayoyi akaina da kuma tunanin meyene yasa na daukoki na kawoki nan to kiyi hqr zan baki amsa nan da yan mintuna" Tana gama fada mata haka ta riqo hanunta suka shiga dakin data bude mata mamaki ne ya cika zuciyar Umaimah ganin dakin a shirye tsaf kamar na matar aure gado wadroop madubi da bedsat komai dai akwai sai wata qofa da take nuna alamun bathroom ne qarewa dakin kallo tayi kafin ta zauna a gefen gadon ita kuma Sa'ud ta fita ta shiga daya qofar ta fara hada musu abinci. ************************* Kusan awansu hudu da zuwa asibitin amma har yanzu bai farfado ba ko numfashi baya iyaye saida taimakon na'ura daga Hajiya har Aunty Zarah ba qaramin tashi hankalinsu yayi ba sun ma manta da baiwar Allah Umaimah da halin da zata iya shiga sai kaiwa da komowa sukeyi tare da likitocin a haka har dare yayi sai goma saura Zarah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111