Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 108

Chapter 108

Gidan Uncle Return Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma ya amsa addu'ar ka Umaimatu ta dawo garek...." Tsayawa yayi cak mgnr ta maqale a maqogaronsa saboda ganin Hameed din kwance a qasa cikin amai yayi kaca² sauri ya saki ihu ya matsa ya dagoshi yana jijjigashi yana fadin “mun shiga uku Hameed kada ka mutu Daddy ya baka matarka ya daura aurenku...” Riqeshi yayi cikin wata wahalalliyar murya yace “yay...ya daura in...ina Umaiman tak..." Muryarsa ce ta sarqe daidai lkcn Daddy suka shigo da gudu suka qarosu suna salati suka tattageshi sai asibiti likitoci suka rufa a kansa suna ceto rayuwarsa bai farka a ranar ba sai washe gari ya farka da qwarinsa saboda yasha drip babu qarya qyam ya miqe yana layi Daddy ya riqeshi ya kalli Daddy yayi murmushi yace “idan naje gdana yanzu zan tarar da bloody tana jirana?” *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* [2/5, 9:08 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_* Murmushi Daddy yayi yace “aa tana gda saita yaye twins sannan zata tare..." Yanda ya wani zabura ne yasa Daddy yin shiru da mgnr yace “aa Daddy bazan iyaba tana karatu ni kuma baa qasar nan nake aiki ba tunda an daura ta tare a gdanta kawai na rinqa zuwa duk qarshen wata kafin ta gama karatun”shidai Daddy bai kuma ce masa komai ba likitansa yashigo ya kalleshi yayi murmushi yace “aa shugaban masoya ka miqe kenan shikenan ni kuma tawa kasuwar zata mutu buri ya cika" Dariya sukayi dukkansu amma bandashi da duk ya qosa yaje gda yaga sanyin zuciyarsa saida suka gama cike²nsu sannan suka bashi dokoki suka tafi Daddy yanayin parking bai jira tsayawarsa ba ya balle murfin motar ya fita ya shiga gdan Aunty Zahrah ya tarar da Umaimah a zaune a parlourn taci kukanta har idonta ya kumbura gabansa ba qaramin faduwa yayi ba saboda yanda ta watsa masa wani dan iskan kallo ta kawar da kanta taci gaba da abinda takeyi qarfin hali irin na Hameed baisa ya hqr da abinda yayi niyyah ba yaja qafarsa ya qarasa ya tsugunna a qasanta ya dora hanunsa a saman cinyarta yana qare mata kallo yanajin qaunarta na azalzalar zuciyarsa yace “ina cikin farin ciki wanda ban taba shiga irinsa ba a rayuwata bloody kin dawo rayuwata” Ture hanunsa tayi ta miqe idonta taf da hawaye tace “nikuma Ina baqin cikin dawowarka rayuwata Hameed wancan karon nayi gangancin dawowa rayuwarka amma yanzu reshe ya juye kaine kayi ganganci kuma zaka dade kana nadama saboda banasonka Hameed banasonka banason rayuwa dakai....” wani abu yaji ya taso masa baisan sanda ya miqe ba ya cafki hanunta da qarfi ya hadata da jikinsa yace “qarya kikeyi bloody ko ki yarda ko kada ki yarda kinasona kuma sai kin rayu dani kuma ni a rayuwata bana ganganci indai akanki ne komai nayi daidai ne saboda haka bakinki ya daina furta wannan kalmar sabo kikeyi" Baki ta bude zatayi mgn yayi saurin dagata ya tura dakinta ya shiga Hajiya nayi masa mgn saboda kukan da Umaiman takeyi amma ko sauraronta baiyi ba ya datse qofar ya jefata gadon yana haki yace “nine nayi gangancin dawowa rayuwarki ko?" Miqewa tayi ta matso gabansa tace “haka nace kuma bazan janye ba Hameed kayi ganganci daka nace har ka kama haukan qarya kasa Daddy ya karya billensa ya roqeni nayi biyayya wa umarninsa ka rabani da wanda na shirya rayuwata dashi ka dade kana zalumtar rayuwata ta wannan fannin na fada kuma bazan fasa ba kayi ganganci Hameed kuma da kanka zaka gasqata kayi gangan...." Hawa gadon yayi ya matsa kusa da ita ta janye ya qara matsawa ta janye yayi murmushi yace “ nayi alqawarin bazan qara takura miki na kusanceki ba amma duk ranar da kika bari kika shigo hanuna zaki gane bakida wayo wayewar da kike taqamar kinyi batakai inda tawa takai ba" Miqewa yayi ya bude qofar ya fice kitchen ya shiga ya tarar da Hajiya ya shafa kansa yace “Hajiya amma yau zata tare ko?" Wani kallo ta watsa masa tace“daka dauketa ka shiga da ita dakin baka tambayeta ba?” shafa sumarsa yayi yana murmushi yace “bafa wani abun nayi mata ba" hanunta ta dora a saman bakinta tace “ya isa fice ka bani guri rasa kunya ai dama nasan ba wani abu kayi mata ba amma dai yz kamata kabita a sannu saboda zuciyarta bason auren nan takeyi ba” hadiye wani yawu yayi me daci yace “dalilin da yasa nace ku bani matata kenan saboda na saitata yanda nakeso Allah wani abun harda zugarki Hajiya yarinyar nan takemin saboda kawai Allah ya jarabceni da sonta to babu yanda zanyi haka zan hqr yauwa Hajiya Ina twince suke?" Bai jira amsarta ba ya fice ya nufi dakin Nanny dinsu ya daukesu ya nufi dakinsa dasu ya kwanta we suka hau jikinsa suma suka kwanta yanata hira dasu kamar wasu masu baki sunata yimasa shirmensu yana dariya kamar zautacce Hameed kenan Allah ya jarabceshi dason yara indai da yara a kusa dashi toshi bashi da damuwa balle twince da yakejin qaunarsu daban a ransa. Duk yanda yake daukar abin da wasa ya wucce masa nan don fir Umaimah taqi yarda ko haduwa sukeyi a parlour kuma duk sanda zaije dakinta a datse zai taddashi da key abun yana matuqar sanyaya masa jiki amma idan ya tuna nadan lkcne sai yaji sanyi a ransa yasha binta makaranta yayi juyin duniya tazo su tafi amma ta qeqashe qasa tace bazata shiga motarsa ba haka zai hqr ya dawo gdan kallon tsiya baya samu daga gareta balle na arziqi daqyar ya shawo kan Daddy ya amince da Umaiman ta tare a gdanta amma saida Hajiya ta buga masa lissafi harna million uku da rabi na kayan lefe da turare da gyaran jiki hakanan ya bayar kudin da suka tatsar Mata a jikinsa ya haura million biyar sannan suka sanya ranar tariyarta wata daya baiso hakan ba so yayi subashi matarsa kafin ya koma California amma sunqi dole ya shirya ya tafi zuciyarsa babu dadi saboda yana iya jure shariyar kowa amma banda ta Umaimah azabtuwa yakeyi sosai koda ya koma yayi tunanin ko wayarsa zatake dagawa tunda matsayin miji yake a gurinta amma taqi ya tura mata text har ya gaji ya zuba mata ido sau daya ta taba daga wayarsa yana farayi mata mgn ta katseshi da cewa “Duk da nasan haramcin da yake cikin neman saki amma yau na nema Hameed domin farin cikinka da nawa ka taimakeni ka sawwaqemin aurenka Allah zuciyata zata iya bugawa idan inajin cewa waini matarka ce" Sosai kalaman suka hargitsa duniyarsa wannan dalilin yasa ya yanke shawarar bazai qara kiranta ba don wataran zata fada masa abinda yafi haka saida yayi sati uku a California sannan ya dawo lkcn saura kwanaki uku tariyar Umaimah a gdanshi tasha gyaran jiki babu qarya hatta gumin jikinta qamshi yakeyi takanas Hajiya ta dauko me gyaran daga Sudan aikuwa fatarta ta gurzu har wani yellow takeyi hatta fitsarinta qamshi yakeyi ko zama Umaimah tayi a guri ta tashi da awa guda idan kazo sai kaji qamshin ya tsumaka yana dirowa qasar da ita ya fara arba lkcn sunyi hutun wata uku na tafiyarsu 400 level tana gda kwance a parlour tana chat bataji shigowarsa ba saida taga inuwa a kanta ta miqe da sauri tana kiran.

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});