Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 100

Chapter 100

Gidan Uncle Return Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

damma ya dage wajan addu'a da neman zabi da sauqi gurin ubangiji yana kuwa samun sauqin sosai duk da yasani son Umaimah bazai taba barin jininsa ba domin dashi aka halicceshi. Hakan kuwa akayi ana sallamarsa daga asibiti yayima Daddy bayanin komai ya bashi goyan baya har dashi suka tafi qauyen Ghabriel garin da kakan Dr Ammar yake suka samu karamci sosai sukayi masa bayani ya cajeshi tsaf sannan ya dorashi akan magani ya fada masa zaiyi wata biyu anan baija ba saboda bama ya buqatar zaman 9ja din kwata² yana karbar maganinsa yana warwarewa sosai. Watan auren Umaimah da D.S bakwai lkcn tanada cikin wata biyar sosai d.s ya dauki so da qaunar duniya ya dorawa cikin jikinta bashi da mgn sai tasa a lkcn kuma tana 300 level a jami'a tare suke fitowa kullum kowa yana yabawa soyayyarsu da kulawar da yake bata a lkcn ne kuma wata qaddarar ta fado rayuwar Ahlin Hameed Shuwa ranar wata juma'a Hajiya tana kitchen tana girki Nihal da Shurafah suna kitchen din suna wasansu saboda Maliha da Shuraif suna gdan Aunty Zarah kawai sai aka kira Hajiya a waya bisa tsautsayi ta fita tabar yaran a kitchen fitarta keda wuya Gas din yayi wata bindaga gobara ta tashi ta kama wani bangare na gdan ihu Hajiya ta rinqayi tana salati daqyar yan kwanakwana suka kashe gobarar amma abubuwa da yawa sun qone a gdan harda asarar rayuka biyu Nihal da Shurafah. Wannan mutuwa ta girgiza mutane sosai Daddy ne ya hana a fadawa Hameed ita kuwa Umaimah sai Mijinta aka fadawa shine yaje ya daukota ya kawota gdan tun daga qofar gdan tasan wani abu ya faru gabanta ya yanke ya fadi tayi baya luuuuuu zata fadi yayi saurin tarota amma ta suma nan fa hankali ya dawo kanta ya dauketa shida Hajiyansa da aunty Zarah suka tafi Asibiti bayan wani dan lkc ta farfado tana tashi ta riqe hanunsa ta fashe da kuka tace “don Allah Sulaiman kada kacemin Abdulhameed ya mutu zuciyata bugawa zatayi..." Rufe mata baki yayi yace “ai dama na sani nasan tunaninki kenan to ki kwantar da hankalinki bashine ya mutu ba..." katseshi tayi da cewa “to waye waye ya mutu D.S?" Share hawayen idonsa yayi yace “Nihal ce da..." Saikuma yayi shiru daya tuna irin son da takewa Shurafah kullum burinta akan Shurafah ya qare katse masa tunanin tayi da cewa “dawa kuma D. S?" Janye hanunsa yayi daga nata ya fice daga dakin da sauri Aunty Jameelah tace “kunyi Mata shuru ai dolene ta sani Umaimah hqr zamuyi Allah ya karbi rayuwar Nihal da Shurafah jiya da magaruba sakamakon gobara da sukayi a kitchen kiyi hqr Allah zai mayar miki da wadda tafita” ajiyar zuciya tayi tana kallon Aunty Jameelah tana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un” iyakar abinda take furtawa kenan har zuwa yamma da D.S ya dawo likitan ya sallameta suka tafi gdan rasuwar ta wucce akayi zaman uku da ita taso tayi kwana bakwai amma ya hanata yace ta dawo ana gobe bakwai din. Haka kuwa akayi ana gobe bakwai da kansa ya kawota tunda ta shigo unguwar taji gabanta yana faduwa hakadai ta daure ta rinqa yi masa yaqe suka fito yana riqe da hanunta saboda cikinta yayi nauyi da girma sosai kamar yakai wata tara bayan yanzu ne ya shiga na takwas tana daga qafarta daqyar suka shiga parlourn yanata zuba mata sannu yana riqe da jakarta dagowa sukayi a tare idonsu ya sarqe da juna taja baya da sauri ta shige jikin D.S inda shikuma ya miqe da sauri yana nunata da yatsa yana kallon cikinta yace “Blo... bloody ciki......." *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* [2/2, 8:49 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_* Yana fadin haka ya nufi qofa da sauri ya fice daga dakin ko hanun da D.S yake miqa masa bai kulaba wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata ya kamata ya zaunar da ita yace “to ya isa haka kinsan banason kuka ko?" qoqarin tsayar da kukan ta farayi daqyar ta tsayar da kukan yayi murmushi ya miqe yace “zanje gda ke sai yaushe?" Qasa tayi da kanta tace “jibi" kallonta yayi da sauri yace “aa gobe dai" batayi masa musu ba ya juya ya fice bayan sun gaisa da mutanen dake dakin sai lkcn ta samu damar gaisawa da kowa ta miqe da qyar ta shiga dakin Hajiya ta kwanta tana tunanin Uncle dinta zuciyarta na fada Mata ta tashi tabishi taje taga halin da yake ciki amma saita dake kawai tayi kwanciyarta har dare ya fara ta fita ta koma parlourn Aunty Zarah ce kawai saboda Aunty Jameelah tun uku ta tafi sai Hajiya Kaka da maqota dayake aikin abincin sadakar duk kwangila suka bayar suna zaune har sha daya sannan kowa yaje ya kwanta itama kwanciyar tayi amma zuciyarta taqi hutawa koda D.S ya kirata ma daqyar ta daga tace masa bacci takeji sukayi sallama ta aje wayar tanata karanta wasiqar jaki ranar daga ita har Hameed babu wanda ya rintsa shi gani yake Umaimah taci amanarsa data yarda wani ya kwanta da ita harma yayi mata ciki wannan ciki ya tsone masa ido da yasan mugun ganin da zaiyi kenan da bai dawo 9ja ba yanda yakejin ciwon abinda ya gani a jikin Umaimah bayajin ciwon mutuwar yaran nasa haka saboda yasan su lkcnsu ne yayi amma ita ta manta da halaccin da yayi mata taje ta bawa wani kanta yanzu abinda yakeji a jikinta shima Sulaiman abinda yakeji kenan? Wani kishi ya taso masa daqyar ya rinqa danne zuciyarsa da qarfin addu'a. Washe gari akayi sadakar bakwai basu hadu da Hameed ba harta gama zamanta a gdan D.S yazo daukarta ta hado shirginta ta fito yana yana riqe da hanunta yana zuba mata zance tana dariya Hameed din ya shigo a motarsa sabuwa dal yayi parking duk da batasan shi bane amma saida gabanta ya fadi ta kalli motar sosai jikinta yana bata na cikin motar ita yake kallo. Ilai kuwa itadin ya zubawa ido yanajin wani abu yana tasowa qirjinsa zuciyarsa tana tafasa yanda suketa dariyarsu da Sulaiman din yana jamata karan hanci har kuma dan jaraba irin tasa ya kasa daina kallonsu yana qara tsinewa Salma data zama sanadin rabashi da farin cikinsa qiri² Umaimansa tafi qarfinsa yanason yaga ya cireta a ransa amma ya kasa hukunci ya yankewa zuciyarsa na barin qasar gaba daya dama ya samu aiki a World Bank of America da yace bazashi ba amma yanzu dole ya hada komatsansa ya tafi can qila ya samu sauqin rashinta saboda yasani Umaimah batada ta biyu a gurinsa har yau idan ya kwanta tunanota yakeyi da irin sadaukarwarta ga farin cikinsa. Buruka da yawa daya dauka akan rayuwarsa da bloody dinsa yanaji yana gani sunbi ruwa wai yau bloody dinsa ce da cikin wani a jikinta har tana ganinsa tana razana to meye ma ya razanata dashi? Tambaya ce da bashi da amsarta tashin motarsu ne ya dawo dashi hayyacinsa ya buga kansa a sitiyarin motar tare da dukan qirjinsa yana kiran “ya rabbih" yana hawaye masu zafi yace “Allah Kaine ka halicci zuciyata da son baiwar nan taka Allah kasani bani na dorawa kaina ba kaine ka jarrabeni Allah ka ciremin ita a raina Allah meyasa kullum

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});