Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Gidan Uncle Return Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suna fita basu karya ba kawai saboda sakacin uwarsu kama hanun yaran yayi yace “kuyi hqr Auntynku batada lfy tana asibiti kuzo muje kuganta sai kuci abinci acan" murna suka hauyi da tsalle da kansa ya cire musu kayansu yasa musu wasu ya jasu suka fice daga gdan suna zuwa asibitin ya nuna musu dakin suka shiga da gudu lkcn an cirewa Umaimah roba ta biyu ta jinin tana zaune ta jingina da pillow da gudu suka nufeta suna murna suna tsalle itama taji dadin ganin yaran saboda ta saba dasu koya ta yini bata gansu ba sai taji babu dadi haurawa sukayi saman gadon suka rungumeta Maliha tasa kuka tace “Aunty shine jiya Uncle ya daukeki kika tafi kika barmu kikaqi dawowa kiyi mana break yau sai haka muka tafi bamu karya ba nayita kuka a makaranta inajin yunwa” Nihal ce me wayo tace “Aunty kin rame kinyi fark meye yake damunki aka kawoki asibiti?” murmushi tayi vta shafa kansu tace “banida lfy ne amma naji sauqi da ganinku kunajin yunwa ko?" Daga Mata kai sukayi tace “no wonder indai yarana sunajin yunwa Ina ganewa Hajiya dake zaune tana kallonsu tana murmushi tace “kaji yan jakar uba ina iyayen naku da suka barku da yunwa” kawar dakai Umaimah tayi tace “mudai ki bamu abinci yarana suci Hajiya idan sunci sayi miki bayani” Nihal ce tace “mu Mom dinmu bata sonmu yau ma duka tayi mana saboda mun tambayi ina Aunty” Daidai lkcn ya turo qofar ya shigo tare da sallama dago kanta tayi da sauri idonsu ya sarqe guri guda yanayi mata kallonsa me narkar da zuciya murmushi yayi mata tare da ajiye kayan daya dauko mata da shopping din da yayo yace “Hajiya sannu da qoqari yame jikin?" Ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa abincin ta zubo jallop din shinkafa ce data wadatu da alayyahu da kifi banda sai qamshi takeyi ta miqawa Umaimah ta karba tare da zaunar da Maliha ta fara basu abincin a baki sunata zuba mata santi itadai batace musu komai ba saboda yanda takejin qwayar idonsa na yawo a jikinta muryar Hajiya ce ta katseta tace “idan kaga dama kaje Daddyn ku yana nemanka yanzun nan ya fita zashi gdanka” amsawa yayi da “to” ya miqe yace bari naje na biyasu kudinsu na dawo dakatar dashi Hajiya tayi tace “aa aikai ka gama aikinka saura namu ubanka ya biya komai" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace “amma Hajiya..." Dakatar dashi tayi da cewa “karkace min komai Hameed wlh da zaka yarda ma daka daina zuwa inda nake saboda idan na ganka jinake kamar na kasheka” *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* *🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊 ( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_ *GIDAN UNCLE* ( _Love and romantic story_) *SHORT AND TRUE LIFE STORY* *MALLAKAR* 👇🏻 *FAUZIYYA TASI'U UMAR* *®FAUZAH* Wattpad👉🏻 realfauzah www.fauzahtasiu41@gmail.com Alhmdllh a madadina da iyalaina munayiwa daukacin al'ummar duniya barka da shiga sabuwar shekarar gogerioun calendar duk da dai mu munci wata hudu a tamu ta musulumci Allah ya hadamu da alkhairan cikinta sharrikan dake tattare da ita Allah ya kade manasu yanda muka shigeta lfy Allah yasa muga qarshenta lfy idan kuma bamu da rabon gani to Allah ya karbi ranmu muna cikin musulumci muna masu aikata ayyukan alkhairi sannan yasamu a ceton Muhammadur rasulullahi (S.A.W). *PAGE ELEVEN* A salube yake kallon Hajiya lallai ta dauki lamarin nan da zafi saboda tunda yake da ita ko baqar mgn bazai iya tuna ranar data fada masa ba amma yau gashi tana neman tsine masa, cikin rashin qarfin gwiwa ya matsa jikin gadon na Umaimah yace “sannu Babyn Uncle ya jikin yanzu inane yake miki ciwo?” ya fada yana dora hanunsa a saman kanta ajiyar zuciya sukayi a tare cikin sanyi muryarta tace “da sauqi” murmushi yayi yace “ok kuzo mu tafi kada ku dame Aunty kunga batada lfy ko?” Nihal ce tace “Mudai anan zamu zauna gurin Aunty da safe ta dafa mana tea tayi mana wanka" Maliha kam kuka tasa wai a dole bazata koma gurin uwarta ba. Daqyar ya shawo kan yaran suna kuka suna komai yajasu suka fice daga dakin itama Umaimah gawayen ta share batason ko kadan taji yaran suna kuka jinshi take har cikin lakarta, Hajiya kam haushine yakusa kasheta ita a tunaninta mgnr data fadawa Hameed dince tasa Umaimah kuka. Kwanansu daya a asibitin yazo da safe dazai tafi aiki ya dubata ya jima sannan ya tafi office a CBN Kano yake aiki, bayan tafiyarsa babu jimawa Dr Saleem ya basu sallama suka tafi gda yayar Hameed Aunty Zarah tazo gdan saboda Hajiya ta kirata ta zayyane mata komai suka hadu a parlour sukayita Allah wadarai da abinda Hameed yayima Umaimah abin takaicin harda Daddy shima ya biye musu yace “wlh badon Hameed dana bane babu yanda zanyi dashi dasai nayi qararsa an fiddawa marainiyar Allah haqqinta jiya fah tsabar ya rainamin hankali na kirashi inayi masa fadan kuskuren da yayi sai cemin yayi shifa baiyi wani laifi ba Umaimah matarsa ce laifinsa daya daya boye mana gsky danaji rainin hankalin nasa yayi yawa sai nace ya tashi ya bani guri kawai saiya fashemin da kuka waishi ba mazinaci bane idan bamu yarda da abinda ya fada mana ba mubashi dama ya gabatar da wasu daga cikin shaidun da suka shaida daurin auransa da Umaimah fada na haushi dashi kamar zan cinyeshi amma bai fasa fadamin ba shifa matarsa yayi mu'amala da ita ba wata ba har yana neman yimin rashin kunya wai gobema idan yana buqatarta zai nemeta yayi duk abinda yaga dama da ita tunda shi yasan ba zina yakeyi ba saboda haka Hajiya sai kinsa tsaro sosai akan yaronnan saboda idan kikayi sake zaa samu matsala tabbas shima mgnrsa abar dubawa ce saboda haka zanyi binkice sosai kuma nace ya gabatar min da shaidunsa nanda kwanaki uku idan ba hakaba zan sauki matakin shari'a akansa” Yana fadin haka ya tashi ya nufi samansa itama Umaimah miqewa tayi daga jikin Hajiya ta shige dakin da idan tazo take zama a ciki ta kwanta itadai zuciyarta babu dadi kwata² batajin dadin yanda suke aibata Uncle din nata saboda koba komai yayi mata abubuwa da yawa da bazata iya mantawa dashi ba, tana wannan tunanin wayarta tayi qara ta dauka da sauri taga qawarta ce Sa'ud da sauri ta kara a kunnenta tace “Hello Sa'ud kizo gdan Hajiyata don Allah yanzu inason ganinki" tana fadin haka ta kashe wayar tananan kwance baafi 20 minutes ba taji muryar Sa'ud din suna gaisawa da Hajiya, Shigowa tayi tare da mayar da qofar ta rufe ta zubawa Umaimah ido tare da cewa “nashiga uku Umaimah meye ya sameki haka kika rame?" Lumshe idonta tayi tare da miqewa zaune tace “meyema bai sameni ba Sa'ud bari nayi na cikin Uncle” nan ta kwashe komai ta fada mata tace “Sa'ud nifa Ina tunanin abinda Uncle yake fada gsky ne saboda shekara daya baya munje Maiduguri lkcn dagani saishi sai yaran Aunty Sadiya qin zuwa tayi tace aiba taron family dunsu bane Ina kwance nayi matashin kai da cinyar kaka ya shigo parlourn tunda ya shigo naga yanamin kallon qurullah hankalinsa gaba daya yanakan qirjina saboda rigar jikina ba wata ta kirki bace kuma ko bra

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});