Chapter 107
Chapter 107
Daddy fitowa da sauri daidai lkcn da Nawwas ya fito yanz rarrafe ya shige jikinsa qanqame yaron yayi yanabin iyayen nasa da kallo zuciyarsa na ciwo yace. “Fisabilillahi Daddy adalci kenan kubar Umaimah ta rinqa kwashe² kowanne kare doki yanzu wannan kuma me yazoyi gdan nan?" Hajiya ce ta tafa hanu tace “Heee Allah na dawo inji dan cirani yanzu Hameed sanyata zamuyi a gaba mu kwadata muci ko kuwa hanata zabin ranta zamuyi shita kawo tace tanaso mgn har tayi nisa ma aure saura sati daya kayi hqr ka rungumi sorry Umaimah ta daina yayinka...." Daga mata hanu yayi a fusace ya miqe kamar mahaukaci yace “ya isa Hajiya basai kin kasheni ba naji naji abinda kikeso kice amma wlh tallahi bai isa ya auri matata ba nagaji da binku din da nakeyi kuna neman turani kabari nine na farko kuma nine na qarshe ko Sulaiman don babu yanda zanyi ne na barshi yayi shuka a gonata amma wannan kodadden balaraben bai isaba wlh saidai muyi mutuwar kasko zan saceta nabar qasar da ita idan yaso kowa ya huta kuma wlh Idan na dauketa guba zan dura mata sannan nima nasha tunda naga Allan ma bazai kasheni na huta ba gara na kashe kaina da kallon wannan ta'addancin da akeyimin ni banida gata banida masu sona bani da wanda zai tausaya min bayan kunsan komai...." Katse mgnr yayi saboda numfashinsa da yake sama da sauri ya dafe qirjinsa yayi waje a guje da sauri Daddy yabi bayansa ya riqo hanunsa ya juyo da sauri zuciyarsa na tafasa idanunsa na fitar da hawaye yace “ka qyaleni Daddy wlh kasheta zanyi na kashe kaina kowa ya huta na gaji Daddy na gaji wanne irin rarrashi ne banyi yarinyar nan ba wanne irin qasqantar dakai ne banyi mata ba koda ace a cikin hayyacina nayi mata laifin da take iqirarin nayi mata indai tanada imani ya kamata ta tausayamin....” Daidai lkcn sukayi sallama Prof Khair ya shiga motarsa ya tafi ita kuma ta tako cikin takunta na isa ta raba ta gefensu zata gifta ya cafko hanunta da qarfi ya finciko ta ta fada jikinsa babu kunya yasa hanu ya matseta yace “wlh tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa babu wanda ya isa ya rabani dake don kece rayuwata Umaimah ko zaa kasheni kuma ko zan rasa komai nawa a yau sai an dauramin aure dake idan kuwa akaqi wannan karon zan saceki sacewar da babu wanda zai sake ganinki har abada" yana fadin haka ya fizge hanunsa daga na Daddy Hajiya tayi saurin riqeshi tace “Alh kayi wani abu kace wani abu wlh Hameed ya haukace baa cikin hayyacinsa yake ba zai iyayin komai Alh yaronnan mukaishi asibitin mahaukata a duba kwalwarsa" daga mata hanu yayi yace. “Babana shiga gda zaayi yanda kakeso a yau da wani bacin ran gara wani Umaimah zo inason ganinki" sakinta yayi ya zube a gurin yana kuka me gigita tunanin kowa da ban tausayi yace “babu inda zani Daddy ni zakayi wa wayo wlh yau saina kwana da Umaimatu kota halin qaqa nasani tana sona toshewar qwalwarta yasa ta kasa fahimtar hakan waye zai aureta ya riqe mana yayanmu idan bani ba so take dole saita tozarta amanar Allah so take dole sai twince sun tashi sun fuskancin cewa su marayune meyasa zata bijirewa saqon zuciyarta bayan nasan babu son kowa a cikinta sai nawa meyasa bazaku kalli idonta ba kalli Daddy Hajiya kalli idonta wlh sona kawai nake hangowa a ciki so take ta kasheni ta kashe kanta bayan tasan ba cikkakiyar lfy ce dani ba itama kuma nasani zuciyarta ta kamu da irin ciwon da yake damun tawa zuciyar" Daqyar Daddy da Hajiya suka bambareta daga jikinsa suka jata suka shiga da ita gdan suka kulle parlourn ya miqe yana buga qofar da qarfi yana cewa “ku bude bude Daddy zan balle qofarnan wlh saika bani matata ai donni kadai aka halicceta bazan yarda ku rabani da matata ba....." Surutai dai rututu na rashin kan gado haka Hameed yakeyi kamar zautacce yana dukan qofar kamar zai balleta saida ya gaji ya hqr ya fita ya shiga motarsa ya nufi gdansa ya bude dake an gama aikinsa tsaf har ya zuba komai na amfani ya fada daya cikin dakunan ko qofar bai rufeba jikinsa yana bari zuciyarsa na tafasa yana dafe qirjinsa da qarfi yana nishi da kakarin aman wahala. Shi kuwa Daddy yana shiga da ita ya zube akan gwiwarsa ya ruqo hanunta yace “badon ni ba badon na isa dake ba don girman Allah Umaimatu ki duba maraicin twince da wasiyyar mijinki Sulaiman ki bani dama ta qarshe na daura auranki da Hameed yaron nan ya garu sosai sonki zai kasheshi Umaimatu ya zakiyi da haqqin ran dan'uwanki idan ya mutu saboda ke bayan kinada yanda zakiyi ki taimakesa...." zubewa tayi ta rungume Daddy tana kuka me ban tausayi tace “kada ka qara roqona akan wannan Daddy zan iya bada rayuwata na fanshi taka balle wannan wlh indai hakan zai zama farin ciki a gareka na amince da auren Abdulhameed indai hakan zai zama farin cikinka na amince wlh na amince Daddy" tana fadin haka ta miqe da sauri ta fada daki saman gado ta fashe da wani kuka me ciwo tana cewa “Allah ka yafemin laifin da nayi maka ka sake jarabta ta da auren Abdulhameed Allah ka dubeni ka kawomin dauki cikin buwayarka Allah na roqeka kabani ikon yima mahaifina biyayya" A wannan daren Daddy bai zauna ba yana fita ya kira Yusuf da mijin Aunty Zarah a masallaci bayan sallar magaruba ya fadawa limamin cewa yanada daurin auren yayansa biyu yabada komai aka daura auran akan sadaki dubu dari biyu suna shiga gdan ya fadawa Hajiya takuwa rangada guda ta daga hanu sama tace “Allah na gde maka daka sake gwadamin wannan rana Umaimatu na matar Hameedu na wayyoh dadi kasheni na huta" tasowa tayi zata fito taji mgnr Hajiyan ta koma da sauri ta zauna tana fadin “Hasbunallahu wa ni'imal wakil Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Allahummah ajjirni fi musibati wa'akalifni khairin minha yanzu nice matar Hameed mutuwa ta tazo ya zanyi da jarabar Hameed" shigowar Hajiya ne yasata dagowa ta dubeta hawaye nabin kuncinta tace “Hajiya yanzu shikenan an daura aurena da Hameed Hajiya kwanana ya qare nama sani bazan iya dauke lalurarsa ba kamar yanda na dauka a baya Hajiya ki taimakeni...." Rufe mata baki tayi da hanunta tana girgiza mata kai tace “kiyi hqr Umaimah Hameed zai canza baza kiyi irin zaman da kukayi a baya ba wlh ni kaina da farko banyi farin ciki ba amma yanzu ina farin ciki sosai saboda na yarda kuma na gasqata Hameed sonki yakeyi da gaske baso irin na sha'awa ba" da wadannan kalaman tayita rarrashin ta har ta samu ta saurara da kukan dama ta fara shiryata da magungunan su kasancewar saura sati daya aurenta da prof Khair saboda haka ta dora daga inda ta tsaya tunda tariga tasan halin dannata ba sauqi gareshi ba. Yusuf ne ya nufi gdan Hameed din da nufin yi masa kyakkyawan albishir get man din ya tambaya ko megidan yana ciki yace masa eh yayi parking ya shiga yanata kiransa yana cewa “dallah malam ka fito haukanka yayi rana Allah dai ya yarda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111