Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 102

Chapter 102

Gidan Uncle Return Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kafin su ankara ta janye yadin da aka lullubeshi ta matsa ta qara kallon fuskarsa da gaske ba gizo ba Sulaiman ne kwance babu numfashi a jikinsa fuskarsa wasai da murmushin sa na rahama ta dafe qirjinta tare da furta Innanillahi wa innah ilaihirraji'un tayi baya luuuuuu ta zube a qasa itama qanwar gawa da sauri Daddy da Hajiya sukayo kanta aka dauketa itama aka shiga da ita ciki aka kwantar da ita a gado babu irin ruwan da basu yayyafa Mata ba amma taqi dawowa hayyacinta hakanan aka kimtsa Sulaiman aka daukeshi aka kaishi gdansa na gsky zuciyoyi na kukan rashin managarcin mutum salihin bawa wanda bashi da tamka Hajiya Sa'adatu fadi takeyi. “Wlh babana da nasan mutuwa zakayi da bazan takura maka kaje gaisuwar nan ba saida ka nunamin bakason tfyr na takura maka dake kaidin dane me biyayya haka ka tafi yanzu ka mutu babana ka mutu kabar matarka abar qaunarka ka mutu kabar yayanka masu kwanaki goma sha daya a duniya ka mutu ka barni kabar yan'uwanka kabar abokanka kabar kowa babana wayyoni kaina wayyoh Umaimatu dole ki suma kinyi rashi Umaimatu wannan mutuwa takice ke akayiwa mutuwa kin rasa miji me sonki da qaunarki kin rasa miji me tausayinki dason farin cikinki Umaimatu Allah ya mayar miki da alkhairi Umaimatu na rasaki yanzu kenan na rasa sukura ta qwarai wadda ta ginamin dana da tsarkakkakiyar soyayyah Allah na gde maka da baka dauki rayuwar Sulaiman ba saida ka cika masa burinsa na ganin yayansa" Bayan ankai Sulaiman makwancinsa aka dauki Umaimah aka tafi da ita asibiti tashin hankalin dasu Daddy basu taba shiga wannan karon shi suka shiga ba akan Umaimah yau shi suka shiga Umaimah ma da ciwon zuciya wannan wacce irin jarabta ce suke fuskanta ne. Bata samu kanta ba saida tayi kwanaki bakwai saboda kumburar da zuciyarta tayi twins kuwa sai madara ake basu bayan ta dawo hayyacinta mutuwar mijin nata ta dawo mata sabuwa tayi kuka kamar ranta zai fita tanajin dama ita ta mutu ta huta daqyar Hajiya ta shawo kanta da dadadan kalamai da misalai kwatankwacin nata da kuma irin nasarorin da zata iya riska a rayuwarta da wadannan kalaman Hajiya da Daddy sukayita kwantar mata da hankali amma duk sanda ta kalli Nawwas da Nawwarah sai tayi kuka saboda tunawa da kalmarsa ta qarshe yayana amanane a gareki inasonki Umaimah” wannan dalilin taci alwashin zata tsaya ta riqe masa amanar yayansa koda kuwa zata mutu babu aure ita aurenma ya fita a ranta tama hqr dashi gara ta zauna tayi rayuwarta ita kadai tunda bai karbeta ba. Haka su Hajiya suka tafi da ita gda aka gyara mata dakinta aka zuba mata komai sabo duk wani abu da zai cire mata kewa saida suka sanya mata ga mai rainon twins dinta ita dakinta guda sannan ga Maliha da Shuraif da suke dauke mata kewa lkcn Allah yasa cikin hutu suke koda aka koma mkrntar ita bata komaba saboda abin na gdane ita daluba ce shi kuma marigayi D.S malami ne da sukeji dashi a Skyline University sunji mutuwarsa sosai hukumar makarantar tayi rawar gani sosai wajen ganin sun yiwa iyalan D.S wani abu aikuwa sunji dadi koda akazo rabon gado da Abba da Hajiya Sa'adatu cewa sukayi sun yafewa Umaimah da yayanta komai. Rayuwar haka taci gaba da tafiya bason raiba sai bayan wata uku da rasuwar D.S sannan Daddy ya sanar da Hameed ya tausayawa twins tare da jin ninkin qaunarsu a zuciyarsa yasan rabonsu shine ya rabashi da mahaifiyarsu sannan rabonsa dabai qare a jikinta ba shine ya kashe mahaifinsu" da wannan tunanin ya biyo jirgi ya dira a 9ja batare daya fadawa kowa ba suna zaune a parlour da hijjab dinta na masu takaba ya shigo da sallamarsa Maliha da Shuraif sukayi tsalle suka rungumeshi Twince kuwa da suke koyon zama sai bangale masa baki sukeyi murmushi yayi me hade da kwallah yana tuna irin wulaqancin daya rinqa yiwa mahaifinsu lkcn da yana neman auren Umaimah ya sunkuya ya daukesu ya rungumesu a jikinsa wani kuka me qarfi ya kwace masa yayi saurin tashi daga gurin ya shige dakinsa da yaran ko gaisawa da Hajiya bai iya yi ba balle Umaimah tasaran zaiyi mata ta'aziyyar mijinta, itama batasan sanda mikin mutuwar D.S ya dawo Mata sabo....... *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* [2/3, 11:53 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_* Miqewa tayi ta shige dakinta ta kwanta tanajin haushi da tsanar duk wanda ya kasa yi mata gaisuwar rashin mijinta da takejin bazata mayar da kamarsa ba a duniya. Shima ya jima yana kallon Nawwas da Nawwarah yana kuka yaran sai wasa sukeyi da gashin qirjinsa sunayi masa dariya kamar Nawwas da mahaifinsa har tayi yawa kamar dai shida Shuraif abubuwan da yayiwa D.S suna sake bijiro masa musamman haduwarsu ta qarshe lkcn mutuwar Nihal da Shurafah da yazo daukarta yana ganinsa yana miqa masa hanu ya bige hanunsa ya wucce hakan baisa yaji haushi ba washe gari ma daya dawo karba mawa Umaimah yajin daddawa lkcn da cikin yaran saida ya sake miqa masa hanu da yaqi bashi nasa kawai sai yaga ya share qwallah ya rungumeshi yace. “Kada ka qullaceni a zuciyarka Yaya banine na rabaka da Umaimah ba qaddara ce kuma nima itace ta hadani da ita wlh da inada ikon halatta maka Umaimah tun kafin muyi aure zan halatta maka ita saboda nasani kaine Umaimah takeso kaima kuma ita kakeso amma Ina banida damar hakan abu dayane zai hanani dawo maka da Umaimah saboda ina burin rayuwarta ta samu farin ciki Hameed ka qaddara idan Umaimah rabonka ce zata dawo gareka amma bayan qasa ta rufe idona saboda a tsarin rayuwata mace ko cutar dani take indai bazata cutar da Umaimah ba zan rayu da ita balle Umaimah da kullum burinta farin cikina Hameed idan na mutu bana fatan kabar Umaimah ta auri wani bakai ba saboda Ina kishinta kuma nasan zaka riqemin dana saboda kanada imani kuma kanason uwarsu" Yana fadin haka ya sakeshi ya shiga motarsa yaja yana daga masa hannu yanayi masa murmushinsa me tsayawa s zuciya “kyakkyawan namiji me kyakkyawan hali da sanyin zuciya ya mutu" ya fada yana rungume yaran a jikinsa yace “dole Umaimah tayi kuka saboda tayi rashin miji na qwarai amma nasani bazai fini sonta ba kuma zanyi iyakar qoqarina naga na bata farin ciki fiye da wanda yake burin bata zan riqe maka yayanka kamar nawa har qarshan numfashina Sulaiman Allah ya gafarts maka" Yana mgnr yana kuka da shishi kamar qaramin yaro tunda yake baitabajin mutuwar data girgiza shi kamar ta Sulaiman ba ko mutuwar yayanss biyu batayi masa dukan mutuwar Sulaiman ba musamman idan ya kalli yaran sai yace “yanzu fah yanason rayuwa dasu Allah ya karbi rayuwarsa ko? Meyesa a duniya mutanen kirki basa dadewa?" Ya tambayi kansa tare da kwantar da yaran da sukayi bacci a gefensa ya ja blanket ya rufesu ya tashi ya dauro alwala yayi sallar Isha yayi shafa'i da wuturi yaci gaba da addu'a rabin addu'ar tasa ga Sulaiman ne yana kuka yana roqon Allah ya bashi hqr da kyawawan halaye da kyakkyawar mu'amala irinta Sulaiman. Bayan ya gama ya fita ya nufi kitchen domin dauko fresh milk sukayi clear da ido ido cikin ido amma sai ta

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});