Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Gidan Uncle Return Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

burin mallakar irinsa kuma namijin da bazaki qara samun irinsa ba a duniya ke bari nayi miki kalmar qarshe Umaimah wallahi tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa bazaki iya zama da kowanne namiji ba sai Hameed shine ya fara saninki dashi kika saba kuma shine daidai dake saboda danshi kadai aka halicceki kamar yanda yasha fadamin"...... _Kuyi manege da wannan_ 🙈 *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* [1/22, 8:35 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GIDAN UNCLE* Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566: *PAGE FOURTY TWO* Kuka ta sake saki me ciwo tana girgizawa Aunty Jameelah kai, sake Mata hanu tayi tace “bazanyi miki dole ba kamar yanda Daddy yayi alqawarin bazaiyi miki dole ki yarda ki auri Hameed ba amma ina tausayawa rayuwarki a gdan wani ba Hameed ba domin shine mahadinki shine abokin rayuwarki kuma shine qaddararki ko ki yarda ko kada ki yarda Hameed nakine kema tasace kamar yanda yasha fadamin danshi kadai aka halicceki saboda haka kiyi gaggawar dawowa hayyacinki kafin kiyi abinda zai zame miki ciwo har qarshen rayuwarki” Tana fadin haka ta dauke Shurafah a jikin Umaimah ta cire mata Pampers tayi mata tsarki karbarta Umaimah tayi ta fita zuwa dakin Hajiya ta bude ta shiga da sallamarta tasa kai ta shiga turus taja ta tsaya ganin Hajiya zaune gefen gado ta hada kai da gwiwa tanata gursheqen kuka. Jiki a matuqar sanyaye ta qarasa ta tsugunna a gabanta ta kwantar da kanta a cinyar Hajiya kawai itama ta saki kukan da sauri Hajiya dago tace. “Ke meye hakan Umaimah?" Cikin kuka tace “kiyi hqr don Allah Hajiya insha Allahu Uncle zai samu lfy zai warke kuma zaici gaba da rayuwa cikin farin ciki kamar baya don Allah Hajiya ki daina kukannan banaso ya kikeso muyi keda zaki rarrashemu" shafa bayanta Hajiya tayi tace “na fidda rai da rayuwar yaronnan Umaimah koda ya farfado idan yaji hukuncin da kika yanke na bazaki qara rayuwa dashi ba zaiyi mutuwar dungurungum saboda nasani kece zuciyarsa Umaimah bazai iya rayuwa babu keba..." Zamowa Hajiya tayi tayi knilling a gaban Umaimah ta ruqo hanunta tace “Don Allah badon niba Umaimah ki taimakeni ki yarda ki rayu da dana kece cikon farin cikinsa Umaimah zan rasashi idan kikaqishi don....." Saurin rufewa Hajiya baki tayi cikin kuka tace. “Kada ki qara hadani da Allah Hajiya ko baki hadani da Allah ba nasani kuma na amince Yayana Abdulhameed mahadin rayuwata ne bazan iya rayuwa babu shiba bansan inason Uncle ba kuma bansan ciwonsa nawa ne ba sai yau dana ganshi Hajiya na shirya sake komawa qarqashin inuwar auran Uncle Hameed indai wannan shine zaisa yaci gaba da wanzuwa cikin farin ciki...." Wata runguma Hajiya tayi mata tana kukan dariya tace “na gde miki yata Allah yayi muku albarka Allah yabawa dan'uwanki lfy kuci gaba da qawatamu da salon qaunarku mai ban sha'awa" murmushi tayi tace “ina Daddy Hajiya?" Ajiyar zuciya tayi tace “yana Riyadh gurin Hameed shida Yusuf" Sunkuyar da kanta tayi tare da qurawa Shurafah idon har yanzu idan ta kalli Shurafah sai taji tsanar Hameed a ranta amma tayi alqawarin kankareta a zuciyarta saboda cikar farin cikin iyayensu miqewa tayi a salube ta kwantar da Shurafah tace “na kawo miki ita ta tayaki hira inason zuwa harami ne Hajiya" murmushi tayi ta matsa kusa da Shurafah tace “ja'ira mekan qwanqwalati bata da aiki sai bacci kamar kasa nidai bansan ina kika debo ragwanta ba iyayenki duk ba ragwaye bane" murmushi Umaimah tayi tace “kun daifi kusa ta kwana tana maki waqa” itama dariya Hajiya tayi tace “to ya zanyi hausawa sunce abin cikin qwai yafi qwai dadi ai Allah ya taimaka saikun dawo” Amsawa tayi da amin sannan ta fice taje ta tarar da Aunty Jameelah har ta shirya suka fito da qafa suka tattaka har masallacin harami suka fara gabatar da ibadarsu kamar kowanne musulmi itadai Umaimah rasa abin da zata roqi Allah tayi banda abu uku yafiya, samun lfyr yayanta da kuma shiriyar yarta Shurafah basu sukabar harami ba saida sukayi sallar asuba da yake tun kwanaki sha biyar da haihuwarta ta tsarkaka sai ciwon dinkin da tasha da har yanzu bai warkeba har zuwa wannan lkcn dingisa qafarta takeyi bata taketa sosai ba. Haka sukaci gaba da gabatar da ibadarsu cikin rashin nutsuwar zuciya saboda itadai Umaimah hankalin ta yaqi kwantawa saboda rashin sanin halin da Hameed din yake ciki ranar da sukayi sati biyu a qasar Saudia ne ranar Daddy ya samu Umaimah a dakinsu shida Hajiya ya dubeta yace. “Uwar masu gida Hajiya ta sameni da wata mgn a baya kinyi furucin bazaki sake rayuwar aure da Hameed ba kuma yanzu naji kince kin janye hakane?" Jinjina masa kai tayi cikin kunya yayi murmushi yace “amma dai ina fatan ba wanine ya takuraki ya canza miki raayi ba?" Sake daga masa kai tayi yayi ajiyar zuciya yace “naji dadin hakan kuma nayi farin ciki da faruwar hakan Umaimah Allah yayi muku albarka ya shiga cikin lamarinku a gobe idan Allah ya kaimu zanje harami a mayar muku da auranku jibi saiku wucce Istanbul zuwa lkcn da zaku dawo komai yayi Normal da izinin Allah" Dagowa tayi da sauri tace “aa Daddy nikam na fasa zuwa Istanbul dinnan ba" kallonta yayi da sauri yace “meyasa?" Qasa tayi da kanta tace “Daddy hankalina bazai kwanta ba ana zuwa yawon shaqatawa ne saboda nishadi toni nawa farin cikin yana asibiti baisan wake akansa ba wlh Daddy koda na tafi hankalina bazai taba kwanciya ba kayimin hqr bazan iya tafiya bansan halin da Abdulhameed yake ciki ba"........ *UMMUH HAIRAN CE...✍🏻* [1/23, 4:34 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U* Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566: Ajiyar numfashi Daddy yayi cike da jin dadi ya miqe yace “shikenan ki zauna Baby bazan miki dole ba amma kinsan bazaku zauna anan ba tunda kun gama umararku zaku koma gda duk halin da ake ciki ma rinqa waya saboda makarantar ki kuma ma jikin Hameed da sauqi tunda yanzu numfashin sa yana fita sosai kuma wasu bangarori na jikinsa suna motsawa ba kamar baya ba" Ficewa yayi ita kuma ta miqe ta haye gado ta kwanta inda Hajiya ta dauki Shurafah suka fice. A washe garin ranar aka sake daura auranta da Hameed itadai a ranar yini tayi zuciyarta babu dadi hakanan bata farin ciki da auran nasu duk da ita kanta tasani yaudarar kanta ta rinqayi a baya da takejin kamar zata iya cireshi a ranta, kwana hudu suka qara a qasar Saudia suka dauko hanyar 9ja badan tanaso ba saidon batason yin musu da iyayen nasu musamman Daddy daya matsa akan sai sun tafi kwana uku ta huta Aunty Jameelah ta kama hanyar gdanta ita kuma ta shirya domin fara halattar makaranta micro biology take karanta kuma tanajin dadin course din sosai da yake Umaimah bamai hayaniya bace yasa ko qawa batayi a skul din ba daga ita sai Shurafah dinta suke harkokinsu yarinyar tayi qiba sosai tayi wayo cikin wata biyun idan ka ganta zaka dauka tayi wata hudu yarinya kyakkyawa abarso ga kowa ga Umaimah da sanin darajar kwalliya wa yaro kullum cikin ado Shurafah take hakan yaja Mata farin jini gurin yammatan department din nasu kowa Shurafah hakan yanasa Umaimah taji dadi

Table of Contents

Chapters

111 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});