Chapter 92
Chapter 92
juna sani a jihar Katsina, lallai bana buk'atar yama k'arasa”. Kusan a tare sukace Alhaji Shehu Darma kuma?. Ficewarsa yayi batareda yabasu amsaba balle su sami k'arin bayani. baki bud'e Nuren da Muftahu suka kalli juna, Muftahu yace, “shikuma miye nasa to?”. Cikin jimami Nuren yace, “nima abinda nake son Sani kenan, mutumin da tunda mijin aunty Mimi ya rasu yake fad'i tashi a kanta da yaranta, danma tak'i amincewa ne da aurenta zaiyi, anya kuwa shi yake nufi kodai wanine mai irin sunansa?”. Jiki a sanyaye Muftahu ya yarfar da hannu alamar bai saniba shima. danshi lamarin Galadima yafara bashi tsoro, mutum kamar wani tsohon aljani. Shikam koda yabar wajensu wani office yace Sarkin mota ya kaisa, yakai tsawon lokacin a wajen tareda wani mutum dabazai gaza shekaru 56 ba a duniya, bansan mi suka tattauna ba, dan ba'a bani damar jinba. A wajen yay sallar azhur har la'asar sannan yayo masa rakkiya wajen Motocinsa, saida yaga fitarsu sannan yakoma Office d'in. Daga nan masarauta suka nufa, dan Galadima a matuk'ar gajiye yake, Ya iske sashensa fes an gyara, ko ina yana tashin k'amshi tamkar yadda yake buk'ata, kayansa yacire ya watso ruwa, bai nemi kowa baya ya zauna a falo yana aiki a System, dukda yaga abincin da aka ajiye masa baiko bud'eba balle tunanin cinsa, Yakuma san Aunty Mimi ce zata saka a kawo. Yana tsaka da aikin Sauban ya shigo, bai kallesaba koda ya gaidashi, yadai Amsa. Sauban yace, “yaa Sam tafiyar safe zamuyine goben?”.. Ido Galadima yad'an d'ago ya kallesa, ya maida kansa ga laptop d'in yana fad'in, “Kwana 3 zamuyi ni da kai mu dawo, komanka na gameda bautar k'asa yagama kammaluwa”. Kamar Sauban zai sanya kuka yace, “Amma Yaa Sam su Momma sai abarsu babu kowa?”. “kafin ka girma dawa suke zaune?, Sauban ka kiyayeni, karka bari na fusata akanka, tashi bani waje”. Sauban ya mik'e zuciyarsa na zafi, harzai fita Galadima yace, “zonan”. Dawowa yay yana mirgina kai, batareda Galadima ya kallesa ba yace, kar6a wannan, kaje ka sakashi jikin rigar Abdurrahman ko Amaturrahman ka d'auki Wanda ka samawa d'in kaje sashen Ummu Amaan (gimbiya Zulfa) dashi”. Sauban baice komaiba ya kar6a abinda yabashi mai kama da ma6alli ya fita, ya iske Munaya na barci, yaran kuma na tare da Khaleel dake ta fama jagwalgwalasu, Abdurrahman ya d'auka ya sakamawa ya nad'eshi a showal ya fita...... Nikam wannan gangancin na Galadima ya isheni😨🙆🏽. Bansake jin miya faruba dan banbi Sauban ba nikam, ina tsoron ganin abinda zai hanani barci😌. __________________________ Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri bayan ya dawo daga sallar isha'i, yagama tsaf cikin k'ananun kaya da jacket d'insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan nasa na gwarzantaka ya fito, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k'ofar d'aki zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad'o jikinsa saboda kad'an yarage ta fad'i, k'amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryarta na rawa saboda kuka tace, “yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d'auki zafi”. Baice komaiba ya kama hannunta suka koma cikin d'akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman kayan jikinsa za'a watsa masa ruwan d'umi kozaiyi shiru. Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty mimi, ya fiddo wani kwali k'arami daga aljihun jacket d'insa ya bud'e, k'aramar kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d'iba maganin cikin tsinken da ake bama yara magani ya zubama yaran a bak'i, dak'yar ya shanyeshi. Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa. Yunk'urin amai da yaron keyi yasaka Galadima d'agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k'irjinsa yana hura cikin kunnen yaron a hankali. Tun yana kukan kad'an-kad'an ya koma ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y'an uwansa ya lullu6esa. Ya kalli aunty Mimi yana mik'ewa, “insha ALLAH zai sauka zaza6in”.. Yanda Aunty Mimi kebinsa da kallon tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik'e tabi bayansa a fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba d'azun. “Dakata Sameer”. Cak ya tsaya yanajan hular rigar bisa kansa, amma bai juyoba. “Sameer wai mike damun kankane haka? da zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka?”. Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici yayi, yace, “Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan abinda nakeyi, zuwa nangaba kad'an kuma zaku fahimci komai”. “ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana zamubi”. Agogon hannunsa ya kalla, yace, “yanzu kam inada uzirin fita?”. “fita? Inakuma zakaje a wannan daren?”. Batareda ya tanka mataba yajuya yakama hanyar fita, saida yaje bakin k'ofa sannan yace, “Farauta”. yay ficewarsa. Kasa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta. ****** Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai k'arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da irin kayan hadiman masarautar, rissinawa yay yabashi keys d'in mota. ya kar6a batareda sunma juna maganaba ya wuce. Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud'e ya shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun yafito ad'an hanzarce, motar yabud'e seat d'in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje, kasan d'an bala'innan yanada securitys dake kaimasa rahoto”. Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada motar yafice daga masarautar................✍🏻 “Hummmm! Reader's harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun, sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama”. Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne🤔? Yaya batun kama SD?, wad'anne sarakuna ne Galadima yake zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai?🤔, Yaya batun warkewar Abie da Auren Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu da zuwanta wankan gida? Ko Galadima zai amince?”. Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da ita Munayar ta d'auki alwashi?. Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na 3 kuma na k'arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had'a muku da albishirin zan dingayi a weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk 3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH. Ngd sosai da had'in kan da kuke bani, muje zuwa my guys⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀🥰🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😍😍❤❤❤. Barkanku da juma'a🙋🏻. Musha weekend lafiya⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀ *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92