Chapter 44
Chapter 44
wani abin mamaki da ban al'ajabi. akwai wani d'aurin Aure da mai martaba yace mu wakilcesa ni da Hakeem (Wambai) amma sai Harun da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d'aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d'aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d'aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban kawo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi ya nuna, zuwa can sai shima ya mik'e ya fice, yacemin yana zuwa, fitarsa babu dad'ewa d'ayar wayar Harun tayi ring, ni mutumne dabai damu da shiga abinda babu ruwansa ba, amma a ranar saina tsinci kaina da duba wayar, bansan Number d'inba, amma nasan fuskar wadda take jikin hoton da Number ta bayyana, ba kowa bace face d'aya daga cikin matan Abie na”. “Matan Abie kuma?”. “kwarai kuwa, wannan shine abinda na gani, Wanda ya zaunamin a rai, koda Harun ya dawo yaga wayarsa kusa dani sainaga kamar baiji dad'iba, na bashi ina fad'in hajia ta kiraka, kinga kuwa yanda yanemi zubewa? humm saida Muftahu ya taimaka masa, dana tambayesa se cewa yayi wai tunkan mu taho dama kansa na ciwo, nasan ba haka baneba amma na sharesa. tunda muka taho na lura ana kallon kallo tsakanina Muftahu da Harun, kuma duk sanda hakan tafaru, Muftahu kanyi wani murmushi mai tattare da ma'anoni masu yawa, Wanda har yanzu nakasa fasarasu”. Huci na fidda daga bakina, na koma Inda na taso na kuma zama, shima saiya tako zuwa inda nake, ya durk'usa a gabana tare da d'ora hannayensa bisa Gwiwoyina, idanu na d'ago a hankali na sakasu cikin nashi, k'ok'arin janyewa na farayi, saboda wasu abubuwa danake hangowa cikin idanunsa. Amma saiya hanani wannan damar, yay wani sassanyan murmushi yana fad'in.............🤫✍🏼 Barkanmu da dawowa sister's😄🤝🏻🥰🥰🥰. *_ALLAH k'a gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/3, 10:02 AM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻1⃣6⃣ .................“Kin shirya taimakon Mijinkine Munaya?”. A salon da yay maganar saida tsigar jikina ta tashi, nad'an lumshe idanu sannan na bud'e a kansa, muryata na rawa nace, “ni bansan komaiba. kuma ina ganin a wajen Abie yakamata ka k'ara samun haske ai, tunda yanzu yana magana”. Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo hannuna cikin nashi, “Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne mahaluki ya sansu baki d'aya ba?”. Kaina na girgiza masa a sanyaye. Ya murmusa, tareda d'ora hannunsa saman cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace, “saboda kece wadda zata zama uwar d'ana ko 'yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan wasiyyace ga abinda zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da yayata da k'anina. daga k'arshe ina rok'onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik'irarki a ma'auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to lallai rayukansu tana cikin had'ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu mak'iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana likitoci sunyi gargad'in kar'a tuna masa da abinda ya wuce yanzun, saboda gudun dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN 'DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da kwanjina, Ni nasan Yaya nayi jiyana, yau d'ina ma a wahale take kasantuwa, dan haka nakeson gyara gobena da goben 'ya'yana da dukkan ahalina, inason sanin dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar hankaliba”. Nad'an muskuta domin gyara zamana, ina fad'in “shikenan, amma kabani lokacin please”. “Nabaki”. yafad'a yana mik'ewa tsaye. Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud'ani, hakan bai habashi zama kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi baneba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon mai girman kai. A gaba d'aya yinin wannan ranar cikin nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano wasu abubuwa danaita karo dasu a d'akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d'in da Innarmu ta sakamu masa wani gyaran d'aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma, na dafe kaina saboda saramin d'in da yakeyi, motsin da d'an cikina yayine ya sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d'aya kaina yana Neman kullewa, har a washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya matsa zan d'ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin gargad'i, yace na sauka k'asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa, amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k'ara k'urewa saina d'auki waya na shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya. Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun d'azun yana lura da dukkan motsita ta camera d'in daya ajiye a d'akin wadda koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen samun abinda yake buk'ata ga Abbanta, dan Abba yak'i bashi kowacce k'ofa dazai san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a idanunsa, masu kuma matuk'ar muhimmanci a aikinsa. Wayarsa tai 'Yar k'ara alamar Munaya na sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka mata a wayarta bata saniba yayi, harta gama typing ta tura sak'on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga Munubiya ta turama sak'on, yay hanzarin bud'ewa. (Galadima ya had'a wani tarko a wayar Munaya batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayarta ko fita saiya gansa a wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta rubuta to). _“ ‘Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan abinda muka Sani, danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k'arshe dazai yadda kwallon mangwaro ya huta da k'uda, sweetheart minene shawararki? dan burina dana haife cikinnan auren contract ya k'are a tsakaninmu, domin babu alak'a kuma kenan, kinga nima na samu 'yancin kaina, nayin auren din din din kamar kowacce mace”._ Babu shiri Galadima ya mik'e tsaye, jikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad'annan yaran suka sani? kenan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92