Chapter 76
Chapter 76
GPS navigation maps naku, yanzu zanyi settings komai yanda zaku ringa ganinsu duk layin da zasu shiga insha ALLAH, waye yake driving d'in a cikinku?”. “nine sir”. “ok bama Sauban wayar”. Saleem ya mik'ama Sauban wayar, Galadima na fad'a masa yanda zaiyi, shikuma yana Controlling maps App d'in dake cikin System d'in cikin kwarewa, (dan shima Galadima bai barsa hakaba, dukda bashida ra'ayin karantar wannan fannin saida ya tsaya tsayin daka ya koyan saboda irin wannan ranar). Saida Galadima ya tabbatar komai ya dai-daita, sannan ya kira su Nuren ma, suma suka dai-daita komai nasu, cikin sauk'i duk suka koma ganin inda yaran suke, saboda Galadima ya saka Abu jikin Amaturrahman, dukda bawai hotonsu ko video suke kalloba kai tsaye. Duk da haka Galadima ke fad'a musu su shiga layin haggu, ko dama, kosu canja hanya dadai sauransu. Duk Wanda yake a wannan masarauta yau hankalinsa a matuk'ar tashe yake, saifa kallon kallo da hasashen juna ake a zuciya, kowa yana zargin Wanda ya raina. Hankalin Abie a matuk'ar tashe ya nemi ganin Galadima, koda sarkin k'ofa yazo yana knocking Galadima bai amsaba, kuma yana kallonsa ta CCTV. d'an aike ya koma ya sanar Galadima ya kulle kansa a d'aki yak'i bud'e k'ofa. Papi inno ya kira, yace maza taje sashen Galadima taga mike faruwa. Ko kuyangi inno batajira sun mata rakkiyaba, hasalima babu Wanda yaga fitowarta a sashen mama Fulani, dan kowa a rikice yake da wannam bak'on lamari na satar yara. Galadima daya ga sarkin k'ofa yabar wajen ya mik'e shima daga gaban kayayyakin da yake aikin, shaddar jikinsa ya cire yasaka bak'in wando da t-shirt, ya kawo bak'ar jacket mai k'yalli kamar rigar sanyi ya ajiye gefe, a bakin gadon ya zauna yana d'aura takalminsa yana cigaba damasu Sauban da Nuren bayanin hanya, a dai-dai lokacinne Inno ta iso sashen nasa, da hanzari Sarkin k'ofa ya bud'e mata k'ofar, bata jira wani isoba ko masa sallama ta turo k'ofar falonsa ta shigo, babu kowa a falon, komai ma a kashe yake. Bedroom d'insa ta nufa, nandai saida tayi knocking kam, saidai kafin yay yunk'urin tasowa ya bud'e mata ta turo k'ofar ta shigo, mik'ewa yay yana kallonta da d'aukar jacket d'insa zai saka. Ajiyar zuciya inno ta sauke, saboda ganinsa normal. “Ranki ya dad'e da kanki? lafiya dai ko?”. “Inafa lafiya Muhammad? takawa ya aiko a kiraka ance ka kulle kanka, gashi baka sanar mana halinda yarinyar nan take cikiba”. Galadima yace, ba kulle kaina nayiba, bansan kuma d'an aiken daga papi yakeba” ya juya yana kallon Munaya da cigaba da fad'in, “itama ta farfad'o, amma sun mata allurar barci”. ‘ya k'are maganar da daidaita zaman kwalar rigar jacket d'insa’. Ajiyar zuciya inno ta kuma saukewa, tace, “to Alhmdllh. ina kuma zaka naga kana shiri?”. Wani murmushin takaici yayi zuciyarsa dake gudun daya wuce kima da suya ya dafe, Inno dai ta zuba masa ido, takowa yay inda take ya kama hannunta ya rankwafo (dan yafita tsaho) ya d'ora bisa kansa, cikin murya mai nuna tsananin karsashi da alwashi yace, “kisamin albarka inno, zanje farautane”. Da sauri ta janye hannunta daga kansa tana matsawa baya, “Muhammad mikake nufine? kana ganin tashin hankalin da muke ciki shine zaka k'irk'iro mana wani kuma? kana tunanin wad'annan mutanen zasu barkane? dama kai suke fako, shiyyasa sukayi tarko da bayin ALLAHn dabasu ji ba basu gani ba, su takawa cikin k'ok'arin d'aukar mataki suke, yanzu haka naga IG da kansa gashican ya iso bisa umarnin kiransu”. Galadima dake tattara abinda zai amfani dashi yana zubawa a aljihu, yace, “inno Muhammad Sameer d'inku ba ragon namiji bane da zai zauna jiran Police d'in da suka gaza gano wad'anda suka durk'usar masa da mahaifi tsawon shekaru a yanzu kuma nayi tunanin zasu iya dawomin da gudan jinina har uku, ba sune sukamin tarko ba nine namusu tarko, idan tsoron na mutu kuke, Ku cire inno, ko babusu mutuwa tabbataccen abune rubutacce a kundina, kimin addu'a saina saina dawo”.. Biyosa inno tayi har babban falo tana Kiransa amma yak'i dakatawa, saima d'aga mata hannu da yakeyi, yana gab da zai fita ya juyo yana fad'in “karki d'aga murya da yawa ranki ya dad'e, dan kunnen magauta a bud'e yake”. Yana fitowa Sarkin mota ya taso, dan suna zaune jigum-jigum a rumfar bunun dake sashen na Galadima, duk gaisuwar da suke masa babu ta wacce ya amsa, yau kam ko d'aga hannun basu samuba ma. Basu damuba dan dolene kowa yamasa uziri. Da kansa ya bud'e mota ya shiga mazaunin driver, Sarkin mota daya k'araso yace, “ranka ya dad'e ka gafarceni gani”. Da hannu yamasa nuni da gefen mai zaman banza batareda yace uffan ba. Sarkin mota bashida za6in daya wuce zagayowa ya shiga. A 360 Galadima ya ja motar, kamarma ya manta yana cikin masarautane, saida suka fito gaba d'aya sannan ya bud'e baki da k'yar yace, “ka dinga kallon bayanmu, dan nasan dole za'a samu masu binmu”. Da “to” sarkin mota ya amsa cike da girmamawa. Sarkin mota yace, “tabbas ranka ya dad'e ana binmu”. Cije lips Galadima yayi, ya canja hanya, cikin salon iya taku suka 6acema su Harun dake bin su tundaga masarauta. Hankalin Harun ya tashi kwarai da gaske, dan bai shirya fito na fito da Galadima ba yanzu, saiya cimma burinsa, daga nan komai ta fanjama fanjam, iya zagaye-zagayensu baiga ko motar datai kama data Galadima ba. Shima yana 6ace musu ya dawo kan titi sosai, Maps d'in GPS ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Sarkin mota kuma dayasan gari. Danshi Galadima ba tuk'i yakeba idan yazo 9ja, saidai idan ta kama tilas babu yanda zaiyi kamar irin haka. Sunyi tafiya mai tsawo, yayinda yake Communication dasu Nuren dasu Saleem. A haka ya iso inda suke, duk fitowa sukayi daga motocin, shima Galadima ya fito, idonsa akan agogon hannunsa, yad'an kallesu sannan ya koma kan waya yana fad'in, “maps d'in ya nuna suna a wajennan, kunga kenan tsakanin gidajennan guda hud'une dake kallon juna?”. “kwarai da gaske suna nan”. cewar Muftahu yana furzar da iska. Galadima yace, “Sauban da Saleem zaku cigaba da Control namu”. ‘yay maganar yana ciro agogon hannunsa ya mik'a musu, “ga wannan kuci gaba da using dashi”. Suka amsa da “to” suna kar6a. ya mak'ala abinda zai taimaka masa yaji magana, suma su Nuren duk yabasu suka saka. Har zasu bar wajen ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu, takawa yay gaban k'ofar gidan farko ya haska gaban gate d'in da fitilar wayarsa, babu abinda yake nema, ya matsa na biyu ma haka, komawa yay d'ayan 6angaren, yana haskawa saiga sawun tayar mota data shiga gidan, duk'awa yay ya d'iba k'asar wajen ya shinshina, ya d'ago ido ya kalli gidan yana jizar lips, saiya zubar da k'asar daya d'iba ya mik'e, da hannu yayma Nuren da Muftahu nuni nan ne. Tahowa sukai garesa, Aunty Salamah datun d'azun suna daga cikin mota suna kallonsu suma suka fito ita da su Ameer. A tare suka rissina suna gaida Galadima ya amsa yana bin su da kallon mamaki. Da yake su Saleem sun sanar dasu Muftahu su Aunty Salamah d'in sai Nuren ya kuma yima Galadima bayani. Aunty Salamah tace, “ka gafarcemu ranka ya dad'e, nasan zakayi mamkin mun shigo abinda ba'a gayyacemu ba, insha
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92