Chapter 60
Chapter 60
jeran sannu yakeyi, nikuma ina amsawa cikeda jin kunya. gaishesu nayi, suka tambayeni yaya jikin? na amsa da “Alhmdllh”. Jakar hannuna na mik'ama Abba, ya amsa yana fad'in “minene kuma?”. “Abba ka bud'e to”. ‘nayi maganar a shagwa6e’. Dariya yayi yana k'ok'arin bud'ewa, “yanzu dai fitinarki k'aruwa ma tayi Munaya”. Innarmu dake ta6e baki tace, “ai bamaka san fitinarta ta zarce tadaba sai jiya, juyi kawai ta zauna tana rusama mutane kuka a gidannan, yo ke aibama asan abin fad'in dazaki bariba ranar haihuwar?”.. “babu abin fad'in dazata bari insha ALLAHU”. cewar Abba yana juya agogon fuskarsa d'auke da murmushi. Nima sai ban kula zancen Innarmu ba nace, “Abba yayi k'yau?”. “sosai kuwa Munaya”. “Abba kawo na saka maka to”. “to amma kekuwa ina kika samu kud'in sayen wannan agogon da zoben mai tsada haka?”. Murmushin nayi, nace, “Abba awani shago mukaje sayen kaya tun kwanaki dashi, daga nace agogon yamin k'yau shinefa yace na d'auka to”. “Amma munaya yayi tsada da yawa, karna sakejin irin haka, dan takurawace ai, idan kuma bashida k'arfin siyen abunfa? Karki sake kinji ko?”. “inasha ALLAHU Abba bazan sakeba, amma dan ALLAH karkace bazaka kar6i wannanba, dan shima bazaiji dad'iba”. Murmushin Abba yayi, yashiga sanya albarka a garemu da abinda ke cikina, hardama addu'ar d'orewar lafiya ga Abie shima. cikeda d'oki naita amsawa da amin, da kaina na saka masa agogon da zoben. Daga nan muka d'an ta6a hira. Dan akwai sauran time sosai na tafiyarsu. Mun dad'e muna hira, dan ko break fast yau tare dasu na sakeyi, dama tun asuba ni yanzu nakeyin nawa🤭, sanda kowa zai k'ara sainayi na biyu.😂 Galadima ma daya dawo ya kimtsa nan yazo ya samemu, yanda suke sakin jiki da juna shida Abba abin na bani mamaki, Galadima yakuma yima Abba bayani sosai akan yanda zaicigaba da tattalin lafiyarsa da kulawa da dukkan dokokin da sukai masa, daga nan muka cigaba dad'an ta6a hira, itadai Innarmu duk adabaibaye take, danma taga yau zasu wuce da bazata zaunaba. Wajen 12pm mukabar gidan zuwa asibiti, a asibitine akayi dogon zama, dan godiya ta musammance tashiga tsakanin surukan guda biyu, Abba kuma yay alk'awarin kuma tsayawa wajen dagewa da addu'oi na musaman ga jikin Abie da alk'awarin kawo wasu taimakon na tsarin jiki, dan sunga fa'idar addu'a sosai. Kowa jiyake tamkar karsu tafi, saboda shak'uwace ta musamman tashiga tsakanin wad'annan families guda biyu, zaman mutunta juna ya gudana sosai a tsakani. Kuka na shiga rairawa lokacin danaga tafiyarfa da gaske yinta za'ayi, sai alokacin muka san ashe wai harda Sauban, zai rakasu saudiyya suyi umrah ta kwana 10, daga nan saisu wuce shikuma yadawo. na kama hannun Abba na rik'e gam nak'i saki zai hau jirgi, su Sauban suka tasani da dariya kuwa, oho ban kulasu ba, Galadima ya girgiza kaiwai yana murmushi, yarinyarnan ta6ararta tayi yawa, yafad'a yana takowa inda muke da Abba yana lallashina. A Kallonsa Abba yayi sukayi murmushi, Abba ya zame hannunsa a hankali yajuya zuwa ga jirgi, yunk'urin binsa nayi Galadima yay azamar rik'o min hannu batareda yayi magana ba, juyowa nayi na fad'a k'irjinsa ina kuma sakin sabon kuka. Hannu biyu ya saka ya rungumoni yana guntun murmushi. Innarmu dake hangenmu ta cikin jirgi ta share hawayenta itama tana murmushi, banda aure waya isa ya rabaka da 'ya'yanka. Abba daya zauna kusada ita ya saka hannunta cikin nasa yana murzawa, juyowa tayi ta kallesa, yamata murmushi yana share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa, jikin kafad'arsa ta d'ora kanta kawai. Sauban dake kallonsu yay murmushi, lallai Aunty gimbiya 'yar gatace a gidansu. Saida naji alamun jirgi zai tashi sannan na d'ago kaina, inaji ina gani jirgin yafara shawagi a samaniya harya shilla da iyayena. A motama haka naita sharar hawaye, dayake dagani sai shi da Samha a motar, cankuma Aunty Mimi da Khaleel da jakadiya. Samha tana ta bani hak'uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d'aya baicemin uffanba.. Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallashi. Galadima ya jingina da bango ya hard'e hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma kallonmu yakeyi cike da tausayina. Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan nacema Momma zanci abinci. Galadima yaje kusada Abie ya zauna yana k'aramar dariya, “dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara?”. Hararsa Momma tayi tana masa dak'uwa, hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai. Gurin ya dafe yana fad'in “a'a yazaku tararmin ne kuma?, gaskiyafa na fad'a ko Samha?”. Samha tace, “Uncle nima dai ina bayan aunty gimbiya”. Idanu ya kwalalo alamar tak'aremin. Muka had'a ido na hararaesa. Lips d'insa ya ciza yanamin alamar zan kamakine da ido. Na ta6e bakina nikuma. Dolenesa yatashi yanemomin abinda zanci. ★★★★★★★★★★ Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin k'aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud'ewa yake yana k'ara girma. Kai kace ba halitta d'aya bane a cikinsa. Galadima dole ya d'auki hutu a office, idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo. Gakuma nasarar jikin Abie daketa k'ara k'yau, dan wasu sassan jikinsa suna nuna alamun fara aiki kamar yanda doctors d'insa suka sanar mana. A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a asibiti na kwana, saboda jiki dai yak'i dad'i, ga masifaffen cin abinci abin babu arzik'i. ★★★★★★★ Su Abba sun gudanar da ibadar Umrah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu wahala ba. Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi suka nufi k'asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka masa albarka. Sun isa Nigeria batareda sanin kowa namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d'aukesu a airport. Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin innarsu munaya takoma wata d'anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data samu, dandanan 'yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH ya kiyaye gaba. Innaro babu kunya taketa haba-haba da d'anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje ta zauna a India itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH🤦🏻♀🤣). Su Ayusher da sukazo suka zage suka gyarama inna d'akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had'a uban datti na tashin hankali. Tafiyarsu Abba Nigeria da kwana 5 Sauban ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar sallama ma, k'ila saina haihu. Saidai randa mukayi waya da Munubiya nake fad'a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiyar sosai. Da to na amsa mata kawai, amma ina tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma tunda 'Yar uwata ta ambata dolene hakan za'ayi, kona so koban soba kuwa. ___________________________ *_Two months ogo_*😬🤭 Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba, tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k'yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi, harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance. Jama'ar gidansu Munaya kuwa sunyi haushin da nuna hassadar ga inna harsun gaji sun bari, dan sudai san ba kulasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92