Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 65

Chapter 65

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Munaya da Munubiya ta zaunar a bakin gado. Magana take musu k'asa-k'asa wadda (banajin🙄). Sai naga duk sunyi murmushi suna 6oye fuska. Itama murmushin tayi tana saka musu albarka. Dan murmushin nasu ya tabbatar mata dasun amince. Daga nanfa shiri aka fara, kowacce aka had'a mata kayanta da y'ay'anta. Gayyar gidansu Munubiya su mama Rabi'a suka kwashi nasu, nasu Galadima ma haka. Manne da hannun juna suka fito, mutane sai kallonau sukeyi abin sha'awa da birgewa. Harda masu musu hotuna daga gefe.. Su doctor Farida ma saida suka matso akayi musu hoto danya zama acikin tarihin wannan asibiti. Saida Munubiya ta saka munaya a mota sannan takona tashiga wajen mijinta itama, kowanne Na share hawaye, ba'a San ransu za'a rabasuba. Saikace wad'anda za'a raba gaba d'aya🤣, kai ALLAH yabamu 'yan biyu😂⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀. ★★★★★★★★★★★★ Tarba ta musamman su Munaya suka samu a masarauta, harma abin yaso basu mamaki, hakan dai baisa Mom tayi sake da yaran ba, duk wani motsi dai idonta Na Kansu, an musu rakkiya har sashensu dayasha gyara, yayinda Galadima keta kar6ar barka ga ahalin wannan masarauta, tun daga hadimai zuwa y'an uwansa na jini, maza da mata yaro da babba. Za'ayi walimar cin abinda data sannu da zuwa ga y'an uku a masarautar k'arfe 8pm, wannan yasa ba'a jimaba aka barsu suka shige Dan Munaya tasamu ta huta. Mamaki ya kama Munaya ganin an cika mata gado da tarkacen Teddy's, wannan abun haushi da yawa yake, kuzo Ku kama jera d'iyan aljanu agado kawai. Sudai su mom suka jasu gefe aka kwantar da yaran, itama zama tayi abakin gadon tana dafe kai. Aunty Mimi tace, “lafiya dai k'anwa?”. “wlhy kaina ke ciwo aunty mimi”. Sannu suka shiga yimata, mom tace, “bara laraba tazo ayi wanka kisamu kici abinci saiki sha magani”.. Munaya ta amsa da “to” tana d'an kwanciya a bakin gadon. ********* Laraba amintacciyar baiwar inno tama Munaya cikakken wanka da babu algus acikinsa, itako sai raki takeyi da zille-zille. a haka dai aka gama wannan wanka, lokacin da suka fito sun iske yaranma Mom tamusu da kanta, ana tsaka da shafesu da mai itada Aunty Mimi. Munaya dake d'aure da zani ta rufo babban towel a jikinta ta zauna a bakin gadon tana jingina da fuskar gadon, k'asa-k'asa take kallon yaran da mamakin anya kuwa itace wai ta haifesu? koda yake ba'a jayayya da ikon ALLAH ai, tanajin k'aunar yaranta a har cikin jininta, hakama Na y'ar uwarta, amma data tuna zasu rabu kwana kusa sai hawaye suka cika mata ido. A dai-dai wannan time d'inne Galadima yay sallama, hannunsa d'auke da Leda fara. Aunty mimi da mom dake sakama yaran kayan sanyi suka d'ago duk suka kallesa suna amsa masa sallamar. Idonsa akan Munaya datai masa kallo d'aya ta d'auke ido, murmushi yayi kawai ya zauna a bakin gadon yanama su mom sannu. Cikin tsokana mom tace, “aikin kud'i nikam nakeyi, musamman akan kishiya sa haushi, bar saurin godemin”, tai maganar tana dungure d'an hancin macen dake hannunta. Murmushi kawai Galadima yayi, sai Aunty Mimi CE ke bama mom amsa da “habawa Mom, dukfa kishinki keda Momma kwayi Ku gama, itafa wannan sarauniyar saita za6a ta darje ehe”. Mom tai dariya tana mik'ama Galadima ita, “yo da wannan nanannen hancinne zata za6a ta darje d'in? maji magani dai ai”. Galadima ya lumshe ido yana manna yarinyar da k'irjinsa, k'aunarta Na rsatsashi, ya sumbaci goshinta sannan ya bud'e idonsa, kwantar da ita yayi akan cinyarsa ya bud'e ledar yana fiddo dabino mai k'yau da tsafta, a bakinsa ya saka ya tauna, kafin ya d'ora bakin nasa akan na yarinyar ya zuba mata, da farko yamutse fuska ta shigayi, taji bak'on abu a bakinta, saikuma a hankali tafara motsa d'an bakin, galadima dai yana kallonta da murmushi, dadai taji zak'i saita mamule abinta. Mom tace, “oh su madan kamila kenan, anji zak'i”. Dariya duk sukayi, ya d'auketa yamata kiran sallar hud'uba a kunnenta sanan ya ajiyeta a gefe yana fad'in “ALLAH ya rayaki akan sunnah da tafarkin gaskiya”. Su mom suka amsa masa da amin. Kallon Munaya daketa shafa manta kamarma batasan dasu a d'akinba yayi, yanda taketa wani basarwa shi mamaki tabashi, baiyi zaton hakanba gaskiya, cayake zata nuna tsantsar farincikinta akan yaran?. janye idanunsa yayi ya kar6i d'ayan yaron. Shima haka ya tauna dabino ya bashi, sannan yamasa hud'uba da addu'a ya kwantar dashi. Kar6ar d'ayan ma yayi, Wanda bai cika kuzariba, yad'an masa kallon wasu mintuna yana tatta6a jikin yaron, sai kuma ya kalli mom da Aunty Mimi da suma kallonsa sukeyi. Mom tace “Yaya dai Sameer?”.. K'aramar ajiyar zuciya yayi yana shafa sumar yaron, “mom yaronnan kamar baida kuzarin sauran 'yan uwansa”. “nima na lura da gakan Sameer, amma maybe yanayinsa kenan, kasan kowa da yanayin da ALLAH yake yinsa ai”. “hakane”. ya fad'a cikin sauke ajiyar zuciya, sannan ya d'auki dabino shima yamasa tamkar sauran y'an uwansa, yaron yadad'e bai shanye dabinon ba, daga Bayama saiya fara kuka mara sauti. Rungumesa Galadima yayi yana hura masa k'aramar iska a kunne da d'an jijigashi, sai kuwa yayi shiru, shima hud'uba yamasa, ya kwantar dashi kusada y'an uwansa amma sai yaron yakuma Sanya kuka, gashi muryarsa bata fita da k'yau. d'aukarsa ya kumayi yana murmushi da fad'in “oh little Sameer what happen?”. Mom tace, “shagwa6a ce mana”. Dariya Aunty Mimi tayi, yayinda Galadima da Munaya suka murmusa, Dan duk abinda ke faruwa tana allonsu ta gefen ido, amma ta basar kamar bata d'akin. Fita Aunty Mimi da Mom sukayi suka barmusu d'akin. tuni 6angaren ya rikice da k'amshin girki, dan cikin kuyangin da su mom sukazo dasune suke tsara girki wa maijego dasu kansu. Tashi Galadima yayi d'auke da yaron a jikinsa ya nufi inda Munaya take zaune, tun d'azun tagama shafa man amma tak'i tashi ta saka kaya. Zama yay kusada ita sosai jikinsa har yana gogar nata. Da sauri ta yunk'ura zata mik'e, ya saka hannu d'aya ya ruk'ota yana maidata. Kallonsa tayi fuska a cunkushe kamar zata fasa kuka, idanunsa ya saka acikin nata yanda bazata iya janyewa ba, aiko duk k'ok'arinta nason ta janye d'in ta kasa, sai cika sukayi da kwalla, dan yana ganin k'yallin ruwan hawayen. Yad'an murmusa yana lumshe ido da bud'ewa a kanta. muryarsa cikeda k'asaita da sanyi yace, “kekuma salon taki murnar kenan?”. Had'iye kukan dake Neman kufce mata Wanda itama batasan dalilinsa ba tayi, tayi murmushin takaici tana janye idanunta daga cikin nasa, muryarta a sark'e cikin sanyin rauni tace, “Ina tayaka murnar sosai yalla6ai”. Lips nashi yad'an cije, ya lalla6a ya ajiye yaron da barci ya d'auka gefen y'an uwansa, Munaya duk tana kallonsa. Kuma matsawa yay jikinta sosai ya jawota jikinsa, batayi yunk'urin hanashiba, kamar yanda bata hana hawayenta zubaba. Ya saka tattausan hannunsa yana share mata hawayen, “Friend dukda bansan miya sakaki kukaba ina mai baki hak'uri, wannan ranar bana buk'atar damuwar kowa sai farinciki, musamman ma daga gareki, ina rok'onki alfarmar fansar wannan damuwar taki da farinciki akan kowanne farashi, komai tsadarsa kuwa”. ya k'are maganar da sumbatar sumar kanta. Murmushi tayi, ta d'ago daga jikinsa idonta akan yaran dake jere reras abin sha'awa. Shima d'in su yake kallo. “bana cikin kowacce damuwa da kake tunani yalla6ai, kawai dai...” sai tayi shiru. Kallonsa ya maido gareta, yace, “kawai dai mi

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});