Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yaja ga zazza6in fama ya rufeni, sallama mukayi nai addu'a Na kwanta. Masu iya magana since sabo tirken wawa, saina kasa barcin, naji kawai ina kewar Galadima. Shima kansa yanacan sai juye-juye yakeyi, yakasa barci, bayan sun gama hirarsu dasu Aryaan yay musu shirin barci da kansa suka kwanta, aiki yad'an ta6a yana Neman dabaru akan binciko Muftahu, baiwani dad'eba ya kwanta shima, amma saiya kasa barci, juye-juye yaytayi agadon, ganindai da gaske ya kasa barcinne saiya mik'e yana jan guntun tsaki, kwanciya ya gyarama su Aryaan ya lullu6esu da bargo sannan ya fito da nufin wai zai duba munaya 🤣😜. Jin shigowarsa yasani k'ara lafewa tamkar nayi barci, ya kunna fitilar d'akin yana kallona, yaja wani dogon lokaci sannan ya kashe ya tako zuwa gadon, “nasan idonki biyu ai, dama kin tashi kinbar wani kumshe-kumshe”. Shiru nayi nakumak'i motsawa. Kwanciya yayi a gefena, yaja bargon shima ya lullu6a, tareda juyamin baya, yace “miya hanaki barcine?”. “farkawa nayi”. Na fad'a batareda ba kalleshi ba. Murmushi yayi yana fad'inn “ Hummm”. Daga nan duk mukayi shiru nawani lokaci, kamar an matse bakina nace “yalla6ai na tambayeka please? ”. Yace, “Uhmm”. Juyowa nayi ina fuskantar bayansa, a nutse nace, “wai dan ALLAH ina sauran matan Abie yanzu?”. Da sauri naga ya juyo gareni, ni harma tsoro ya kamani nai baya da sauri, nazata makeni zaiyi, amma sainaji ba hakaba, yace “Munaya mi kika sani a kaina ne?”. “yalla6ai kamarya mina sani a kanka? daga tambaya?”. Yace, “Humm yana matsowa gareni, zan matsa ya rik'o hannuna................✍🏼 Kuyi manage da wannan please🤦🏻‍♀ *_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🙏🏻_* [7/3, 9:59 AM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻1⃣4⃣ ................Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”. Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, muryarshi a sanyaye yace, “Miyasa kikeson 6oyemin abinda kika Sani? shin bak'ya tausayinane? kullum cikin aiki kwakwalwa ta take, aikin Neman kud'in da zan taimaki kaina da ahalina, aiki akan mak'iyana, ya kike tunani a kaina? yanzu haka ji nake tamkar kwalwar kaina zata tarwatse saboda damuwa da abubuwan da suka sakata matuk'ar nauyi, ta6a kiji yanda zuciyata takoma bugawa a slowly”. ya kamo hannuna ya d'ora a k'irjinsa, saitin zuciyarsa. da gaskiyarsa kad'an-kad'an zuciyarsa ke aiki, ba kamar kowanne bugun zuciya dake tafiya normal ba. Sai naji tausayinsa ya kamani, cikin sanyin murya nima nace, “yalla6ai kayi hak'uri da abinda zan fad'a maka, inhar ka kawoni gidanka ne domin muyi aiki tare a matsayin Friend bai kamata ace ka gaza yarda daniba akan sirrinka. kasan minene yake saka kwalwarka da zuciyarka wannan nauyin kuwa?”. Kansa ya girgiza mini. Na gyara kwanciyata ina kallon p.o.p, “Matsalarka d'ayace baka yarda da kowa ba sai kanka, mu cire Momma da papi, dansu aiyukansu sunkai amusu uzuri, Momma hankalinta akan jiyya yake, dan haka kana k'ara mata damuwa, papi kuma babbane shawara da dabarun manya kawai kake buk'ata daga garesa. Sai kuma Muftahu da Harun nakula suma kakan d'an saki jiki dasu akan wasu abubuwan, to amma fa.........”. Saitayi shiru bata k'arasaba. Ya matso jikinta sosai, tare da d'ora hannunsa saman cikinta, murya k'asa-k'asa yace, “Harun da Muftahu amma fa mi? Please ki k'arasa mana”. Kad'an Na juyo nad'an kallesa, Na d'ora hannuna nima akan nasa daya d'ora akan cikina. Janye fuskata nayi Na koma kallon p.o.p d'in. “kayi hak'uri da abinda nake fad'a, badan ina zarginsu bane zan fad'a d'in, dama zancene Harun da Muftahu kuma kamar bai kamata 100% susan komaiba, dan za'a iya sayensu ko tursasasu suci dunduniyarka. domin koba komai har yanzu bakada tabbas d'in cewar babu hannun wasu a cikin masarautar nan. amma kayi hak'uri idan na shiga hurumin daba nawaba”. Shiru yay baice komaiba tsawon lokaci, har nayi zaton nayi laifi ko yayi barci, a sanyaye nakuma fad'in “please & please kamin afuwa yalla6ai”. “is okay”. ‘kawai ya fad'a yana kuma sakani a jikinsa, tareda d'ora ha6arsa saman kaina. Babu Wanda yasake magana a tsakaninmu, kowa yay shiru yana k'ullawa da kwancewa, har dai barci yafara fisgata. “Kina ganin su Aiyaan bazasuyi kuka ba idan suka farka sukaga su kad'aine?”. Naji maganarsa cikin kunnena. “a'a” na fad'a ina girgiza masa kai, “ko'a gida sukad'ai suke kwana dama”. “okay”. Saikuma muka kuma yin shiru, har barci yakuma fara d'aukata yakuma fad'in “kozaki sha Magani ne?”. ‘yay maganar yana ta6a gefen wuyana’. Kaina Na girgiza masa batareda nace uffanba. shima bai sake cewa komaiba.. Yanda numfashina ke sauka a hankali sai ya fahimci nayi barci, shiko gaba d'aya yakasa nasa barcin, tunanin wani Abu daya ta6a faruwa a baya ya fad'o masa, dukda shi ba yayi imani da hakan baneba. 👇🏻 *_Wata ranar juma'a a India, sai suka tashi da matsananciyar damuwar motsawar ciwon Abie, a time d'in ma sun zata rai zaiyi halinsa, hankalin Galadima ya tashi har ciwonsa shima yakai ga motsawa, amma yak'i yarda doctors su dubashi, yace abarsa kawai gara ya mutu ya huta, hankalinsu momma ya tashi, amma Galadima yak'i sauraren kowa, daga k'arshema saiya sulale daga asibitin ya fice abinsa, haka yayta tafiya rik'e da k'irjinsa saboda azabar ciwon da zuciyarsa ke masa, mutane sai kallonsa sukeyi, shiko baimasan sunayiba, yayi tafiya mai nisan gaske batareda yasaniba. k'arfinsa da kuzarinsa sukai gazawar da bazai iya cigaba da tafiyanba, shine yazube a wajen ya fad'i._* *_bai tashi farkawa ba sai awani d'aki mai kama dana bunu, ya yunk'ura zai mik'e amma saiya kasa, wani tsoho ba indiye, a cikin indiyawan ma irin masu k'yawunnan sosai, ya dafa kafad'arsa, cikin harshensu yace ma Galadima “koma ka kwanta d'an saurayi, bakada lafiyane”. Galadima yace “kayi hak'uri baba gida zanje nasamu sauk'i, zamana annan bak'aramin tashin hankali bane ga ahalina”. tsohon yay murmushinsu Na manya, yace “zakaje gida d'ana, ni da kainama zan kaika, amma lallai kai acikin al'amuranka akwai abubuwan ban mamaki da al'ajabi, gakuma tsantsar rud'ani, saidai komai yanada lokacinsa, kuma lokaci zai tabbatar maka hakan, albishir d'aya zanmaka, nanda wasu shekaru dabasu Gaza 7 ba mai taimakonka zatazo, kwarai zatazo gareka, ba lallaine ka fahimci abinda nake fad'aba ko yarda dani, Dan Na lura kaid'in musulmine, kuma bad'an wannan k'asarba, amma wannan mai taimakon naka itace zata zama fitilar haska maka hanya kakai ga cinmma burinka, domin taurarinta da naka sunada matuk'ar k'arfi, harma suna gogayya da juna, zaku zama sh........”. Saikuma yayi shiru yana murmushi, ya shafa kan Galadima yana fad'in “tarin Albarka sucigaba da baibaye rayuwarka data zuri'arka”._* *_daga wannan maganar sai barci mai nauyi ya kwashe Galadima, koda ya farka saiya gansa a asibiti tareda su Momma, yata tambayarsu INA tsohon yake sukace su basu San wani tsohoba, wasu samarine su biyu suka kawoshi asibitin, wai sungansa yafad'i a gefen hanya, zancen tsohon yata damun Galadima a time d'in har yayta bincike kozai gansa amma ko alamun mai kamarsa bai ta6a ganiba, daga hakama saiya cire abin a ransa yacigaba da harkokinsa._* Ajiyar zuciya ya sauke, tareda kuma rungume Munaya, a kan la66ansa ya furta “ALLAH kaine mafi sani”. daga haka yay shiru tareda lumshe idanunsa, barcine yayta fusgarsa harya samu nasarar sacesa. Can gabannin asuba yay wani mafarkin daya sakashi farkawa a firgice, har itama Munaya ta farka tana tambayarsa lafiya?. Kansa ya dafe, da hannu yaymin nuni na bashi

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});