Chapter 57
Chapter 57
Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa. Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i. Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, “kallonfa?”. Janye idona nayi ina ta6e baki. Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time. Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, “tabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon”. ‘Ya k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshinta’. Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne. Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima. Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters😉🤩......................✍🏻 Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d'inane🥰🥰🥰🤝🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭_* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭_* [7/8, 1:47 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ___________________________ _jinjinar gaisuwa a gareku da fatan alkairi, Bilyn Abdull ta gaisheku, gaisuwa irin ta musamman d'innan my lovely sister's🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻_ *_Aysha Manshart (Ummu zunnur😍), Hafsa abdulaziz, mmn fukaihat, Hannah A Ali, marnona, Mmn Al'ameen, Sumee waziri, Ummu walid, Yar tulluwa, Khadija Aliyu Sa'id, Umm Abdul, Umm Yusuf, Mrs Ahmad, zubby abdullahi, Hajara Ismail shatu, Ummu barakat, maryam haruna, Ummu sulaym, Ummu Ahmad, Haizarana halliru._* I love you mazga-mazga😂🤸🏻♀ ____________________________ ~Book 2~ 👉🏻2⃣0⃣➖2⃣1⃣ ................Tafiyar su Abba dai ta kankama, dan Abba ya matsa ainun, dole Galadima ya musu dukkan shirin daya kamata, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu jirginsu zai d'aga. Da yake yau Saturday ce babu aiki, amma hakan bai hana zama gidan shiru ba, su Sauban da innarmu sun fitane, nikad'aice a gidan sai jakadiya, nima barci nake suka gudu suka barni a gidan. Yunwar dana farka da ita ta tilastamin sakkowa k'asa neman abinci, dan a 'yan kwanakinnan nazama wata acici, danaci abinci danaji sabuwar yunwa, narasa wannan dalili. Bannemi kukun gidanba ma ko cikin bayi, nahau dafa abinda zaimin saurin dahuwa, kafin ya dahunma saida na d'umama madara nad'ansha sannan 'yar nutsuwa tazomin. ina sauke abincin kuwa Na juyoshi a plate na koma sama. tun a hanya naji k'amshin turarensa, ban kawo yashigo gidan bane nidai na ida hawa. ban tsaya faloba na shige bedroom. Galadima dake zaune a sofa yana kwance igiyar takalminsa ya d'ago ido yana kallona da amsamin sallamar danayi. Sandunan wasan Golf d'insa daya shigo dasu ya zube a carpet d'in gaban gadon na janye gefe na zauna, dan nafijin dad'in xaman k'asan yanzu. Shidai bai fasa kallona ba baikuma bar cire takalman ba, dan abincin dayaga ta zubo yakema kallon mamaki, kafinfa yafita harda kukanta ta farka wai yunwa takeji, haka dole yafita yasaka kuku dafa mata abinci, baibar gidanba saida taci takoma barci, da fitarsa kuwa baifi 3hours ba, amma jita yanzu dawani abincin. Ya janye takalaman daya gama cirewa a gefe ya zubamin ido kawai, dukda abincin nada zafi haka nakecinsa da sauri-sauri. Janye plate d'in yayi daga gabana, fuskarsa babu walwala yace, “waike mike damunki hakane?”. Idona harya fara tara kwalla cikin marairaicewa nace, “dan ALLAH kabani, wlhy yunwa nakeji bata wasaba”. Rasa ma mizaicemin yayi, ya zubamin ido kawai yana kallona. a mamakinsa saiyaga ma ina hawaye, abincin ya tura min yana fad'in “wannan cin naki yayi yawa, gama muje wajen Akash ya dubaki”. Uffan bance masaba, shima bai sake tankawa ba yanufi bathroom, yaja wasu mintuna saigashi ya fito d'aure da towel, kallo d'aya namasa na janye idona, wannan abun nasa yafara damuna, yanzu baijin kunyar yafitomin a duk yanda yaso, ko yana mantawa bashi kad'ai bane a d'akin oho. Shima dai kallonta kawai yakeyi, dan nacinye abincin plate d'in tas, a ransa yace shiyyasa taketa zama k'atuwa, irin wannan ci haka. Oho bansan yanayiba, nidai mik'ewa nayi nashige bathroom abuna, nasamu nai wanka da ruwa mai sanyi dan naji dad'i. lokacin dana fito yagama shiryawa cikin ainahin kayan malam bahaushe, blue d'in shaddace akaima d'inkin wando da 'yar shara, saidai tasha aikin sarauta d'an asali da d'aukar hankali, ya kawo bak'ar hularsa ya d'ora, itama dai irin ta mutanen dace *dara* (irin wadda su ibro suke sawa), saidai wannan batakai waccan tsawoba, dai-dai take kamar sauran huluna. harga ALLAH kwalliyar tasa tamin k'yau, dan yafito a cikakken bahaushensa, turare yake fesawa amma nakasa d'auke idona daga kansa. Duk kallon k'urillar datake masa yana kallonta ta gefen ido, wani miskilin murmushi yayi Na gefen baki, ya juyo muka had'a ido, saurin janyewa nayi cike da basarwa. Shikuma ya ta6e baki yana takowa inda nake. tuni zuciyata harta fara tsitstsinkewa, dan ayanzu babu abinda nake gudu kuma irin yace zai ra6u jikina koya nunan buk'atar wani abu, shima inaga fahimtar hakanne yasa a kwanakinnan bai cika takurani kamar abaya danake kawo kaina ba. Ganin yanda ta tsorata sai abin yabashi mamaki, waskewa yay yafasa zuwa gareta, ganin ya canja hanya Na sauke ajiyar zuciya wadda har fitar sautinta saida yaji. Kansa kawai ya girgiza ya zauna a bakin gado yana fad'in “kishirya mana”. Bance komaiba nawuce Na d'auki Arabian gown da zan saka, dan yanzu sune kawai kayan dakemin dad'in sakawa, bathroom nakoma Na saka, Na fito Na iskeshi yana waya da Akash dake fad'a masa inda zamu iskeshi. wucewa nayi nad'an gyara fuskata, inason shafa mai a k'afa amma ina tunanin yanda zan sunkuya. Lura da yay da hakan yasashi mik'ewa, wajen takalmanmu yanufa ya d'aukamin masu taushi cikin wad'anda ya siyamin saboda naji sauk'in tafiya. Kafad'una ya kama ya zaunar dani ga stool d'in mirror, sannan ya d'auki man ya duk'a k'asa a gabana yakamo k'afata yana shafamin, nidai kallonsa kawai nakeyi, harya gama yasakamin takalman ya d'auran igiyar yana fad'in “yakamata ma mufara fita kina motsa jiki, dan k'afarnan kamar tana d'anyi fushi a kwanakin nan”. Nace, “ai bata ciwo”. Baice komaiba yamik'e yana kama hannuna ya mik'ar dani. A falo muka iske jakadiya tana kallo, tamin sannu sannan ta gaida Galadima. yafad'a mata zamu fita, tabimu da addu'ar dawowa lafiya. Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda muka saba inhar ta had'amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida mai k'yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafito yana zabga murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92