Chapter 13
Chapter 13
“na gode d'an uwana, insha ALLAH nabari har abada, kuma kwannan zakaji maganar aurena ta tashi, wlhy tun wancan lokacin da abunnan yafaru ban sake mu'amulla da kowacce maceba, idan najima zan takura saina fara azumi”. “tom ALLAH yacigaba da gadinmu muda zuciyoyinmu, amma Auren shine tafi cancanta dakai, dan wani lokacin da mutum yakai azumin ma zakaga komai yadawo, kaga Auren shine cikakkiyar mafita kawai”. “gaskiyane wlhy, ALLAH dai ya k'ara shiryamu”. ‘Nuren yafad'a yana horn a k'ofar gate d'in katafaren gidan gonarsa dayake kiwo’. An bud'e musu gate d'in suka shiga, ma'aikatan sai murnar ganinsa sukeyi, tsayawa yay da motar batare da sun fitoba, sukaita zuwa gaishesu, bawani Sanin Galadima sukayi sosaiba, tunda bawani zuwa wajen ya keyiba, Nuren zai fad'a musu wanene, amma Galadima yamasa nuni da karya fad'a, hakkane yasakashi 6ame bakinsa. ****************************** Ran mama Fulani a 6ace yake kallon manyan jikokin nata maza guda uku tayi, cikin isarta da k'asaitarta tafara kiran sunayensu, “Talba! Wanbai! Matawalle!, kunsan dalilina Na taraku anan kuwa?”. A tare suka girgiza mata kai kawai. Takuma gyara zamanta cikin tsantsar mulki da izza, tace, “nakula mahaifinku har zuwa yanzu baison ciwonku ba, shi dole yanaso ace masa adalin Sarki, shiyyasa kullum yake fifita d'an wani bisa Ku da ALLAH ya bashi, Matawalle shekarunka dana Galadima kusan d'ayane, amma mahaifinku nagani Galadima yay aure bai ta6a nuna damuwarsa akan kai kayiba balle sauran 'yan uwanka, to yanzu matar Galadima cikine da ita, kuma tabbas ta haifi namiji kuda sarautar gagara badau saidai kallo”. A razane Talba da wambai suka zaro idanu waje a zabure, matawalle kuwa murmushi kawai yayi yana girgiza kai da mamakin wannan kakar tasu mai shegen son kanta. Wambai yace, “haba Granny miyasa kike fad'ar wannan maganar, yakamata bakinki ya fad'i alkairi mana, shi dan uban cikin basai mun bari an haifesa ba, koshi uban cikin dayake tak'ama yana jiran gado bai isa yayi mulkiba balle cikin da babu tabbas d'in haifosa, ni wlhy kinma 6atamin rai”. Talba yaja tsuka shima yana harare-harare, “Granny ya akayi kikasan tanama da cikin to? wannan sarkin girman kai d'inne zai iyama mace ciki?”. Harara mama Fulani ta zubama Talba, “to uban matanbaya, azatonka zai zuba mata idone yana kallonta kamar hoto ko television a gida? ince kwana nan 4 kenan dabaro inda suke”. Wambai yace “amma shine bakiyi maganarba sai yau Granny?”. “to ubana koyamin yanda zanyi”. “ALLAH yabaki hak'uri”. ‘cewar wambai yana k'unk'uni k'asa-k'asa’. Matawalle dabaice uffanba tunda aka fara maganar yay guntun murmushi, muryarsa a tausashe yace, “Ranki ya dad'e ni banga amfanin wannan maganarba, ALLAH shine ya azurta Galadima da samun ciki a jikin matarsa, wannan kuma abun farin cikinmu ne amatsayinmu Na 'yan uwansa, shi dai mulki Na ALLAH ne, shike badawa ga Wanda yaso akuma lokacin da yaso, bamuda tabbacin tsawancin ran ganin gobenmu ma balle maganar gadar sarautar cikinma daba'a San miza a haifaba, please musama zukatanmu sallama kodan mutuwa, nifa banga wani dalili dazamu ke saka kammu a wahala akan mulkin da ubangijine kawai madawwami a mulkinsa, nikam kunga tafiyata, ki gafarceni inada uzuri”. Tunda matawalle yafara maganar Mama Fulani da Talba da wambai ido suka zuba masa, harya fice ba'a samu mai iya tanka masaba. haka yake shi, babu ruwansa da bak'in mugun abun masarautar, da zuciya d'aya yakeson d'an uwansa, shi bama wani zaman k'asar ma yakeba sosai. Wani wawan tsaki Talba yaja, yabi bayan Matawalle da harara yana fad'in “lusari kawai, inkai bakason sarautar mu ai munaso, shifa wannan ko sarautar ya gada wlhy lusarin Sarki mai lasisi za'ayi anan, duk wannan wahalar akansa akeyinta danya zama magajin Abba amma shashashan nan baya gani”. “mtsoww!! bar banza d'an uwa, idan zai bamu matsala kai basai ka zama magajin Abban ba, nifa harma tunani nake, anya matawalle jinin gidannan ne?..........” “kai ya isa haka, banason rashin tauna magana, Ku k'yalesa zaima dawo hanyane, miye mafita yanzun?”. “mafita d'ayace Granny a 6arar da shegen cikin kawai, kuma ma ai Galadiman yazo jiya”. Da sauri mama Fulani ta tashi zaune daga kishin gid'ar datayi, “wambai kana nufin Sameer na a masarautar nan?”. “kwarai ma kuwa, da safe nagansa zaishiga mota a k'ofar sashensa, yanata faman d'aurema mutane wannan shegiyar fuskar tashi da yakejin tafi ta kowa k'yawun gani”. Wani k'asaitaccen murmushi mama Fulani tayi tana fad'in “lallai yaronnan ya isa, kuje kawai, bayan nagama tsara komai zan nemeku”. atare suka mik'e suna fad'in “ahuta lafiya ranki ya dad'e sarauniyar gagara badau”. Murmushi tama jikokin nata tana gyad'a musu kai. ____((____(((★)))____))____ Galadima da Nuren sun shiga ainahin matsakaicin gidan Nuren dake a gidan gonarsa Na kiwo, sosai ya tsara cikin gidan, dan ananne yake holewa da 'yammatansa a watannin baya, sai dai yanzu kam alhmdllh yabari gaskiya, dan sai lokaci-lokaci yake d'an ta6awa, fatansa ma yabari gaba d'aya, dama ta silar abokai ya koya🤦🏻♀. Galadima ya zauna saman kujerar guda d'aya yana sauke numfashi, har yanzu zuciyarsa tak'i nutsuwa waje d'aya, halin da yaga Abban Munaya ya dank'are masa zuciya. Cikin ma'aikatan wajen yay sallama daga waje, Nuren yabashi izinin shigowa, kayan marmarine yahad'o ya kawo musu bayan ya tsaftacesu, a saman center table d'in ya ajiye, sannan yakona yaciro musu ruwa a freight d'in dake falon da cups Na glass. Bayan fitarsa Galadima ya kalli Nuren d'in, “Brother wai miyasa ka kawoni nan ne?”. “cinikin kanka nayi”. ‘cewar Nuren yana harar Galadima’. “Wani k'asaitaccen murmushi Galadima ya saki, yakai hannu yana shafa sajensa zuwa gemu, cikin d'age kafad'a da la6e baki yace “baka kai girman saida kainaba yaro”. “uyim! Haka kace ko?”. ‘cewar Nuren yana kallon galadima’. “kaima kasan hakanne ai”. Mik'ewa Nuren yayi yashiga wani d'aki yana dariya, mintuna 4kacal saigashi tare da wani dattijo. Galadima da yake kishingid'e yad'ago ido yana kallon Nuren da dattijon, amma baice komaiba yacigaba da latsa wayarsa hankali kwance. Dattijo direban Alhaji balala ya zube k'asa yana kwasar gaisuwa ga Galadima. Galadima shi mutumne mai mutunta Wanda ya girmesa, dan haka Yakuma d'ago kai yana kallon dattijon, fuskarsa ba'a d'aureba ba'a sakeba, cikin muryarnan tasa ta isar masu mulki da k'asaita yace “no baba zauna da k'yau, kabar durk'usamin banaso”. Dattijo yace, “ai girmanka ne ranka ya dad'e”. Murmushi kawai Galadima yayi, ya ajiye wayar hannunsa yatashi zaune sosai, ruwa ya d'auka ya zuba a cup sannan ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallon dattijo. “bawan ALLAH minene sunanka?”. Jikin dattijo Na rawa yace “Barau ranka ya dad'e”. “humyim baba barau, koka sanni?”. “sosaima ranka ya dad'e, wanene zaice bai sankaba a wannan nahiyar”. Galadima ya wani lumshe idanu yana cije lips nashi, ya bud'e idanun akan Mal barau da duk yake a tsure, sosai kwarjinin Galadima da cikar haibarsa suka rikita dukkan tunaninsa da kwarin guywarsa. Galadima ya katse masa tunani da fad'in, “Baba barau nasan akwai tambayoyi taf bakinka a gareni, saidai bazan baka amsar ko guda d'ayaba, zan baka dama da sharad'i, Na farko shine kanada damar fad'amin gaskiyar abinda kasani idan Na tambayeka, nikuma nabarka ka tafi salin alin, Na biyu inada sharad'in ka d'aukarmin alk'awarin komai zai fito abakinka ya zamto gaskiyar abinda Na tambayeka, idan kamin k'arya koka yaudareni kuma.... Humm”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi batare da ya k'arasaba’. Hakan yasaka jinin Malam barau rawa, yana karkarwa yace, “insha
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92