Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 91

Chapter 91

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yabasa sukayi musabaha, sannan suka cigaba da tafiya cikin gidan a jere, fuskarnan babu walwala yace, “ya kuke ciki dasu?”.. Muftahu yad'an nisa yana bud'e masa k'ofar shiga falon dansun k'araso, “Ranka ya dad'e bamu tambayesu komaiba, Dan wannan ba Hurumin mu baneba ai”. Galadima baice komaiba, ya zauna kujera mai zaman mutum d'aga yana d'ora k'afa d'aya kan d'aya. Muftahu bai zauna ba saida ya d'akko glass cup da kwalin Hollandia ya ajiye gaban Galadima. Galadima dake danna waya yad'an d'ago ido ya kallesa ta cikin glasses, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya maida kansa ga wayar. Girgiza kai kawai Muftahu yayi, Dan yasan magana yakesonyi amma yaza6i yayi shiru daya bud'e bakin. yana tausayama Munaya wlhy, “Ranka ya dad'e su zone?”. dan yasan bai wuce abinda yake son cewa kenanba. Ilai kuwa sai Galadima ya jinjina kai yana nuna yatsansa d'aya alamar mutum 1 yakeso. Nanma dai Muftahu kan ya girgiza kawai sannan ya mik'e. Mintuna uku kacal saigashi da mutum d'aya a cikinsu. har yanzu kuma idon Galadima nakan phone nashi. Saurayi da bazai wuce shekaru 30 zuwa sama a duniya ya durk'usa gaban Galadima kamar yanda Muftahu ya umarcesa, kwarjinin Galadima da cikar haibarsa da tsare gida duksun rikita gayen, bakinsa na rawa yace, “barka da safiya ranka ya dad'e”. K'ala baice dashiba, kusan mintuna biyu ya ajiye wayar yamasa kallon tsaf sannan ya janye idonsa, kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanu, hannayensa duk suna bisa hannun kujerar, cikin maganar nan tasa mai kama da anmasa dole yace, “wanene kai? miya kaika gangancin shiga hurumina?”. Ba k'aramin tsuma da birkita muryar Galadima ta saka guy d'inba, haka kawai sautin muryar Galadima dabata da r a cikin kalami ya rikita guy d'in, murya na rawa yace, “Ranka ya dad'e sunana Shazali, kuma wlhy bansan komaiba, nidai kawai anzo an bamu aikine”. Halbi Muftahu yakai masa yana fad'in “k'arya kakeyi”. “Wlhy da gaske nakeyi”. Shazali yafad'a cikin mak'yark'yata. d'agowa Galadima yayi zaune sosai, yace, “kozan iya sanin wanene yabaku aikin?”. “Bansan sunanta ba Ranka ya dad'e, amma zan iya ganeta”. Kallon Muftahu Galadima yayi, Muftahu daya san abinda yake nufi ya jawo laptop yana ajiyewa gaban Galadima. Zama ya gyara, cikin kwarewa yafara sarrafa System d'in yana cizar lips kad'an-kad'an, wannan salo na yarima yana burge Shazali, aransa yana jinjina mulki mai dad'i kenan, haka kawai k'aunar Galadima ta shigesa, kuma yayi alk'awarin taimakonsa cikin sauk'i insha ALLAH....... Tunaninsa ya katse lokacin da Galadima ya turo masa laptop d'in. Kallonsa yad'anyi Dan baisan mizaiyi da itaba. d'auke kai Galadima yayi alamar bazai yi magana ba. Muftahu yace, “ka duba idan akwaita anan”. Laptop d'in Shazali ya ida jawowa gabansa, hotunane suka bayyana da yawa. Muftahu yamatso yana masa zooming nasu one by one. Nuren yafito daga wani d'aki yana mik'a, da mamaki yake kallon Galadima dashima shi yake kallo, “brother kaine?”. Kai Galadima ya girgiza masa alamar a'a. Nuren ya murmusa yana tahowa cikin falon, hannu yabama Galadima sukayi musabaha, yana tambayarsa yaya jiki?. Akan la66a ya amsa da “Alhmdllh”. Nuren yace, “ina yarana?”. Da hannu yamasa nuni da lfy. Kular da Nuren yayi yau k'asaitar a kusa take saiya barsa ya mik'e, Coffee ya had'o yadawo ya zauna yana kallon abinda su Muftahu sukeji. Shikam Galadima yayi shiru yana tunano yanayinsu da Munaya na d'azun, yana da buk'ata mai tsanani, saidai yakan danne saboda jarumta, musamman idan ya tuna matsayin auren nasu, ko a baya saboda yanayin data shigane ya sakashi yin yadda yaso da ita, Dan hak'k'insa ne ya taimaketa a lokacin kodan buk'atar tazame mata lalurar cikinsa, yanzu kam dolene yanemo mafita ko matar aur.......... Tunaninsa ya katse lokacin da Shazali ke fad'in “itace wannan yalla6ai”. Daga Muftahu har Nuren kallon picture d'in suka tsaya yi, sannan duk suka kalli Galadima da shima idonsa ke Kansu. Nuren ya d'auki laptop d'in ya mik'a masa, shiru Galadima yay yana kallon hoton, Matar Abie ce ta biyu, wadda yata6a gani a wayar Harun, yay wani miskilin murmushi yana yana kallon Shazali, saikuma ya janye idonsa batare da yace uffanba. Shazali ya gyara zama yana fad'in “bayan ita kuma sai aka had'amu da wannan matan daga masarauta, sukuma sunce Uwar gidan sarkice ta sakasu”. Nuren yace, “uwargidan Sarki kuma? to tayaya tasan kud'in ga abinda zakuyi?”. “wlhy ban saniba nima ranka ya dad'e, abinda na Sani kawai a ranar wlimar kafin mu shigo hall d'in aka taremu a hanya, shine wani dogari ya shigo motarmu, da farko mun taso masa harda fiddo wuk'ak'e, saishi kuma ya nuna mana bindiga, hakanne ya sakamu nutsuwa, yace, yasan abinda zamujeyi ai, dan haka idan munason mu tsira da ranmu mu sauraresa da k'yau, shima aiki zai bamu. Zai had'amu da bayi biyu mata dazasu taimakemu mu sace yaran, bayan mun gama akwai kaso mai tsoka, sannan zai fad'a mana wani sirri, mahaifin yaran yayi shirin canjasu da y'ay'an babyn roba dan haka karmu sake mu d'auki yaran da za'a bama wasu yara, mu d'auki na cikin gado daza'a sakasu a wajen taron, sune zasu zamo na gaskiya, mak'udan kud'in daya bamune suka samu amincewa da gaggawa, Yakuma sanar mana aikin uwargidan sarkine, idan har mukayi kuskuren wani yasani dagamu har ahalinmu sai sun shafe labarinmu a doron k'asa”. Daga Muftahu har Nuren kallon Galadima suke da mamakin Brain nashi, hakan suka shirya, amma daga baya sai sukaga ya canja yabada yaran da gaske, sunyi mamaki sosai, amma bai basu fuskar tambayarsa ba a time d'in. Yay musu alamar miye suke wani kallonsa. Salute d'insa sukayi su duka, ya kauda kansa kawai yana ta6e baki. Sun kuma tabbatar da akwai sirrika da yawa da Galadima ya Sani, akwai yana basarwane saboda jiran lokaci. Da hannu yamasu Nunin Shazali yatashi yaje. Bayan tafiyar Shazali ya kallesu yana sauke ajiyar zuciya da gyara zamansa, ya d'auki kwalin hollandia yazuba a cup, Muftahu da Nuren dai na kallonsa, saida yafara sha da kallon agogon hannunsa sannan yace, “Zanje India gobe idan ALLAH ya kaimu, akwai ayyukan dazan tattara na kwanaki uku, sannan na d'auki Hutu a wajen aiki, dukda muna shirye-shiryen fidda kaya na shekara mai zuwa, a Daren yau Harun zaisan matsayinsa, Dan tuni nagama da matsalarsa dama, wannan ranar nake jira, so Nuren ka bincikamin inda matarnan take zaune a yanzu, Dan ina dawowa zan shiga aikine sosai, matsalar Harun da ita da Sarauniya kowanne akwai manufa, su nasu wasan yarane a wajena. Erfan shine yajema Munaya a matsayin Fu'aad, yanzu na fahimci sune suka saka aka buga waccan jaridar, amma da saka hannun wasu a gefe........” Muftahu yay saurin cewa “yi hak'uri ranka ya dad'e zan katseka, sai yanzu wani Abu yazomin a rai, wato ranar salla a filin idi, kasan Erfaan yana tare damu, anya kuwa ba a wannan time d'in ya ganku kaida gimbiya ba, lokacin da kukayi karo, wata k'il shikuma yayi tunanin alak'a Ce a tsakaninku?”. Murmushi Galadima yayi yana lumshe ido, “ni kaina ina tunanin haka, saidai akwai wani Abu bayan wanna, dan haka sarakuna uku sun shigo cikin aikina”. Da mamaki Muftahu da Nuren sukace sarakuna kuma?. K'ala baice da suba ya mik'e tsaye, ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan ya kallesu, “gobe da safe Alhaji Shehu Darma zaije taron k'arama

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});