Chapter 55
Chapter 55
jiyar zuciya ta sauke, “yaya inaga kamar dai akwai wani Sagir dauda dana Sani, amma bansan aikin da yake a k'ark'ashin Abbanmu ba, sai kuma ya Shareffudden k'anin Aunty Umma, sai Steven Daniel”. “shi Steven d'in wanene shi a gidanku, itama Aunty Umman haka?”. “Driver d'insu Mom ne, shike kaisu anguwa, ita kuma Aunty Umma matar Abbanmu ce ai, itace amaryarsa”. “Uhyim”. Nuren yafad'a yana jinjina kai. “Dan ALLAH yayana in tambayeka mana?”. “ina saurarenki”. “laifin mi Abbana yamuku hakane?”. murmushi Nuren yayi, “karki damu nangaba kad'an komai zai wuce, kuma bashi yay laifinba, wanine yayi na kusa dashi”. “to ALLAH yasa Ku kamashi, amma dan ALLAH karkuma Abbana komai”. “insha ALLAH babie”. Murmushi Farhat tayi, Nuren kuma ya mik'e tsaye idonsa a kanta. “babu dai wata Matsala ko?”. Cikin shagwa6ar data saba tace, “please ko TV ka samin, banajin dad'in zaman hakanan”. “Am sorry to say dear, har kibar gidannan dokace, babu television, babu phones, amma way not nakawo miki irin Hausa novels d'innan danaga mata na karantawa?”. Idonta ya cika da kwalla, “ayya yayana wlhy ban iya karatun hausaba sosai, yana bani wahala”. Ido yad'an zaro waje, yace, “saboda mi? Keba bahaushiya bacene?”. “bahausa mana”. ‘tafad'a cikin turo bani irinnan ta6ararru’. Baki ya ta6e yana kama hanyar fita, “zaki cigaba da kad'aicinki ashe kuwa”. Ganin zai fice da sauri tace, “please ka siyo zan fara koya to”. “it's better”. ‘yafad'a yana ficewarsa’. Saman gadon ta fad'a ta fashe da kuma mai ban tausayi. Duk abinda ke faruwa Galadima najin komai ta waya, Munaya ma na zauna a sofa har yanzu tana satar kallonsa, amma batajin miyake saurare da ya nutsu haka. Cire wayar yafara k'ok'arin yi ya jiyo muryar Nuren na fad'in “hello brother kana jina?”. Galadima yace, “eh”. “okay duk kaji aimi ta fad'a ko?”. “duk najiku, saika samin ido akan duk d'unsu, a bincikomin komai daya shafesu”. “indai wannanne insha ALLAH angama, amma ni a ganina banda wannan Shareffuden d'in datace, domin babu wani kamanni a cikin nashi sunan, ballema tace k'anin step mom natane”. “Humm Nuredeen kenan, shifa mak'iyi ba'a rainashi, mutane da yawa sukan d'auki cinnaka ba komaiba, amma idan yacijesu sukan ji cizon har a ransu, dan haka karka ta6a d'aukar mage mafi sauk'i akan kare, itama idan taga nama citakeyi”. “wannan gaskiyane brother, ALLAH yabamu sa'a”. “amin ya rabbi, naji kuna maganar buks da ita, kaje ka samo mata dukkan Wanda take buk'ata, har English novels d'in, sannan ak'ara tanadar mata dukkan abinci mai k'yau datake so”. “insha ALLAH angon Munaya”. Girgiza kai kawai Galadima yayi ya yanke wayar. Kallon Munaya yayi suka had'a ido, saita janye cikeda basarwa. Shima tashi yayi ya koma gaban mirror, duk uzirinsa yayi ya gama sannan yamatsa ga wardrobe ya ciro kayan dayake buk'ata. Ganin haka Munaya tazame ta kwanta cikin kujerar yandama bazata gansaba. Baki kawai ya ta6e yacigaba da saka kayansa. Bayan yagama yamatsa kusada ita, “tashi ki canja kaya ki rakani wani waje”. Fuska Munaya tad'an yatsina, kamar zatace wani Abu saikuma ta yunk'ura zata tashi kawai, hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune. fita yayi abinsa. Hakan yasata fahimtar zai jirata a falo kenan. Bata 6ata lokaciba ta canja kayanta da atanfa skt da riga, takawo after dress ta saka sannan ta nad'a Vail d'in rigar, d'as ta fito itada cikinta, kamar ka saceta ka gudu abinka. Tunda ta fito ya zuba mata idanu, ko k'yaftawa bayayi, saida yaga tana gabda k'arasowa garesa ya basar yana mik'ewa. Gaba yayi tabisa abaya, yandama yake taka steps d'in benen dolene ya birgeka, duk takunsa nakan idonta, yayinda itama take binsa daki-daki a hankali. Babu kowa a falon, dan haka suka fice basu nemi kowanba. A mota yana tuk'i da sauraren karatu itakuma tana latsa waya suna charts a families group d'insu. Sai murmushi take zubawa, duk abinda take yana kallonta ta gefen ido. Sun isa wani k'aton shagon saida kayan babies, duk abinda kake buk'ata zaka sameshi indai na yarane daga 1year zuwa 15. Itadai mamaki ya ishi Munaya, miye nawani kawota nan? yabari a haihun mana ma. Tarba ta musamman aka musu, hakan ya tabbatar ma Munaya yasan mai shagon kenan, dan yanda aketa girmamasu sai abin ke bata mamaki. gashi indiyanci sukeyi bata fahimtar maganganunsu. Itadai tana zaune hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu Galadima da kuma wasu mata biyu da yaransu uku dabazasu wuce 7-7years ba, yaran k'yawawa masha ALLAH, ga wayo. Galadima ya juyo zai mata magana saiya lura da inda ta zubama idanu, shima shagala yay a kallon yaran, iyayensu na za6ar kaya amma su suna tibirewa sai Wanda sukeso za'a d'auka. Munaya sai zuba murmushi takeyi, dan suntafi da imaninta, shima murmusawa yayi yana lasar lips, kafin ya d'auke kansa ya maida ga Wanda suke maganar. Zuwa can gardama ta hark'ume tsakanin yaran akan wani game da iyayen ke dubawa maybe zasu saya musu ne. Kuma games d'in suna kusada Munaya ne, d'aya a cikin yaran ya d'akko yazo wajen Munaya yana tambayarta wai “Aunty wannan yafi dad'i aidai ko?”. Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabata ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?. Yaron ya d'aga mata kai alamar eh. Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne. Da turanci munaya tace, “yarona kai kata6a irin wannan game d'inne?”. Murmushi yamata shima, yace “aunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu ma”. “da gaske?”. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa. Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, “Aunty na koya miki?”. Munaya ta d'aga masa kai. Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace “mikenan to?”. Shima dariyarsu ta yara yayi, yace “Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal”. Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume. Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka. Wadda tace sunanta Radha tace “kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an”. Munaya tace babu komai. Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu. Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu. Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai. Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?. Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?. Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92