Chapter 14
Chapter 14
ALLAHU ranka ya dad'e zaka sameni yanda duk kake buk'ata”. Nuren yace, “good daka fahimci hakan”. Galadima bai sake cewa komaiba yacigaba da latsa wayarsa. Nuren ya kalli Malam barau yace, “malam barau kasan wanene tsohon Sarki?”. “eh kwarai ranka ya dad'e Na sanshi, shine yake jinya a India yanzu haka aiko”. “shin minene alak'ar uban gidanka da tsohon Sarki?”. A rikice Malam barau yace “ranka ya dad'e miyasa zakamin wannan tambayar? Ku gafarceni, kuyi wata amma ba wannanan ba dan ALLAH”. Galadima ya d'ago idanu ya zubama Malam barau su, jiyay zuciyarsa tana Neman fara hasala, har zaiyi maganar sai kuma miya tuna yay shiru ya had'iyeta, maida kansa yayi yacigaba da latsa wayarsa. Nuren ya bud'e k'aramar drowa dake jikin center table d'in falon, saiga bindiga 'Yar k'arama ta bayyana, Malam barau ya waro idanu waje yana kallon yanda Nuren ke d'ura Bullets a cikin bindigar. Galadima duk yana kallon Nuren ta gefen ido amma baice masa uffanba, saida Nuren ya gama sannan ya tashi ya koma kujerar kusada Malam barau, cikin d'aure face yace, “nasan dai tsoron mutuwa ko rasa aiki zai hanaka bamu amsar tambayarmu, to tabbas in baka fad'anba zan fasa kwalwar kanka da wannan gun d'in, kuma ko k'arar fitar bullet d'inta baza'ajiba ballema asan an kasheka, akuma cikin falonnan zan binne gawarka wlhy!!”. Jikin Malam barau Na 6ari yarik'e wandonsa, dan har fitsari yafara fito masa kad'an, yace, “ranka ya dad'e mi kuke son sanine?”. Galadima dake latsa wayarsa hankali kwance, batareda ya d'agoba yace, 20 ga watan Yuli miya faru a masarautar gagara badau”. “ranka ya dad'e wlhy bansan komaiba, amma tabbas ogana yafito ransa a 6ace daga wajen meeting d'in dasukayi da Sarki shida abokansa. daga hakan bansan komaiba wlhy kaji Na rantse maka”. Idanu Galadima ya d'ago ya zubama Malam barau, yace, “malam Saminu kafadda!. koba shine ainahin sunanka ba? Na sanar da kai karkamin k'arya, dan tunkan nakawoka nan nasan komai daya shafeka, amma a tashin farko kamin k'aryar sunanka Malam barau, humm abin dariya, inason mutum mai gardama dason ku6tar da kai. Malam Saminu shiga tarkon Muhammad Sameer ba abune mai sauk'iba, ina aiki da kwakwalwa, kamar yanda gangar jiki take aiki da zuciya, karka yarda a maganarka ta gaba k'arya ta shigo, idan hakan ta kasance saina binneka da ranka, wannan tabbatacciyar maganar Muhammad Sameer Saifuddeen ce”. ‘ya k'are maganar da mik'ewa tsaye yana had'a yatsunsa biyu ya buga a saitin fuskar Malam Saminu, suka bada sautin d'as! d'ass!, sannan ya ra6a ta gefensa yafice’. Nuren ya girgiza kansa, “dattijo kayi kuskure kwarai da gaske, Galadima ya wuce dukkan tunaninka, tashi mu koma inda ka fito, a yanzu kam bazai ta6a saurarenka ba sai kuma wani karon”. Hawaye Malam Saminu yafarayi yana bama Nuren hak'uri, “yalla6ai dan girman ALLAH ka kirashi, wlhy zan fad'a yanzu, wlhy nagaji da zaman kurkukunnan, nasan hankalin iyalaina da mai gidana a tashe take, ka taimakeni”. K'ala Nuren baice masaba, ya dannashi a d'akin ya maida ya kulle sannan yabi bayan Galadima. ★):(★):(★):(★)(★):(★):(★):(★):(★ Tunda suka tafi babu Wanda yay maganar, saida suka shigo cikin gari sosai. Nuren yace, “dattijonnan nakula zaiyi taurin kai gaskiya”. Murmushi Galadima yayi yana kuma lafewa cikin seat, idonsa a lumshe batareda ya bud'eba yace, “mu wuce asibiti”. Amsawa da to kawai Nuren yayi. Sun isa asibiti suka iske duk 'yan gidanmu suna nan, saisu Munubiya da Dady yace su tafi gidajensu hakanan, tundama ba bari ake aga Abban ba basuga amfanin zaman nasuba, gashi mafi yawansu duk da tsohon ciki, sai kuma Munubiya da Fauziyya da Haleematu dake fama da laulayi. Haka ba dan sun soba kowacce takama hanyar gidanta, wadda mijinta kuma yace ta jirasa ta zauna jiransa. Suma su innarmu Yaa Anas ya kwashesu ya maida gida. Lokacin da su Galadima suka shigo asibitin mafi yawansu duk sun wuce, sai mazan kawaine a asibitin. Dan haka Galadima yasamu gaisawa da Munubiya dake jiran yaa marwan yazo d'aukarta. Munubiya ta tambayi 'Yar uwarta fa?, gaban Galadima yafad'i, danshi yama manta su Munaya suna hanya, guntun murmushi yayma Munubiya yace insha ALLAH suna hanya itama, maybe su iso cikin darene kokuma da asuba”. “ALLAH ya kawosu lafiya”. ‘cewar Munubiya tana sharar hawaye’. Tabama Galadima tausayi sosai, haka ya k'arasa wajen doctor domin kumajin ko ansamu wani cigaba a jikin abban.. Doctor yamasa bayanin duk an gyara karayar jikin Abba, hakama sauran ciwukan suna samun kulawa, kuma bugun zuciyarsa ta daidaita bakamar jiya zuwa safiyar yauba. Galadima ya jinjina kai, tareda sake jaddadama doctor gargad'in kulawa da Abba d'in sosai. Yad'an jima a asibitin sannan su sarkin mota sukazo d'aukarsa, Nuren kuma daga nan hotel d'in daya sauka yanufa. ya sauka hotel ne saboda basa buk'atar wani a masarautar su Galadima yasan da Nuren d'in. ___________________________ Wajen misalin 2:30 na dare su Munaya suka sauka, Sauban yayta wayge-wayge ko an zo d'aukarsu, amma baiga alamun wani mai alak'a da masarautaba, ya kalli Munaya yana dariyar tsokana, “Aunty gimbiya Honey d'inki ya manta damu, bai aiko d'aukarmu ba, kuma inatsoron mu shiga motar haya azo a kwamushemu, kinsan yanzun kasuwancin kidnapping shine keda tsada a 9ja”. Duk da Munaya tana tare da damuwa hakan bai hanata yin dariyaba, tace, “kai yaa Sauban bakada dama, ina zamu samu waya mu kirashi to?”. Kafin Sauban yabata amsa sukaji magana a bayansu. “to maganannu, saikuzo mu wuce, wannan surutun nakuma bayasa ayi kidnapping d'in naku ba”. Gaba d'ayansu juyowa sukai suna kallonsa, Galadima ne sanye cikin wando fari 3quarter da riga t-shirt pink mai gajeren hannu. harya kwanta suka fad'o masa a rai, babu shiri yazari mukullan mota yafito, bai tada kowaba a dogaransa saboda kasada irin tasa ya fito zuwa airport, isowarsa baifi da 17minutes ba jirginsu Munaya ya sauka, tunda suka fara fitowa daga jirgin idonsu a kansa, har tsayuwarsu da waige-waigen dasukeyi na son ganin Wanda yazo d'aukarsu yana kallonsu. shagala yay da kallon Munaya, wadda sai a yanzune yaga k'ibar da Samha ke fad'in tayi, ta murje tayi 6ul-6ul da ita, har wani haske yaga ta k'ara masa, saboda hasken daya haske ko'ina a cikin airport d'in. yadad'e tsaye a bayansu, duk gulmarsa da Sauban yayi akan kunnensa ne. Sauban ya k'araso da sauri ya rungume d'an uwansa, dukda jiyane kawai suka rabu saiyaji yayi kewarsa. Galadima yad'an daki bayansa yana fad'in “k'aton banza, ka girma bakasan ka girma ba”. d'agowa Sauban yayi daga jikin Galadima yana dariya, yayinda Munaya da Galadima suka had'a idanu, gira d'aya ya d'aga mata, itakuma tayi guntun murmushi tana kauda idonta gefe. (A ranta tace d'an duniya). Juyawa yayi batare da yak'ara magana ba, Munaya da Sauban sukabi bayansa, Sauban ya shiga baya, badan Munaya tasoba tashiga gaba kusada Galadima da zaiyi driving nasu, wannan ne karon farko da zataga tuk'insa a k'asarsa. Saida yatada motar suka fita daga airport d'in sannan a hankali kamar bataso tace, “yalla6ai mun sameku lafiya?”. Juyowa yayi kad'an ya kalleta ya maida kansa ga titi, saida yaja numfashi sannan yace, “kunzo lafiya my Friend?”. Kallonsa kawai tayi kad'an ta girgiza kai, a zuciyarta tace su Friend anji jiki, zanbika a hakan kodan samun yanda nakeso a kanka, danna cika alk'awarin danama mahaifiyarka insha ALLAH. jin batace komaiba yakuma fad'in “ko gajiyar tafiyarce?”. “kusan haka yalla6ai”. Yace,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92