Chapter 29
Chapter 29
ya shiga, sannan suma suka shiga. Daga asibiti Galadima yace su wuce birnin gayu plaza. Cike da girmamawa sarkin mita ya amsa da to. Maida kansa yayi jikin seat ya kwanta tareda lumshe idanu ya fad'a duniyar tunani................✍🏼 Barkanku da juma'a💋💋💋🤝🏻. Musha weekend lafiya sisters⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀😄. *_ALLAH ka gafartama iyayen mu_*🙏🏻😭 [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 _________________________ _Duk marubucin daya kafa alk'alaminsa bisa takarda tabbas yagama tanadar yanda labarinsa zai kasance ne, amma sai wasu wabubuwan mamaki kaga sun gaza k'arewa a social Media, ban saniba ko samunmu available ne yakesa a kullum kuke mana kallon marasa aikinyi?, ni dai nasan time d'in dana shirya labarin RAINA KAMA ban zauna tebirin shawara da kowaba a online, inkuwa hakane tayaya wasu har suke tunanin nafara sauka akan layin labarin?, to magana d'aya zanyi a wannan ga6ar, ban gina labarin Raina kama akan kwanciyar aure bane, dan haka masu maganar munaya bata da aiki saima Galadima rashin kunya saisu jira saina kai k'arshen labarin kafin su k'alubalanceni, abin dariya, (wai aikina kenan daga nasa munaya ta murgud'a baki sai ta harari Galadima da masa k'unk'uni) tunda aikina kenan babu lallai wajen 6ata lokaci karantawa, haka Na tsara labarina tun farko kuma haka zanyi, duk wanda yaga bai masaba zai fara iya rubuta nashi shima kawai. wannan abun da kukema writer's yana 6ata mana rai, bai kamata ku dinga k'alubalantar writer's ba, bayan su suke da masaniyar yanda suka shirya labaransu, idanma zakuyi saiku ringa tanadar lokaci har zuwa bayan mun kammala, hakan zaifi tasiri fiyeda katsalandan a tsakkiyar labaran mu, akoda yaushe kuzama masu kula kafin Ku k'alubalanci mutum🤷🏻♀._ *Ba akan kaina kawai nayi wannan bayaninba, harda sauran writers da yawa da akema makamancin hakan koma fiye da nawa.🙅🏻* _____________________________ ~Book 2~ 👉🏻1⃣0⃣➖1⃣1⃣ ...................Koda motocin suka tsaya sarkin mota ya bud'e masa k'ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take cikin matsanancin matsi gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k'aranci, shi kansa yasan yanada buk'atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k'arancin rik'on amana Na d'an Adam ne yake yawan gargad'arsa da taka masa birki, ba kowane zai fahimci ma'anar nok'ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a makamancin halin da yake ciki......... “Ranka ya dad'e mun iso”. Sarkin mota yasake fad'a cikin taraddadi da taka tsantsan. A hankali Galadima ya bud'e idanunsa da suka koma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya ziro k'afarsa k'asa yana cije lips da had'iye wani kududun damuwa a mak'oshi. Tunda ya fito ma'aikatan wajen suketa masa sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k'asar sai yanzu ne zai shiga cikin plaza d'in. Hannu kawai yake iya d'aga musu, amma bakinsa yay masa nauyi, kallo d'aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da buk'atar hutun dake tartare da kuzarinsa. A cikin plaza d'in ma bata sauyaba, d'aga hannu agaresu shine yazama linzamin amsa gaisuwar dasuke masa. Da hannu yayma d'aya daga dogaransa nuni da amso masa key. Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar sashen da zai kaishi office d'in Saleem mai kula da CCTV camera's. Sai dai kafinma yakai ga k'arasawar suka had'u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa. Keys d'in ya damk'ama dogarin, sannan ya k'araso domin mik'a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa. Shima d'in dai hannu Galadima ya d'aga masa, hakan kuma ya saka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan. Koda aka bud'e ya shiga saiyayma dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali. Shi kansa baisan tsawon lokacin daya d'auka a hakanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske. Knocking d'in k'ofar da akayi yasakashi bud'ar baki da k'yar ya bada izin a shigo. Nuren daya shigo ya maida k'ofar ya kulle, kafin ya ida takowa cikin office d'in, idonsa nakan d'an uwannasa. Zama yay a d'aya daga kujerun dake fuskantar Galadima, “brother what happen?”. “Northing”. Galadima ya fad'a batare da ya bud'e idonsa ba. Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d'akko laptop a briefcase d'in daya shigo da ita, kunnawa yay, kusan mintuna biyu ya d'ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d'in. “Sameer nasan kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad'a labarai ta k'asarnan akan d'iyar minister, sannan jami'an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamata musan abinyi kafin lokaci ya k'ure mana”. Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya bud'e idanunsa ba yace “Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai yarinyarnan, kuma ka cire sim card d'in phone nata a lokacin daka d'auketa, to babu wata hanya dawani jami'in tsaro zai ganota, dama hanya d'ayace da kuskure zai basu damar bibiyarta, na d'aya lokacin daka d'auketa yazam wayarta na aiki, tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta biyu itace ka kashe wayarta baka cire sim card d'in ta ba daga phone nata, koda wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar 📡 su ganota” ya tashi zaune sosai yana bud'e idanunsa akan Nuren, “wannan hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu wannan basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da tsarinsa right?”. Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute d'in Galadima yana fad'in “I thrust to you my dear broth”. Shima galadima salute d'in Nuren d'in yayi yana murmushi. Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar, “yanzu inaga time d'in turama minister Massage yayi?”. Cikin zaro idanu Nuren yace “baka kallon hakan a matsayin ganganci kuwa?”. Baki Galadima yad'an ta6e yana crossing k'afarsa, cikeda izzarsa yace “sai idan nabama wani damar hakan ai”. Nuren baice komaiba, dan yagama sanin hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan zancen ya d'akko wani. “yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu fa har yanzu?”. “wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera's jikin mutane 10 danake iya zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda mutum d'aya ba, hakan ya tabbatar min da gaske Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba, ko kuma waye sakashi?”. Nuren ya jinjina kansa, “brother aini da Harun dama mun dad'e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumin kirki daman”. Lips kawai Galadima ya cije, amma baice uffanba, Nuren yaci gaba da 'yan danne dannensa a laptop d'in, zuwa wasu mintuna batareda ya d'agoba yace, “maganar Sirikinka fa?”. Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan kansa sannan ya murmusa tareda maida idonsa ya lumshe, “a daren jiya nagama da wannan matsalar, sim card d'insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum 172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya fara amfani dashi shekaru 8 kenan, wad'annan sune Sim card d'insa da yake mu'amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai acikinsa, sannan ba kowane yasan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92