Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zafafe Abbanmu naji yana fad'in “SD ubanwa yabaka damar shigomin gida ne?”. sautin tafin bak'on na jiyo dan haka nai saurin lek'awa ta kafar labule, gani nai yana zagaye Abba yana dariya da tafi, cikin shak'iyanci yake cewa “Alhaji Auwal, Alhaji Auwal! dama kanada k'yawawan 'yammata haka? Woow nice babie, idan na samu wannan ai ko rana bazata sake ganina ba, wlhy nasan zan kwashi rom........., mari Abba ya zuba masa a kumatu, yana nunashi da yatsa, a matuk'ar fusace yace, “wlhy idan ka kuma furtawa saina datse kazamin harshenka a falonnan, wawa kawai”. SD ya shafa kumatunsa sannan ya sumbaci hannun yana hurama Abba, “Kafa birgeni Alhaji Auwal, kai jarumi, 'yarkama jaruma, kai inason irin haka mutumina uhhhhhhm mutccch”. ya k'are maganar da kuma kissing hannunsa. Banza Abba yamasa ya d'auke kai daga kallonsa yana fad'in “miya kawoka gidana?”._ _Alhaji Auwal kenan, kaima kasan dakaga SD kasan zancen, a wannan karon da albishir d'in k'arin farashi akan tayin baya nazo maka, sannan kuma damace a gareka ta k'arshe hakan, mun yanke shawarar baka naira milyan 500”. Abba yaja tsaki yana hararsa, “ka koma ka sanar ma iyayen gidan naka ina kan bakana, sannan Ku farka daga barcin da kukeyi, dan bazan ta6a badawa ba, kamar yanda ban ba da jiya ba, bazan bayar yauba, sannan gobe ma bazaku samuba, wannan kuma yazama first and last dazaka shigomin gida, inba haka ba ina mai tabbatar maka zaka aikata kuskuren da bayan bayanka ma saisunyi takaicin jin yanda zaka k'are”. “kwantar da hankalinka sarkin jarumai, tabbas zan tafi, bakuma zan sake dawowa ba balle nayi nadama Oga, ammafa bazan 6oye makaba, kana bani mamaki, kak'i bama Wanda akace ka bamawa, sannan kak'i saida mana mu masu buk'ata, shikuma wannan Abu ba tuwoba balle muyi tunanin zakacine, waikai mike damun kankane haka? ka zauna kanata rik'ema Wanda yarigada ya mutum amana, shikuma Wanda kakema tanadin bashida maraba da gawa, koda yake ashefa ga Galadiman Ku nan, koshi kakema tanadi?”. “wannan ba matsalarka bace”. Abba yafad'a cikin karsashi. “kumafa gaskiyarka wannan ba matsalata baceba, amma tabbas inada yak'inin kai zata zama taka matsalar maybe ma harda santaleliyar budurwar 'yarka, lallai labarin k'yak'yk'yawa da ahalinta zai Shiga duniya kwanannan, nabarka lafiya, ka huta”._ Da sauri nabar wajen gudun karya fito ya ganni, nakoma cikin gida ina juya wad'annan zantuka na abbamu da bak'onsa, masu tsananin wahalar fassara, mi bak'on yake nema a wajen Abba dahar yake ik'irarin sun basa zunzurutun kud'i naira na gugar naira, d'ai-d'ai har miliyan d'ari biyar? Amma dukda yawansu Abba bai firgitaba balle mik'a wuya?, sannan wanene Galadima kuma? Miyake nufi da labarina zai shiga duniya? Na shiga uku ALLAH karka bama bawannan damar cutar da rayuwata ko ahalina gaba d'aya. Munubiya data lura da halin danake cikin ta sakani gaba da tambayar, tun ina k'ok'arin 6oye mata Dan kar hankalinta itama ya tashi, harna fito fili na sanar da ita gaskiyar abinda naji da kuma gani, harma Wanda na aikata. Hankalin Munubiya ya tashi sosai itama, nanfa muka Shiga kullawa da kwancewa Munason gani gaskiyar lamarin, amma mun kasa kama bak'in zaren, fita kuwa mun koma yintane a d'arare saboda tsoron furucin mutuminnan. a wata ranar talata da Abba zai dawo daga tafiya sai innarmu ta sakamu gyaran d'akinsa saboda kanta namata ciwo. muna tsaka da aikin sai muka tsinci wani file da yasha k'yak'yk'yawar adana a awani akwati dake cikin wardrobe d'in Abba, to dama da biyu muke aikin, harda bincike akan Neman hasken maganganun da mukaji ranar, jikinmu har rawa yake muka bud'e wannan file, a shafin farko mukaci karo da wani Abun daya kuma rikita tunaninmu”. 👇🏻 *_Tabbataciyar wasiyya ga ahalina, koda ace na kwanta dama kafin cimma burina ko mik'a wannan sak'on amana ga Wanda ya cancanta, to na shaida muku da cika umarnina na ida nufina a garesu 'ya'yana ko 'yan uwana, inason Ku isar da wannan amana da aka bani ga ahalin wannan masarauta............”._* “iya nan rubutun ya tsaya, muka bud'e shafin na biyu kozamuga sunan masaurar da Abba ke magana da k'arashen zancensa, amma sai sunayen mutane muka gani a k'alla sunkai goma. Wucewa mukayi shafi na uku, a dai-dai wannan lokacin Abbanmu ya shigo d'akin batare da mun Ankara ba, wata hargitsatstsiyar tsawa mai tsinka hanji ciki da zukata ya daka mana yana fad'in “ku harkunkai girman da zakumin bincike a d'aki a matsayina na mahaifinku? mi kuka sani akan wannan takardar dahar kuke binciken abinda ke cikinta? Yaushe kuka koma la6e?”. haka Abba ya rikice gaba d'aya muma ya rikita mu, ya dinga zabga masifar dahar tajawo hankalin jama'ar gidanmu, indai tak'aice maka bayani har innarmu saida fushin Abba ya shafa ranar, hakanne yasani fahimtar Abba ya gane naji komai a ranar. munshiga damuwa a time d'in matuk'a, dukda hak'urin da muka bashi yak'i saurarenmu, ya d'au tsawon lokaci yana fushi damu kafin ya daina. bayan komai ya daidaitane kuma wani yammaci mun fito daga school saiga motocika a jere suna tsula uban gudu a titi, wucewarsu tamkar iska yasakani fad'ar bak'ar magana ga manyan k'asarnan har 'yan uwana na tayani. Sai kuma mukaji sunanka a bakin wani saurayi da 'yammata biyu. Wannan ganinaka ne yasakani dawoma Munubiya da abinda ya wuce, saboda sunan Galadima da mukaji saurayinnan ya ambata, sai muka dinga tunanin kokaine Wanda muka ta6aji a furucin bak'on Abba?. ga kuma sunan masarauta da muka gani a rubutunsa, dukda bamuji sunan ainahin masarautarba kuma, balle mu tabbatar da kaid'inne.. Ganinmu dakai na biyu kuma saika bani haushi, dan ganinka mutum mai yawan izza, sainaga bebekin Abba daya saka kansa had'ari akan Wanda shi baima damu da damuwar kowaba sai tasa gakuma tarin girman kai Dana hango tartare dakai”. (Kafayi hak'uri, gaskiyata nake fad'a, guntun murmushi kawai Galadima yamata baice uffanba) taci gaba da fad'in “Wannan ne dalilin yimaka tsak'i a asibiti, idan har baka mantaba, har dogarinka d'aya yataho da zummar d'aukar mataki amma ka dakatar dashi da fad'in ya barni”. Galadima ya murmusa alamar bai mantaba. Nace, “ka tuna kenan?”. “Na tuna kwarai da gaske, dan bancika manta abuba saidai idan na d'aukeshi mara muhimmanci, amma a time d'in ai banga face nakiba, shiyyasa banida tabbacin kece, saidai na muku kallo d'aya a lab da muka iskeku keda sisters d'inki, ni nama zata Ku 'yan uku ne ai”. “Umyim, amma a time d'in babuma Wanda zai d'auka Kasan da zamanmu a lab d'in, dan gaisuwar da ake maka ma, kamak'i amsawa sai d'aga hannu, hakanne ya tunzurani na fito daga lab d'in, dasu munu sukace kainema kabada jinin da za'a sakama feena ban yardaba”. Baki Galadima ya d'an ta6e yana shafa kwantaccen sajensa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “bazaki fahimta bane yalla6iya. yanzu labarin da kika bani ya farune duk a wace shekara?”. Na d'an ya mutsa fuska ina fad'in bamai nisa bace, dan ko 2years cikakku baza'a k'ulla ba, Muna Exam d'in NECO nema, dan har results d'inmu suka fito aka fara biyan JAM Abbanmu ya biyama sauran 'yan uwanmu amma banda ni da Munubiya, sai baba k'aramine ya biya namu, so munfara karatu dai babu dad'ewa muka shirya da Abbanmu saboda magana da dad d'insu Ayusher yamasa Yakuma sake bashi hak'uri. tundaga nan komai yazama Normal. Amma kaikanka yakamata kayi mamakin yanda a

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});