Chapter 59
Chapter 59
bazai zargi wani abuba kuwa?”. “miyasa kikace haka?”. Shiru nad'anyi, dan ganin ina neman zirma kaina, saina d'an murmusa kawai cikin basarwa, nace, “waynot abashi ba kai tsayeba”.. Murmushin gefen baki yayi, yace, “y'ar tsuntsuwata wai mikike tunanine? da har kiketa kwana-kwana haka?”. Baki na tunzuro gaba, ina fad'in “nidai ba tsuntsuwa bace ba”. Dariyace ta kufce masa babu shiri, yasaka hannu yana rufe bakinsa. Haushi ya kamani na d'auki filon dana kwanta na jefa masa. da sauri ya cafe yana cigaba da dariyarsa, hakan yasa najawo na kujerar ina cigaba da kai masa duka yana karewa da wancan. daga k'arshe sakkowa yay yahad'a nida filon ya rik'e yana fad'in “sorry sorry na bari, ba 'yar tsuntsuwa ba giwar mata”. Hararsa nayi nafara kukan shagwa6a kuma. dariya Yakuma sakawa yana fad'in “toni bansan mikikeso nace mikiba kuma?”. “ni banaso duka”. “to shikenan nabari, yanzu dai yaza'ayi Ring yaje yatsan Abbanmu to?”. ‘yay maganar yana d'ora kaina jikin kafad'arsa’. “saika fad'amin sirrin sannan zan fad'a nima”. Ya murmusa yana jan hancina, “kin cika wayo yarinyarnan wlhy”. K'aramar dariya nayi nace, “ai awajenka na koya”. Murmushi kawai yay baice komaiba, ya jawo wata 'yar k'aramar bag mai k'yau fara ya mik'omin. Kar6a nayi ina tashi zaune sosai na bud'e jakkar ina fiddo kayan ciki, agogone mai masifar k'yau da tsari, na azurfa 'yar asali mai tsada, sai wani d'an akwati da ring mai k'yau na azurfa shima, an masa ado da farin stone mai garai-garai tamkar diamond, na jujjuya zoben kafin na d'ago mu kalli juna ni da Galadima, ido d'aya ya kashemin😉. Janye idanuna nayi nakuma maidawa ga zoben ina k'ok'arin sakashi a yatsana, saidai yamin yawa sosai, na cire ina fad'in “amma gaskiya zobenan ya had'u sosai yalla6ai”. “duk haduwarsa bai kaikiba ai”. ‘yay maganar acikin kunnena’. Kallonsa nayi, amma saiya basar tamkar bashi yay maganar ba. Lips na cije na d'an hararesa. Shikuma ya ta6e baki. Na maida kayan duk a cikin bag d'in dad'an hanzari ina rik'e cikina dayay wata wuntsulawa. “lafiya?”. ya fad'a yana rik'o hannuna. 'Dagowa nayi na kallesa da k'yar, da hannu na nuna masa cikina dake juyamin, jinake kamar numfashine zai bar jikina. Babu shiri ya dire wayar hannunsa ya rik'oni jikinsa da k'yau. Sosai na fara murk'ususu ina kuka da k'ank'amesa, dukya rikice, yama rasa mi zaiyi?. Ana cikin haka saiga sallamar Aunty Mimi dataga shirun yayi yawa sun dawo ban sakkoba, saitai tunanin kobana jin dad'ine, sallama tayi Galadima ya amsa murya a rikice, hakanne yasakata shigowa batareda jiran isoba. Da hanzarinta ta k'araso tana tambayar miya faru?. nidai kuka kawai nake ina kuma k'ank'ame Galadima. Shine yasamu damar mata bayani sama-sama, yak'are maganar da fad'in “Aunty mutafi asibiti please, maybe haihuwa Ce?”. Da sauri tace, “badai haihuwaba Sameer, cikin dake wata takwas, kaga ina zuwa”. Ta fita a hanzarce. Babu dad'ewa sai gata tadawo da innarmu da jakadiya, dak'yar innarmu ta amince ta hawo, danma taga tsantsar rikicewar da aunty Mimi tayine. har yanzu dai kukan nake ina jikin Galadima dashima dukya koma kalar tausayi kamar zaiyi kukan. Ganinsu a haka yasaka innarsu munaya k'ok'arin komawa da baya, dan saitaji kunya ta kamata, dukda tasan suma bada son ransuba ne. ita kanta jakadiya taji kunya. ganin innarsu munaya zata gudu Aunty Mimi tayi azamar rik'o hannunta. “please inna karki duba ta kunya, halen datake cikine abin dubawa, kowa yasan dai ba haihuwa baceba tunda da saura”. Ajiyar zuciya inna ta sauke, batare da ta motsa daga inda takeba takuma musu kallo d'aya ta d'auke kanta, tace, “inaga juyine ai, zai lafa insha ALLAH”. ‘tana gama fad'a ta fice abinta’. Jakadiya da aunty Mimi suka kalli juna, murmushi jakadiya tayi, tace, “gaskiya ta fad'a, juyine, amma nadad'e banga uwa mai kawaiciba irinta a wannan zamanin”. Murmushin itama aunty Mimi tayi, ta maida kalonta kansu, yafara lafawa sosai, dan haka munaya tafara tsagaitawa da kukan. Galadima yakuma k'ank'ameni a jikinsa sosai yana shafa kaina, nikam sai ajiyar zuciya nake saukewa tareda shashshekar kuka, ya manna min kisses a kaina idonsa a lumshe, danshi yama manta dasu Aunty Mimi a d'akin. Jakadiya ma dai lalla6awa tai ta gudu, dan taga magajin gari yau sai a hankali. Aunty Mimi ta tako inda suke ta zauna a sofa tana fad'in “sannu Munaya”. Bud'e ido Galadima yayi, harsun kad'a zuwa launin jaa, yad'an furzar da iska yana lek'a fuskarta, barci ya d'auketa. ido ya d'ago yana kallon aunty Mimi dake kallonsu cike da sha'awa, tamasa murmushin kwantar da hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana cije lips da jinjina mata kai. Tace, “tayi barcine?”. Nanma kansa ya jinjina mata, yana gyarama Munaya kwanciya a k'irjinsa yanda zataji dad'i, yace, “Aunty Mimi amma yakamata muje asibiti aga miye matsalar?”. “karka damu my k'ani, juyine kawai, insha ALLAH babu wata damuwa. bara inje nima saida safe, idan kuma kaga dawata matsala saika kirani muje asibitin tunkan dare ya kumayi”. Bayan fitar aunty Mimi kuma k'ank'ameta yayi yanamai jin tausayinta na ratsashi, ya sumbaci goshinta, kafin ya d'auketa dukda nauyin datayi ya maidata saman gadon, yanzunma a jikinsa ya sakata, yaja bargo ya lullu6esu tareda musu addu'ar kwanciya. Cikin barci ta farka da wata matsananciyar yunwa, k'irjin Galadima na shiga girgizawa ina kuka. Galadima ya farka a firgice yana rik'e hannunna, ya yunk'ura da k'yar ya tashi zaune, “miya faru?”. ‘yafad'a cikin muryar barci’. “yunwa yalla6ai, abinci xanci, kafad'a masa magana yabar halbina”. Dukda tabashi tausayi saida ya murmusa, sauka yay yafita, k'asa ya sauka zuwa kitchen, yau saiga Galadima a kitchen🤣, rasa mizaimayi yayi, ganin yana 6ata lokacine kawai dan ba iya uwar komai yayiba saiya fice, dole yaje ya tado kukunsu. Mai aiki da aikinsa dannan saigashi ya had'a mata Abu mai sauk'i, Galadima ya kar6a da kansa Yakoma saman. Isketa yayi zaune tsakkiyar gado tana kuma rurus, saita k'ara bashi tausayi, ya haye gadon da abincin, da kansa yabata yana lallashi. saida tayi nak sannan ya sauka da tiren yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Nikam hankalinna kwance nazame na kwanta, barci ya sake kwasheni. Mamaki yasakashi tasata gaba yana kallo, saikace wata mai aljanu, lallai duk namijin daya kasa tausayawa matarsa lokacin da ciki yake jikinta yacika mara tausayi number d'aya, babu abinda miji zai iya biyan matarsa dashi akan rainon cikinsa datayi da tarbiyyar 'ya'yansa, amma a wannan time d'in wani namijinma rashin tausayinsa ke tashi akan matar, ALLAH ya ganar dasu to. Amin galadima🙁😔. ********************** Washe gari A safiyar yau su Abba suka tashi da shirin komawa Nigeria, gaba d'aya saina tashi duk babu dad'i, jinake kamar karsu tafi, dana tuna yaune zasu barmu sai hawaye ya zubomin, inama zai amince nidai nabisu mu tafi tare?. Agogo da zoben jiya na d'auka nafita masaukin su Abba, dan Galadima ya fita tunda sasaafe, bansan ina yajeba. Saida nayi sallama aka bani izinin Shiga sannan na shiga, Abba na zaune a bakin gado agogo rik'e a hannunsa suna magana da innarmu dake tsaye ita kuma tana zuba sauran kayansu a k'aramin akwati. Abba yay murmushi yana fad'in “sannu munaya kinji”. Murmushi nayi a kunyace, na dafa gadon zan durk'usa k'asa na gaidasu amma saiya dakatar dani ta hanyar rik'e hannuna, “kinga zauna, inake ina durk'uso yanzu”. da taimakon Abba na zauna a kujerar dake kusada gadon, sai faman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92