Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Aunty salamah tazo, daga ni har Munubiya da Ayusher rungumeta mukayi. Cikin tsokana ta ture Munubiya da Ayusher tana fad'in “ku matsamin, kullum Ku ina ganinku, kewar gambo nakeyi”. Gwalo na shiga yi musu, mama Rabi'a da Feena namana dariya. Bayan mun zauna Aunty Salamah ta shiga yaba canjawar danayi tanamin shak'iyanci, nanfa su Munubiya ma suka samu abinyi, sosai suka tasoni gaba sai mama Rabi'a ke kareni. Can muna tsaka da hira takamo hannuna tana fad'in “zo nabaki wani sirri nan autana”. Mik'ewa mukayi inamasu Ayusher gwalo, yayinda suma suka tubure basu yardaba sai an bada sirrin dasu. da k'yar muka samu muka shige d'aki muka kulle. A bakin gado muka zauna Aunty slamah ta sauke ajiyar zuciya tana kamo hannuna cikin nata, serious nima na zama na maida hankalina gareta. Tace, “Munaya! Aiki yatafi yanda ya kamata, saidaifa labarin ya canja daga yanda kike zato, Muftahu ba munafuki baneba”. A matuk'ar razane naja baya ina ture hannunta daga cikin nawa, “Aunty kinsan mi kike fad'a kuwa? Anya yaranki Muftahu suka kama?”. Hannuna ta kamo tana murmushi, kinga zauna, shiyyasa na saka aka d'auki komai dan kema ki gani da idonki”. Zaman nayi kuwa, ita kuma tayi 'yan latse-latsenta a iPad d'inta ta mik'omin. kar6a nayi cikeda fargaba, da kaina nayi playing d'in video n, tun daga fitowar Aunty salmah daga mota har shiganta cikin gidan zuwa shigarta d'akin, tsayarwa nayi na kalli Aunty ina dariya, “kai Auntynmu kinfa iya Acting wlhy, wanifa saiya d'auka da gaske irin mugayen hamshak'an matan nanne”. Dariya Aunty Salamah tayi, “wlhy koni dai nayi mamakin dakewata, bakiga sai wani hura hanci nakeba, sukuma su Ameer saikace guards d'in irin manyan mutanan nan”. Dariya mukayi, sannan nakuma playing na cigaba da kallo. Shigar Aunty Salamah d'akin da tattaunawarsu da Muftahu. gaba d'aya jikina yayi sanyi, zuciyata sai wani tsitstsinkewa takeyi, idona cike da kwalla nace, “anya gaskiya Muftahu yake fad'a Aunty Salamah?, wlhy da gaske fa shine ya saka mana desire tablets, inhar bada wata manufaba miyasa yay haka?, kumafa ni banta6a ganin wani alamar rashin gaskiya ba ajikin Harun”. Murmushi Aunty Salamah ta yi, ta dafa kafad'ata tana fad'in, “Munaya mugu bashida kama, Ai Muftahu baisan nid'in ba matar sarkin bace ta gaske, mizaisa ya za6i 6oyemin? yanda yanuna akan k'yamar matar sarkin tabbas akwai mai mugun hali a cikin su da gaske, kinga ai kince bakiga fuskar wanda kika kama yana wayarnanba a bayan window d'inki randa kuka iso”. “Eh hakane, ban ganiba, maganganun kawai naji”. “to kin gani, kifa tuna kuma firar da kika ta6aji Galadima nayi a asibiti shida aunty Mimi. wad'annan alamomin sun nuna akwai wata a cikin matan Sarki dakeda hannu a ciki, maganar Harun kuma idanu zamu saka masa tamkar yanda mukaima Muftahu, dan ayanzu idan mun saki Muftahu zakiga sun cigaba da takun sak'ar datafi ta da zafi, dan nariga da nasaka rud'ani a zuciyar Muftahu cewar zamu kashe galadima, tabbas ta wannan hanyar Harun zaizo hannunmu. Maganar Galadima kuma har yanzu karki fara kwantar masa da kai, dan kwantar da kanki zai d'arsa masa rashin aiminci a kanki, ke dai kinsan halin mijinki ai yanzu, kinkuma fi kowa sanin yanda yakamata ki cigaba da tafiya da shi”. Insha ALLAH Aunty zan cigaba da k'ok'ari nakuma gode da gudunmawarki akanmu, sai dai akwai matsala, dan na lura agogon hannun Muftahu kamar akwai wani sirri a cikinsa, dolene a daren yau a fitar da Muftahu daga gidanan, zanma sarkin mota bayanin yanda zai taimakeku a maidashi masarauta kamar yanda yaymana aikin d'akkoshi, shima Galadima zansa ido akansa saboda tsuntsune shi nai azabar wayo”. “Hakan yayi Munaya, ALLAH ya cigaba da bamu nasara, insha ALLAH zamu gano komai, ALLAH dai yabama Abba lafiya, yasa mu fahimci komai cikin sauk'i, akan Galadima kuma kici gaba da k'ok'arin da kikeyi Fiyeda da, dan dolene saimun samu had'in kansa kafin musan komai, ALLAH ya ku6tar damu baki d'aya, dan kina dai ganin yanda suka maida Abba”. Hawayen da suka ziraromin a kumatu na share, cikin Murmushin k'arfin hali nace, “insha ALLAH Aunty Salamah, domin raina da farin cikina fansane akan mahaifina, kuma zuwa yanzu Auren Contract bai damuna, sai dai bazan 6oye mikiba aunty Salamah wannan cikin shine damuwata a yanzu, inaji ina gain zan haifishi na barsa inda yafi k'arfina, bansan wace rayuwa zaiyiba a wannan gidan da kowa zuciyarsa takeda k'arancin imani, Aunty Salamah gidan sarauta tsantsar matsalace kawai, bazaki fahimci hakaba saikin tsinci kanki a ciki, Aunty dan ALLAH ki amince na zuba da cikinnan”. “munaya waishin miyasa bakida hankaline? to idan baki saniba wannan cikin shine zai zamemiki tsanin mallakar cimma nasara, kuma ta hanyarsane kawai zamu samu had'inkan Galadima domin fidda Abba daga wannan matsalan da Ku kanku ahalinsa, kina tsammanin koda Abba mutuwa yay masu farautar rayuwarsa zasu barku Ku6utane? Dolene saisun samu abinda suke nema koda ace dukkan gidanku zai k'are, bak'ya tunanin aurenku yana cikin abinda yakuma hasala zukatansu, a zatonsu Abbanki yasamu damar had'a kan mijinkine, ya ina jinjinama fik'irarki ke da munubiya kuma zaki 6ata shirin, karma ki bari 'Yar uwarki taji maganar zubda cikinnan, wlhy zaku samu Matsala ne babu ruwana”. Munaya ta share hawayenta, “shikenan Aunty Salamah nabar maganar insha ALLAH. Amma a yaran nan masu mana aiki bak'ya tsoron wani yaci amanarmu?”. “komai zai iya faruwa, domin amana tayi k'aranci a rayuwa, tunda yau gashi Harun yafito cikin masu cin dunduniyar Galadima, amma ki kwantar da hankalinki, su duka ukunnan da kike gani amintattunane, kuma Saleem ya saka mana idanu sosai a kansu”. “to Alhmdllh aunty, ALLAH kamana jagora”. “amin dai, saikima Munubiya dukkan bayanin da mukayi, ki bata itama ta gani, zuwa gobe zan aiko Bilkisu ta kar6a min, kuma ki fad'a mata yakamata ta koma gidan ta, dan gaskiya aiki bazai cigaba da yuwuwaba tana gidannan, saboda kinga ba ita kad'ai baceba, yanzu haka randa zaku zo da zamu kama Muftahu wlhy nasha wahala wajen nemanta naji kokin iso? dan ta tabbatar min inhar kin iso k'asarnan saitaji a jikinta, amma naita kiranta batayi picking ba, ashe wai wayar na hannun Feena”. murmushi nayi nace, “sorry sweet auntynmu, insha ALLAH zata koma gobe”. “shikenan, bara na wuce to”. “to Aunty ngd sosai, ALLAH ya bada ladan zuminci, ammafa gaskiya kinci zalin muftahu da yawa”. Dariya tayi sosai, “kibari kawai, nima wlhy ina marinsa tausayinsa Na ratsani, insha ALLAH zan nemi yafiyarsa zuwa nan gaba, ALLAH yasa ya yafemin dai”. “hhhh zai yafe miki aunty ai duk cikin aikine”. Mun rakota har tsakar gida, su Munubiya na tsokanarmu wai nad'an sammusu sirrin suma. Daga ni har aunty Salamah dariya mukayi kawai. Bayan dawowarmu na turama Munubiya massage akan taje tagani itama. Sai da taja wasu times sannan tamik'e tana fad'in bara tad'an watsa ruwa. duk muka amsa da to saita fito. ************************** Su Abba sun isa lafiya, anzo da motar Ambulance d'in asibiti aka d'auki Abba, yayinda Sauban da baba k'arami da inna khumar yazo d'aukarsu su kuma. Inna da baba k'arami sai baza ido suke suna kallon gari. Gida suka wuce kai tsaye, yayinda aka wuce da Abba hospital shikuma. Sun iske jakadiya a gidan, dandanan aka shirya musu abinci, itadai inna sai jinjina k'yawun wannan gida take, yanzu anan gidan jininta ta rayu?. shi kansa

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});