Chapter 68
Chapter 68
aunty gimbiya ya mantar dashi”. Itama rungumeshi tayi cikeda farin ciki, “hakane wlhy my love, yau ina cikin farinci mai tarin yawa, tarihi ya maimaita kansa da wani sabon salo mai banmamaki”. “Wlhy nima haka Momma, kallafa pictures d'in babies d'inmu”. Dukda tagani itama bata katse masa hanzariba ta kar6a wayarsa tana kuma kallo, harda na Munubiya. Momma tace, “kai yau innarsu yazataji, jikoki 5 a lokaci d'aya, baiwar ALLAH, dama mahak'urci mawadacine, tayi kukan shekaru masu yawa ga lokacin dariya kuma yayi”. “wlhy kuwa momma, nakira Yaa Sam batajeba”. “Ai yama manta wayoyinsa a nan, kasan sun tafi hankalinsa ba kwance ba, nima da wayar Muftahu mukayi wayar”. “wayyo Momma dan ALLAH kicema Yaa Sam mutafi gobe, wlhy kamar nayi tsuntsuwa na ganni a 9ja nakeji”. Dariya Momma tayi, tarasa inda zata saka kanta dan dad'i. Motsin da Abie ya farane yasakasu maida hankali garesa, idonsa ya bud'e ahankali a kansu. ganinsu tsaye kansa sunata murmushi saiya ma Momma alama da ido wai miya faru?. Da sauri Sauban ya rungumesa yana fad'in “Albishirinka Abie d'inmu, matar Yaa Sam y'ay'a uku ta haifa”. Ba k'aramin shock bane ya kama Abie, ya kalli momma alamar da gaske?. Kanta ta jinjina masa tana murmushi. Wasu hawayen dad'ine suka gangaro a kumatunsa, fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi, A hankali yaketa jero Alhmdllh. Yace, “Mafarkina na shekaru da yawa yazama gaskiya Zeenah, tabbas ubangiji shine masanin gaibu, ya ALLAH na gode maka, godiya marar yankewa balle gajiyawa”. A hankali yake maganar Amma su Momma naji saboda sun matsar da kunuwansu. Dad'i duk yakuma lullu6esu, Abie yakuma fad'in “Zeenah wannan yarinya ta zama alkairi ga Ahalinmu, ALLAH ya albarkaci rayuwarta da abinda ta Haifa daku ma gaba d'aya”. Sauban da Momma suka amsa da amin. Yace a kira masa Galadima. A time d'in sunta neman Number Mom amma bata wuceba saboda Network, hakama ta Nuren da Muftahu, daga k'arshe dai sun hak'ura ne sai wani lokacin a sake gwadawa. Yau dai kam har doctor's d'in Abie sun shaida yana cikin farinciki, dan jikinsa ma ya nuna haka, k'arfin muryarsa ya k'aru, hakama bugun zuciyarsa dawasu yankunan halittun jiki dake bama d'an adam garkuwa, sun tabbatar a kowanne lokaci ALLAH zai iya gwada ikonsa ga wannan bawa, bayan tsawon shekaru daya d'auka a kwance sai an juyashi. Wannan albishir ya k'ara yalwata farin cikin wannan ahali, saima dasu Samha suka iso, duk sun rikice da ihun murna, yau d'in ta dabance a ransu. Isowarsu ce ta tunama Galadima da ranar haihuwarsa dai-dai da haihuwar yaransa, kuma dai-dai da haihuwar su Munaya ma😳😜. Wannan abin al'ajab da yawa yake, ita kanta munaya sai lokacin ta tuna, wayar Ayusher ta kar6a ta kira Munubiya tana mata tuni da ranar haihuwarsu. dad'i ya kama Munubiya ma, dan itama ta shafa'a, sai murna kan murna ta k'aru🤸🏻♀. ************************** Uban gayya dai Galadima da k'yar barci 6arawo yake sace sa a kowace rana, daya rimtse ido 'y'ay'an sa kawai yake hangowa, badan kar aga rashin hak'urinsa ba shikam da dasu zai ringa kwana. O baban zumud'i😘😘😽. A 6angaren yalla6iya ma hakane takan kasance, da taga laraba tayi barci dash Ayusher da Samha, (dayake itace take kwana dasu) saita tashi ta dinga d'aukarsu d'ai-d'ai tana runguma da musu addu'oi, jitake kamar ta had'iye kayanta ta huta kawai, takan dad'e tana Abu d'aya kafin barci yaci k'arfinta take kwantawa. Tosu yalla6iya anaso ana kaiwa kasuwa😂😜. ************************* Fad'a muku yanda abubuwa suka cigaba da kasance ga y'an barka ai 6ata lokacine ma, dangin Munaya ma sun taka rawar gani, Ayusher ma dai ta dawo nan zata zauna har ayi suna, hakama madam Innaro Galadima da kansa yaje ya kwasota🤣😜, aiko baki har kunne. Gaskiya fans sannunku da k'ok'ari, irin wannan tururwa haka, lallai kunma Galadima halacci shida yalla6iya, ALLAH ya saka muku da alkairi dai my sweetness🥰🥰🥰😘😘😘😘❤🤝🏻. Dole Galadima ya nemi waya da sim card ya lalubo su Abie da Momma d'insa da jakadiya dabasu samu zuwaba, suna shan hira a kullum shida su Abie ta video call, ga jarirai aita jera musu sunata shan kallo abin birgewa, Abie jiyake kamar yay tsuntsuwa ya gansa a 9ja, tsakanin nan yana cike da kewar k'asarsa ta haihuwa, yana fatan yakuma takata ko sau d'ayane kafin yabar duniya. “Insha ALLAH zaka taka da yawa Abie😭”. Mu tafi ran suna kawai😨⛹🏻♀⛹🏻♀. Abubuwa da yawa sun faru a kwanakin bakwai d'innan, sai dai Alhmdllh bamasu tayar da hankali bane, dan jinjirai suna cikin k'oshin lafiya da kariyar ubangiji. Samha dai konan dacan bata matsawa, duk wani motsinta nakan yaranan, tazama bodyguard d'insu itada Ayusher da hajiya innaro, dan itamafa ta kafa ta tsare🤣. Mama Fulani dai ta danne zuciyarta tazo har sashen Galadima taga babies, harma suka samu k'yauta mai tsoka daga gareta. Ana gobe suna masarautar gagara badaufa tayi dank'am da jama'a, dan bikin suna na ban mamaki Sarki ya shirya, abin ba'a cewa komai. Inno ma dai wannan karon ba'a barta a baya ba, tazo masarautar su sunan tatta6a kunnenta, kuma 6angaren mama Fulani ta sauka😳😜. Koba komai zata kafa zata tsare, takuma raka ta jira🤸🏻♀😂 mana ga Mama Fulani. Harun da baya k'asar yayi tafiya a fannin aikinsa yau ya diro a Daren suna cikin masarautar, dama tun yana can labari yagama Isar masa Galadima ya samu y'an uku, Muftahu da kansa ya kirashi ya Sanar masa haihuwar, Yakuma tura masa hoton babies😽🤥 ***************** Wajen 8pm Galadima suka dawo daga masallaci sallar isha'i, shikad'ai ya shige falonsa, dan yana son magana da Munaya, gaba d'aya yinin yau tun safe daya Shiga bai samu komawa wajensu ba saboda hidimomi sun masa yawa. Ayusher ya kira, dan itama Munaya batazo da waya ba, lokacin da su Sauban zasu taho kuma basusan inda ta saka layinta Na Nigeria ba, sai sukaga babu amfanin d'akko wayarma. d'agawa Ayusher tayi, Galadima yace ta bama Munaya. Murya k'asa-k'asa tace bata da lafiya. Tashi yay daga kwanciyar da yayi, yace, “ciwon cikin ne dai?”. “eh shine wlhy Yaa Galadima ”. Dukda kunyar shiga mutanen yake dole ya mik'e ya fita, sashen nasu kam Alhmdllh da yawan jama'a babu laifi, ga yawan bayi da suka k'aru saboda inno da tawagarta, dukda ba'anan ta sauka ba. Tunda ya fito suketa gaisuwa da jama'a, wad'anda ma basu sanshiba yau sun gansa, musamman wasu a y'an uwan Munaya. cirko-cirko ya iskesu tsaye, Munaya Na kwance a gado ta cure waje d'aya da alama tanajin ciwon sosai, Aunty Mimi nata faman jijjiga yaron d'aya dake kuka. Duk kallonsa sukayi, cikin damuwa yace, “ciwon cikinne?”. Da eh suka amsa masa, ya taka zuwa gaban gadon ya zauna kusada ita, har zai ta6ata Mom tamasa nuni da a'a ya barta. dakatawa yayi shima ya zuba mata ido cikin tausayawa, gaba d'aya fita hayyacinta take idan cikinnan yana ciwo, kuma saida ta kwana biyu da haihuwa sanann yafara. ya tsira mata idanu ganin yanda take zufa, dukda garin akwai sanyin ruwan da akayi da yammaci. Yakai tsawon mintuna 30 a zaune kafin ya lafa mata, ahankali tafara gyara kwanciyarta tana mik'ewa sosai, da Galadima suka fara had'a ido, yace, “sannu”. Kanta ta d'aga masa cikin murmushin k'arfin hali, suma duk sukai mata sannu sauran. Nanma ta amsa cikin d'aga kai. Maganin da laraba ta tace a Kofi ta mik'o mata,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92