Chapter 66
Chapter 66
yalla6iya?”. ‘ya k'are maganar cike da tsokana’. Ta murmusa tana mik'ewa tsaye, wardrobe ta nufa ta fiddo sabbin kayanta cikin na lefe, bata kuma kallonsa ba ta wuce bathroom domin saka kayan. Binta yay da kallo harta shige, yasaki miskilin murmushi yana kwantawa kusada yaran, a fili ya furta “yarinya nasan matsalarki”. yay maganar yana sumbatar kuncin na kusa da shi, sauran kuma ya shafa Kansu. A haka Munaya ta fito ta iskeshi, ya ta6a wannan ya ta6a wancan, kallo d'aya tamasu ta d'auke kanta. Sallamar da akayi a bakin k'ofar ya saka Munaya amsawa da bada izinin shigowa. Laraba tashigo d'auke da tire babba. Da sauri Munaya ta nufeta ta kar6a, Dan dattijuwace sosai, sannu ta mata tana fad'in “iya aida wanine ya kawo”. 'Yar dariya laraba tayi, tace, “dole na kula da amanar uwar gijiyata ai ranki ya dad'e”. Munaya da Galadima suka kalli juna suna murmushi, Dan sunsan inno take nufi. Laraba ta juya zata Fifa saboda ganin Galadima na nan. Kiranta yay ta juyo, yace, “zokiyi aikinki kar Inno taga ta rame tace baki rik'e amanaba, nima yarana abincinsu suke buk'ata”. Hararsa Munaya tayi, yay Biris kamar bai gantaba, saima d'an yatsansa daya saka cikin hannun yaron, shiko ya rik'e gam tamkar yasan minene. Laraba tace Munaya ta zauna ga abinci taci.. Yamutsa fuska Munaya tayi, kamar zatayi kuka tace, “wlhy iya bakina banajin d'and'anon koda yawuna ma”. “hakane ai saidai hak'uri ranki ya dad'e, dama wasu idan sun haihu sukanyi k'am baki, amma a hankali zai canja”. Badan munaya tasoba ta zauna, laraba tabata kunu mai k'yau da aka dama don ita, sai k'amshin kayan yaji yakeyi, sai farfesu. Kallon abincin kawai Munaya keyi, amma ko kad'an batajin sha'awar ci, ta tuna kwanakin baya da idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi wajen son ci, hikimar ubangiji daban ce, ta d'ago ido suka kalli juna itada Galadima dake kallonta tun d'azu, a zuciyarsa yana tuna kwanaki uku rak dasuka shige, yanda ta maida abinci, murmushi yamata ta d'auke idonta ta maida ga abincin. A haka Mom ta shigo ta iskesu, zama tayi tana fad'in “yanaga bakici komaiba?”. Idon Munaya cike da kwalla tace, “ALLAH mom banajin d'and'ano”. Zama mom tai kusada ita, tace laraba taje itama ta karya. Kunun ta d'auka ta tsiyaya a Kofi ta d'iba mata farfesun, “kar6a maza runtse ido ki shanye kunun nan d'iyata”. Kunyar Mom ta sakata k'ar6a tana had'iye kwallarta, tafara sha badan tanajin dad'inba, sai dan tsatstsareta da ido da Galadima yayi shida Mom. ahaka dai tasamu tasha yafi rabi, dama yunwar takeji, dad'in bakinne kawai bataji, shima farfesun tad'anci, dandanan tafara zufa. tace, “Mom dan ALLAH bara na kunna AC”. “a ina?”. ‘galadima ya fad'a yana tashi zaune da sauri’. Ita mom ma dariya ya bata, yawani had'e fuska yana harar Munaya, “malama babu wani AC da zaki sakama mutane anan, kina ganin yara duk da mura sukazo duniya saboda rashin jin maganarki.....” Mom ta katseshi da fad'in “ai bama zai yuwuba, itada ke jego ko fankace a d'akinnan ai saidai kallo kuma, yanzu ruwan sha ma sai mai zafi”. Galadima ya sakko daga gadon yana fad'in “hakan ai shine dai-dai wlhy, remote d'in AC d'in ya d'auka a lokan gefen gadon ya masa yanda bazata iya control d'insa bama gaba d'aya, sannan yafice abinsa yana murmushin mugunta. Mom ta girgiza kai kawai, a ranta tana mamaki canjawar Sameer...... Maganarsa ce ta katse mata tunani, harya fita ya dawo baya, “mom ga maganinta nan tasha, kuma yaranan yunwa sukeji”. ‘yak'are maganar cikin marairaicewa’. Dakuwa mom tamasa, “Sameer kaci kidanku, wai yaushe kama fetsare hakane ban saniba?”. Fita yayi yana dariya, ta kirashi da sauri. Kuma dawowa yayi, tace, “kasandai Doctor tace a nemi madara, naga kuma bama kada niyyar hakan”. Gaba d'aya fara'ar fuskarsa ta d'auke, yad'an shafi girarsa da d'anyatsa d'aya yana fad'in “Mom wai wace madara ga abincinsu?, ALLAH dai ai shiya haliccesu, kuma shine zai wadatasu da abincin nasu, amma kawai sai a kama wani danna musu wata madara? dan ALLAH mu ajiye zancen madarar nan ma gefe mom”. Numfashi mom ta sauke, tasan murd'ad'd'en halin Galadima da dagewa akan ra'ayinsa, cikin kwantar da murya tace, “na yarda da maganarka, amma ita za'a tausaya mawa, shayar da yara uku bafa abune mai sauk'iba Sameer, wasuma d'ayane idan suna da fargabar shayarwa kaga duksun k'are sun lalace, koda dai sau d'ayane sai a ringa basu madarar a rana, tunda ALLAH dai baya hanaka yanda zakayi bane”. Tashi Munaya tayi tana hawaye, taje ta hau gadon kawai tayi kwanciyarta, ta kula Galadima yacika son kansa, tanaga saita tuna masa da matsayin auren nasu da alfarmar yarda ta haifa masa y'ay'an dayake neman nuna mata mulki a kansu, aidai abin shayarwar a jikinta yake, sai kuma yanda taso tayi da kayanta, dolene ta takama wannan homar tasa birki. Daga Mom har Galadima da kallo suka bita, yaja guntun tsaki yana juyawa zai fita. Mom tace, “zaka siyo d'in?”. A k'ufule yace, “zan duba”. Yay ficewarsa. shifa ya lura yarinyarnan ma batason yarannan, shin bak'in ciki take ALLAH yamasa k'yautar abinda kud'i baya sayane ko me? ALLAH zaiyi maganinta kuwa. 🤣🤣ho Galadima, uwa ta ta6a k'in d'antane🤦🏻♀. ★★★★★★★★★★★★ Mama Fulani dai yau tagaza gane kanta, duk yanda taso danne zuciyarta tayi murnar koda ganin idone ta kasa, shiyyasa ko zuwa wajen tarbarsu batayiba. Takuma hana dukkanin bayinta da kuyangi shiga inda take. Abinda bata saniba idon Galadima fes yake akan dukkan Wanda ya tayashi murna da samun k'yautar ALLAH, wad'anda bama su fitoba sun shiga black lists, kuma d'aya bayan d'aya saiya kartama kowa rashin m acikinsu. ★★★★★★★★★ Innaro kuwa dai saita hau tsiya dataji labarin su Munaya kowa mijinta ya d'auketa zuwa gidanta, tahau zazzaga masifa anmata ba daidaiba, babu Wanda ya kulata, dan masu zugatan suma hassada ta ishesu, basuda kuzarin taya 6era 6ari😂.. Haka tagama jarabarta takoma gida tana huci, Abba yasha dariya, danshi lamarin mahaifiyar tasu yanzu kallon rikicin tsufa kawai yake masa, inba rikicin tsufaba miye abin tada jijiyar wuya anan? Sunada damar hana yaran komawa gidajen mazajen sune?. Shikam baba k'arami ma lokacin da take jarabar zuwa yay ya ra6a ta gefenta ya fice daga gidan. Ai lamarin innaro sai ita🤣🤦🏻♀. ****************** A 6angaren Munubiya ma Alhmdllh, dukkan wata kulawa mama rabi'a tana tsaye akan 'yarta da jikokinta, sai zuba mata gata akeyi da k'yak'yk'yawar kulawa mai ban sha'awa. Suruka ta gari dadi alkur'an💃🏻💃🏻😘😘. ★★★★★★★★★★★★ Mom dai da k'yar suka lalla6a Munaya itada Aunty Mimi ta amince ta shayar da yaran, suna sha tana kukan zafi kuma😹, sunsan zataji zafi tunda Na farkone, ga yaran a buk'ace suke dama, amma kukan datake yawuce Na zafi kad'ai, (basusan harda haushi Galadima bane😂🤭). Mom data fahimci hakan saita fara lallashin da nuna mata muhimmanci hak'uri, su maza komai zasu iyayi akan y'ay'ansu, musamman ma shi da yake tsaka da d'okinsu yanzu, karma tabari irin wad'annam abubuwan su dameta, shima yafad'ane kawai amma zai sayo madaran”. Itadai Munaya kai kawai take d'agawa amma batace uffanba, dan tagama Sanin Galadima da halinsa Na kafiyar tsiya da dagiya akan ra'ayinsa. Bayan duk sunsha sun k'oshi Aunty Mimi tace ta kwanta ta huta kafin time d'in walimar yayi. ALLAH ya taimaketa maganin yasata barci kuwa, yaran Na gefenta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92