Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 90

Chapter 90

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a hankali, “toke yanzu Yaya kenan? naga alamar auren Contract yakusa k'arewa, gashi ko rabin sadakina ban Moraba, zaki dawomin da kayanane ko yaya?”. Kai wannan Bawa ya shahara a fagen rainin wayo, nafad'a a zuciyata, a fili kuma sai nace, “nima sai'a biyani d'aukar ciki da nak'uda, da shayarwa ai, tunda babusu a yarjejeniyar auren”. Yanda nayi maganar ina yamutse fusaka da murgud'a baki saiya shagala da kallon la66anta, hannu yasaka ya tallafo fuskarta yajuyo da ita sosai inda tashi take, dukda idonta a rufe suke, “kifad'i ko nawane sai a biyaki ai, nikuma ba kud'in Dana bayar nake buk'ata ba”. Na bud'e ido baki bud'e, “to mi kake buk'ata? Naga kud'i ka bada kuma kud'i ya kamata a baka”. Cikin ta6e baki yace, “farashina ya wuce haka”. Nina bakin na ta6e nace, “Niba arhar banza bace”. Nayi maganar ina yunk'urawa da tashi zaune, da kallo ya bini, saida na ziro k'afafuna k'asa sannan nakuma fad'in “mun gama sahirinmu”. Shiru yamin tamkar bazai tankaba, harma na juyo na kallesa, idonsa a rufe suke yayi filo da hannayensa, d'auke idona nayi ina gyara rigata. Yace, “zuwa ina kenan?”. Nace, “gidanmu”. Tashi yay ya sauka daga gadon duka yana nufar wardrobe, saida ya bud'e yana kallon kayansa sannan yace, “mizai hana kibari ki k'arasa aikinki kawai saiki tafi gaba d'aya”. Na murmusa ina mik'ewa tsaye nima, na koma jikin mirror na jingina ina hard'e hannayena a k'irji, idona akansa nace, “aini nagama aikina, Dan nabaka dukkan sirrin dake raina”. Yana ciro wasu bak'ak'en wando da Riga yace, “zadai ki gamane yarinya, Abin cikin kwan bazasu gusa a kusa daniba”. “Humm” nafad'a cikin takaici, nace, “mizai hana ka yanke dukkan alak'a, Dan nima iyayena na buk'atar ganina a kusa dasu”. Murmushi yayi yana juyowa hannunsa d'auke da kayan daya za6o, kallo d'aya yamin ya janye ido, “mikikeci na baka na zuba babie, indai an gama yak'in ai zata yanke”. “nikuma bana buk'atar ganin k'arshen, in ank'i cikin sauk'i zan bud'e komai kowa ya sani”. Murmushi yay mai sauti, har fararen hak'oransa na bayyana, ya kwance igiyar rigar wankar babu kunya ko shakkar ganina, kauda idona nayi daga inda yake, yafara saka kayansa, cikeda izza yace, “wace k'arfin gwiwa gareki na samun wannan damar?”. “Court, tabbas zan maka ka a Court, sai a kar6a min ai”. “kinada abin dariya kwarai da gaske, a mutum dubbunai dasuka shaida na biya sadaki sannan na d'auka, mutum d'ayane yasan sirrin ba haka bane, bayan wannan hujjar kinada watane?”. Dariya nayi irinta tsantsar rainin hankali, harya d'ago daga d'aura belt d'in da yakeyi ya kalleni sannan ya janye, zama nayi a stool mirror, na d'ora k'afa d'aya kan d'aya ina girgizawa, “yalla6ai kenan, a tunaninka zaka iya cin bulus ne?”. Murmushi kawai yayi bai sake tankawa ba, Dan ya kula ciwon kai take Neman saka masa, ya zauna bakin gadon yana saka sock's da takalmi, yayinda Munaya taketa cika da batsewar sharetan da yayi. rigar jacket d'insa milk color ya d'ora bisa bak'ak'en kayan, komai nasa ya kasance bak'i, jacket d'ince kawai milk, ya matsa gaban mirror kusada ita yana gyara sajensa da fesa mayen turarensa. Saida ya gama dukkan uzirinsa kafin yazo gabana ya tsaya hannayesa duka zube a cikin aljihu. Dan k'yau yayi k'yau kam, amma saina kauda kai gefe ina ta6e baki, irin bakayi d'innanba. Shima bakin ya ta6e yana rankwafowa kaina har inajin hucin numfaahinsa, “karki damu mai yabawar tana nan tafe lokaci kusa, matar Sameer sarauniyarsa kinji yalla6iya”. Cikin azama na mik'e, yay saurin ja da baya, Dan daya tsaya saina buga masa kaina wlhy. Hanyar fita na nufa ina fad'in “idan kana buk'atar y'ay'anka zaka iya bina gidanmu ka kar6o abinka”. Da kallo yabi bayanta kawai yana ta6e baki, akan la66ansa yace “iya tsiwa”. Agogonsa ya d'auka bak'i ya d'aura, sannan yazuba wayoyinsa a aljihu tareda saka eyeglasses mai duhu a idonsa, ya 6oye tsananin jaa da sukayi, a falo ya iske tea a cup an had'a yanata turiri, zama yay yana lumshe idanu, yakan rasa Munaya wace irin macece ita? So salon nata akwai tsagwaron k'ayatarwa, Crossing k'afarsa yayi yana shan tea d'in a hankali, yasha kusan rabin cup ya ajiye yana mik'ewa da kallon agogonsa yanajan k'aramin tsaki. sashen Munaya ya nufa, bayin daketa gyare-gyare suka zube suna gaidashi, hannu ya d'aga musu kawai batare da yace k'ala ba, cikin takunnan nasa na k'asaita da izza yake tafiya, bayinnan sai satar kallonsa suke, da sallama ciki-ciki ya shigo d'aki, Laraba tai saurin risinawa tana gaisheni, ya amsa batareda yako kalleta ba, ficewa tayi da hanzarinta, Samha ma ta gaidashi. Zama yay a bakin gadon idonsa akan akwatina da Munaya ta had'a, ya janye ya maida kan yaran yana fad'in “ku shirya gobe zaku koma?”. Cikin d'oki Samha tace, “Uncle Sam harda Aunty gimbiya?”.. Cire glasses d'insa yayi ya maka mata wani kallon daya saka hanjin cikinta mitsawa, yace “tare kuka zone?”. Da k'yar ta had'iye yawu tana girgiza masa kai. Da yatsa ya nuna mata k'ofar fita, jiki na rawa ta ajiye Amaturrahman tafice tana tuttura baki da share kwallan shagwa6a. Ya lumahe ido yana jan tsaki, Munaya dai na zaune tana had'a wasu y'an kaya da suka rage a k'aramar bag, ko kallo basu isheta ba. Rankwafawa yay duk ya sumbaci kumatun yaran, sannan ya kalleta fuska babu alamun yasan dariya yace, “wannan kayanfa?”. Duk da na tsorata da yanayinsa, hakan bai hanani dakewa ba, cike da jan aji nace, “Na tafiya”. Uffan baice daniba ya mik'e, kansa tsaye ya nufi k'ofa, nikuma nabisa da kallo harya fice. Wasu hawaye danake rik'ewa tun lokacin dana baro d'akinsa suka samu damar zirarowa, hannu nasaka na sharesu ina zuge zip d'in bag d'in. Waya na d'auka na kira Momma, na gaisheta cikeda ladabi, albishird'in cigaban jikin Abie da aka samu ta sanarmin, tsantsar farinciki ya sake kamani, nace insha ALLAH su Samha ma zasu taho da wasu magungunan. godiya tamin da sake sakamin albarka, ta tambayeni ya mukayi dashi?. Na sanar mata yace baza'a jemai ko ina da yaraba. Murmushi tayi mai sauti har ina jiyota. “karki damu d'iyata. Da Kansa ma zai kaiku”. Na amsa mata da to kawai, Dan banga alamar Galadima zai tankwaru ta cikin sauk'iba akan tafiya wanka d'innan. *********** Tunda ya fito hadimansa keta kwasar gaisuwa damasa Yaya jiki, hannu kawai yake iya d'aga musu fuskarsa babu walwala, sarkin mota da dogaran dakan bisa yayin fita suka taso da hanzarinsu, bud'e masa mota akayi ya shiga. Saida Sarkin Mota ya tada motar sannan yace, “ranka ya dad'e ina muka nufa?”. Banza ya masa kamar bazai tankaba, sai zuwa can yad'an nisa yana bud'e ido, “mu fara Shiga wajen mai martaba”. “Angama ranka ya dad'e”. Sarkin mota ya fad'a cikeda girmamawa. Bai fita a motarba, sarkin mota ne yafita domin nema masa iso, amma sai jakadiya tace, “ai takawa tunda safe suka fita shida su Masu da baraya. Sarkin mota yazo ya sanarma Galadima, baice komaiba sai kansa daya jinjina kawai. Daga nan basu zame ko inaba sai gidanda su Muftahu suka kai yarannan. Muftahu da kansa ya bud'e musu k'ofa suka shiga, aka bud'ema Galadima ya fito, tafiya yake a nutse cikeda k'asaitar masu mulki da tashen k'uruciya, Muftahu ya tako a hanzarce garesa, hannu

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});