Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zuciya ba zai iya bashi taimakon gaggawa, shikuma Dr jalal ya fara kar6ar Abdurraheem dake hannun inno, yan d'ube-dube, yayi Na tsawon lokaci kafin ya ajiyeshi ya kar6i Na hannun mai Martaban, shima yagama duk abinda ya dace ya kar6i Amaturrahman a hannun papi, ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in “Alhmdllh duk basu mutuba, allurar barci mai k'arfi sosai suka musu, shiyyasa numfashinsu yay nisa sosai, danta musu k'arfi da yawa, amma idan kuka saka kunne nawasu mintuna saitin jikin zuciyoyinsu zakuji suna motsawa kad'an-kad'an, sai dai ta wannan tafi yin k'asa sosai gaskiya”. Ya nuna Abdurraheem dake hannun inno. Su mai Martaban suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala ga ubangiji. A cikima Akash nata iya bakin k'ok'arinsa ganin Galadima ya farfad'o, Ahaka su mai Martaban suka k'araso cikin d'akin d'auke da yaran a hannun, Munaya Na gefen Galadima an lullu6a mata bargo batasan wainar da ake toyawa ba, dan barcin nata shine mafita fiye da zama ido biyu. A gadon suma yaran duk aka shimfid'esu, Dr jalal yad'an musu dabarun likitoci sauran kuma aka barma ubangiji ikonsa Na jiran farkawarsu. Hankali kuma duk saiya koma ga Galadima da aketa fama. Har aka kirayi sallar Asubahi babu amo babu labari akan farfad'owar tasa. daga k'arshe dai Akash saida ya kira likitan Galadima na zuciya. Shiya dunga fad'ama Akash d'in yanda yadace yayi, lokacin shiga salla ya saka su mai Martaban fita masallaci dole, sukabar Akash da Dr jalal dake taimaka masa suna aikinsu, saisu Aunty Mimi da suka kasa matsawa ko nan da can, Sauban ma da k'yar su papi suka lalla6asa yabisu salla. Har gari ya waye sashen Galadima ya cika da manyan masarautar irinsu mama Fulani matan Sarki da sauransu Galadima babu wani bayani, zuwa yanzu ma wasu sun fara tunanin kodai yama mutu ana 6oyewane kawai. Wajen 8:00am Dr Yaseen Ali Modibbo babban likitan zuciya da akeji dashi ya iso, bisa kiran da Dr jalal ya masa yafad'a masa, dan abubuwan da sukaima Galadima bai farfad'oba Akash yakuma sanarma likitansa, shine yace tofa gaskiya Kodai asamo ainahin likitan zuciya ko kuma su taho dashi kafin cikar awanni 12, idan ba haka ba komai zai iya faruwa. A k'iyasin da sukayi cikin awanni 12 bazasu Isa india ba, tunda duk tsiya sai an samu jirgi mai tafiya, sannan ma kafin komai ya biyo baya. Hakkane yasaka Dr jalal kiran Dr Yaseen Ali Modibbo d'in, cikin amincin ALLAH kuma ya amsa zaizo d'in, saikuwa gashi ya iso. Canjama Galadima d'aki akayi, dukkan kayan aikin da Dr Yaseen yazo dasu aka shigo dasu, rufe d'akin sukayi suka duk'ufa su uku kansa suna taimakon Dr Yaseen d'in. Sun jigata kwarai da gaske kafin zuciyar Galadima tafara bugawa k'asa-k'asa, sai numfashinsa yafara fisga yana k'ok'arin fita. Duk ajiyar zuciya suka sauke. Suka cigaba da aikinsu, ana sakama Galadima wani abu a k'irji kamar dutsin guga, saiya girgiza sannan a cire, akuma maidawa. Basu barsa ba saida yasaki wata ajiyar zuciya mai matuk'ar sauti, harsu mai Martaban dake falo saida suka jiyosa kuwa. Wannan ne yasaka zukatan doctors d'in uku sanyaya, Dr Yaseen da Dr jalal suka had'a baki wajen fad'in “Alhamdulillah!”. Numfashin Galadima ya dawo dai-dai, amma sun masa allurar barci danya samu nutsuwa. Yaranma an kawosu ne Dr Yaseen ya kuma bincikawa, shima dai yace suna da ransu, amma Abdurraheem yanada ciwon zuciya shima, shiyyasa yafi sauran y'an uwansa jigata, ALLAH nema dai yay rabon yanada sauran numgashi, amma allurar tamasa k'arfin da zata iya dakatar da bugun zuciyarsa. Suma dai sun kuma samun taimako, musamman ma dai Abdurraheem da tausayinsa ya kama mutane da yawa a wajen. *_2:00pm_* Zuwa wannan lokacin Munubiya da mama Rabi'a da Ayusher Feena duk sunzo masarautar, Hakama baba k'arami da daddy, dan an sanar musu samo yaran da halin da galadima yake ciki. Amma saboda kara irinta Abba da innarsu Munaya sai suka bar su Baba k'arami da maman Fauziyya da mamansu yaa Hameed, maman Safara'u suka taho, sai innaro da gwaggo Safiyya. Ba'a barin wani bak'on fuska shigowa masarautar a yau, amma su sai mai Martaban yasa aka shigo dasu, basu samu ganin ko d'aya a cikin su Munaya ba, saidai Munubiya da aka shigar d'akin galadima inda Munaya ke kwance, Sauran kuma sun shiga ayarin y'an zaman jigum-jigum da jiran tsammani. Har zuwa wannan lokacin Galadima da Munaya babu Wanda ya farka, Amaturrahman da Abdurrahman dai sun farfad'o, sai dai suna kuka ko fita bayayi. Wanka laraba ta musu aka gasa musu jikinsu sosai, yau dai dole aka nemo madarar da Galadima bayason susha d'in, ita aka dama aka basu sukasha, aiko sun shata sosai dan yunwa sukeji, bayin ALLAH, rabonsu da abinci tun jiya da rana kusan I war haka d'in. Tausayinsu ya kama Munubiya dake basu madarar, tana yi tana sharar hawaye, da da farko nono inno tace ta basu, sai papi yace, “a'a kar ayi wannan gangancin, dan ba'asan abinda ALLAH zaiyiba wataran, ko akwai k'addarar aure a tsakanin yaransu, kar azo ayi Dana sani a watarar da baza'a iya maido wannan ranarba balle a gogo 6arnar da akayi”. Kowa ya gamsu da wannan magana, dan haka Muftahu yafita suka nemo madara shi da Saleem. Shine aka basu. Baiwar da aka kami da mutumin kuma suna hannun police, kuma kowa yaji cewar tana cikin bayin gidan wad'an da aka aminta dasuma sosai, saidai ba'asan ta wane sashe bace. Wannan Abu ya tsurar da zukatan Sauran bayin, dan dolene ya shafesu. Hankalin Uwargidan Sarki Sarauniya Zulfah (mahaifiyar su matawalle) a tashe yake, amma dayake ta iya takunta bazaka ta6a fahimtar haka ba, saima nuna tsantsar damuwarta akan lamarin da tayi fiye da sauran matan Sarki. dama kuma tafi nuna kulawarta ga Galadima kowa yasan wannan, shiyyasa babu Wanda yakawo wani Abu game da ita, saima wasu daban ake zargin. Munaya da Galadima sun farfad'o ne kusan time d'aya, amma Galadima ya riga Munaya, dama allurar awanni 4 kacal aka masa, da Sunan ALLAH a bakinsa ya farka, sannan yafara kiran yaransa d'aya bayan d'aya yana fad'in karsu tafi su barsa.. Rik'eshi Dr Yaseen yayi yana fad'in “ka kwantar da hankalinka ranka ya dad'e, dan zuciyarka tana cikin yanayin jiran k'iris ne, inamaka albishir da cewar yaranka suna raye, yanzu nan zakagansu insha ALLAH”.. Galadima ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kallon Dr Yaseen, ya lumshe idonsa a hankali sannan ya bud'e, hanunsa ya d'ora akan saitin zuciyarsa saboda wajen yamasa matuk'ar nauyi. Ana haka Dr jalal ya shigo d'auke da yaran biyu, dan Abdurraheem shi yanan a d'akin kusa dashi bai farfad'o ba. Tunda Galadima yaga yaran sa suna a raye saiya kuma rungumesu a k'irjinsa da Dr jalal ya d'ora masa, wasu hawaye masu zafi suka gangara gefen kunnensa. Dr Yaseen yaji dad'in kukan da Galadima d'in yakeyi, dan zai rage masa rad'ad'in da yakeji da nauyin zuciyar, hakan ya nuna aikinsu zaiyi k'yau insha ALLAH. Galadima ya dad'e rungume da yaran, saidaga baya ya farga babu guda d'aya. A hankali ya bud'e baki yana fad'in, “ina d'ayan?”. Murmushi Dr Yaseen yayi, yace, “gashi a gefenka yana barci shima”. Juyawa Galadima yay ya kallesa, ganin d'an cikin yaron Na motsi alamar fitar numfaahi sai dad'i ya kuma ratsashi, ya lumshe idonsa yana yun k'urawa zai tashi zaune, taimaka masa. Dr

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});