Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

addabarsa da kallo, shi saiya rasama mi suke kallon? Shidai bayasha banban da sauran halitta bane, bakuma za'a kallesa ace ba bak'in fata bane, bakuma wasu kayan ado na musamman ya sakaba, hasalima k'yank'yamin kayan jikinsa yakeyi, dan sun kwana suna Neman yini a jikinsa, (tunda ba time d'inmu d'aya da India ba) yaja guntun tsaki yana k'arasawa ciki ya mik'ama Muftahu wayarsa. *********** Sai bayan isha'i su mom suka iso, dan basu sami jirgi da wuri ba, a lokacin jama'ar gidansu Munaya suna asibitin, masu kukan zuci nayi masu murna da gaskiya nayi, hakama a wasu daga masarauta suna nan, wasu lek'en asiri kawai aka turosu, wasu ko na taya farincikine da tabbatarwa. Yau dai yan gidansu Munaya suna kallon abin mamaki, da gaske dai inna Ai'sha tamusu fintinkau irinna jirgi, saidai hange daga nesa da harara cikin duhu. Mom bakinta yak'i rufuwa, harda rungume Galadima, Nuren kuwa hardasu taka rawa🤣, Muftahu na masa lik'i. Mutane abin ya birgesu, Galadima yay murmushi yana d'an dukan kafad'ar Nuren da Muftahu kawai. Su Munubiya basu farkaba har sannan, doctors sunce babu wata Matsala, a barsu su huta sosai yanda zasu tashi da kwarinsu zuwa Safiya. Dole dai Galadima yasa aka zuba police a asibitinan ranar, sauran kuma anbarma UBANGINJIN TALIKAI dake kallon motsin kowa. Masu tafiya duk suka tafi, aka bar masu kwana kawai. Galadima da ya dage anan zai kwana shima, da k'yar dai mom ta lalla6ashi ya tafi gida kodan yasamu yad'an huta, kallo d'aya zaka masa ka gane a matuk'ar gajiye yake, jijiyoyin Kansa sunyi rad'a-rad'a, ga yunwa waddama ya manta da ita da alama. Wannan dare dai ya kwana rayashi da bautar ALLAH ne da godiya mai yawan gaske. Innarsu Munaya ma dai kuka sosai tasha na dad'i, itama haka ta raya wannan dare, hakama Abba, shima yamik'a godiyarsa ga ALLAH dan lokacin dayake buri da tanadi ya cika, koba komai zai sauke nauyin dake rataye a wuyansa insha ALLAH. Washe gari...............🤩✍🏻 *_media ko bala'i, kayi turanci a novel ace ka cika iyayi da son asan ka iya turanci🤦🏻‍♀, muda muke koyo muyi ace bamusan abinda mukeba🤦🏻‍♀, kai jama'a babu mai iyama 'yan social media sai ALLAH, ko uwarka ka yanka kagasa tasha mai kwallan tana d'iga, da wani yagama ci zaice bataji gishiri ba🙄, ALLAH ya shiryar damu muda bakunanmu dai.🙏🏼._* _Ayshan sadiq sak'onki ya iso gareni, nakuma gode kwarai da gaske, saidai ina mai baki hak'uri da sauran fans d'ina, a gaskiya weekend d'inan ina muhimman abubuwane a cikinsa, bazan iya alk'awarin typing ba, sannan ni kaina idanuna 👁👁da Brain 🧠 d'ina suna buk'atar hutu, inada aure, akwai wasu hak'k'oki a kaina bana typing kawai ba, kunga yadace suma na basu lokacina, dan Ku gamsu nake zaman yin typing mai tsawo, insha ALLAH idan mukai hak'uri kamar yaune raina kama zaizo k'arshe abarma yayinsa Ku manta dashi saikuma wasu dazasu 6ullo daga sauran writers namu, dan haka muringa hak'uri da abinda ALLAH ya k'addara namu a lokacin da ya tsara, kar muyi gaggawa domin aikin shaid'ance, nima Ku duba nawa buk'atun amatsayina na mutum kuma mace mai rataye da igiyar auren. Ina godiya kwarai da gaske da k'aunar da kuke nunama wannan buk, bammasan yanda zan nuna muku farincikina ba kusan inajin dad'in Comments naku nima, amma ina sonku irin sosai d'inan a raina, kumuje zuwa guys, duk Nisan jifa k'asa zai fad'o👎🏻_ I love you mazga-mazga all.😘😘🥰🥰😍😍😍🤝🏻. Ayshan sadiq, ina miki fatan alkairi a duk Inda kike😘😘😘😅🤝🏻. *_ALLAH ka gafarma iyayenmu_*🙏🏼😭 [7/11, 1:10 PM] Aysha Galadima: [7/9, 11:05 AM] ❤y'ar K'asa❤: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻2⃣3⃣ ...............Koda Muftahu ya sauke Galadima saiya sake shiri Yakoma asibitin, tunda ya shigo idon Nuren a kansa, sai mamaki ya kamasa, shin miya maido Muftahu asibitin? bayan kuma tare suka tafi da Galadima. Bai masa maganaba dan karma yasan ya gansa, saiya saka ido a dukkan wani motsin Muftahu d'in, shidai Muftahu baisan yanayiba, dan baima je d'akinda su Munaya sukeba, sai zagaye-zagaye dayaketa famanyi har ALLAH ya wayi gari lafiya. Wannan lamarifa ya zaune a zuciyar Nuren yanata kaikawo, anya kuwa ba suna zargine akan abinda ba haka yakeba?, dukda jami'an tsaro dake wajen Muftahu Nada damar aiwatar dadukkan abinda yay k'uduri tunda kowa namasa kallon makusancin Galadima, amma har ALLAH ya wayi gari baimayi wani yunk'uri na shiga d'akinba balle alamun rashin gaskiya, saima aikinsa dayay kama dana mai k'ok'arin bama wani abu kariya, “ya ALLAH ka warware wannan lamari cikin sauk'i kodan wannan bawa naka yasamu nutsuwa shima”. Nuren ya fad'a a fili yana d'aga hannayensa sama alamar rok'o. Muftahu dake kallonsa yay murmushi yana amsawa da amin a la66ansa, daga nan yafice abinsa ya koma masarauta, saboda anata kiraye-kirayen sallar asubahi **************** Misalin 7:30am Munaya ta farka, kamar a kunnen Munubiya itama saita farka, su mom dake d'akin suka shiga musu sannu, cikin tsantsar farin cikin farkawar tasu, dandanan aka kira doctor. Alhmdllh babu wata matsala a tattare dasu, aka kikkimtsasu dagasu har yaran daketa barci irinna jinjirai, daga Munu... Har munaya dai kallon y'ay'a biyar sukeyi, amma tunaninsu ko cikin y'ay'an y'an uwansune. Doctor Farida data lura da hakan tayi murmushi kawai. umarni tabama Nurses d'in abama kowa nata, kallon kallo akeyi tsakanin Munaya da Munubiya, amma kowa bakinsa yagaza furta komi, saisu kalli juna sukuma kalli jariran gabansu. Doctor Farida dai dataga basuda niyyar d'aukar yaran tace “y'an biyu wannan itace k'yautar da ALLAH ya baku, Munubiya 2, Munaya 3. Duk waro ido sukayi, Dan Na Munaya ne yabasu mamaki, tunda dukansu sunsan Na Munubiya dama. Munubiya ta sakko daga gadonta batareda ta d'auki ko d'a d'aya anata ba, gadon Munaya ta nufo, ta durk'usa k'asa tana rungumo yaran, ga hawaye ga dariya tanayi, saikace sokuwa. Munaya ma dai batabi takan nata d'inba, saita nufi Na Munubiya ta d'auka duk ta sakasu a jikinta, k'aunarsu Na ratsa dukkan 6argonta kamar yanda take k'aunar mahaifiyarsu. Galadima da Yaa marwan dake tsaye a bakin k'ofa suka kalli juna suna murmushi, kowanne yana mamaki a ransa, anacewa y'an biyu akwai shak'uwa, sukam suna mamakin ta wad'annan Matan nasu, soyayyar dake tsakaninsu tanada ban mamaki da birgewa. Galadima ya k'arasa ga Munaya da har yanzu take a tsaye idonta arufe y'an biyun Munubiya na jikinta, had'ata yay itada yaran ya rungume. A firgice tabud'e ido, saitaji k'amshin turarensa, tayi baya kad'an yay saurin ruk'ota. Idonsa ya saka cikin nata yana wani murmushin dabata ta6a ganiba daga garesa. Ahankali ya furta haba “Maman y'an biyar a hankali mana”. K'aramar harara ta sakar masa, ya saka k'aramar dariyar da tadawo da Yaa marwan daga duniyar daya tafi😳, danshifa mutunmin naku har yana Neman sakin layi🤭🥳. Mom dake bayansu tayi gyaran murya, kowa saiyaja baya daga jikin matarsa🤣, suna wani susar k'eya. Munubiya da Munaya sai suka koma kusa da juna, Munaya ta kama hannun Munubiya a cikin nata. ita mom dariyama suka bata, Dan haka tad'an dara tana fad'in “An sallamemu to yanzu ya za'ayi?”. Munubiya da Munaya suka kalli juna, da alama dai basa buk'atar rabuwa, sudai su Galadima kallonsu suke kawai. Ganinfa zasuyi daru sai mom tai murmushi, da ido taima Galadima da Yaa marwan magana akan su fita. Babu musu suka fice, itakuma takama hannun

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});