Chapter 84
Chapter 84
Dagacan Momma ta murmusa tana gyara zama a harabar asibitin, dan batason Abie yaji wayar da zatayi, tace, “humm d'iyata kema 6oyemin zakiyi kenan? yanzu koda mutuwa yaran sukayi dashi kansa kowama saiya shiga fargabar gayamin?”. Na had'iye yawu dak'yar, “kiyi hak'uri Momma, ki gafarcemu”. “Bakumin laifin komaiba ni, hakan da Muh'd yay shine dai-dai, dan lokaci yayi dazai daina zama jiran sak'on mak'iya ko zuwansu, shine yakamata ya fita farautarsu domin kawo k'arshen komai, na yarda dake 100% Munaya, nakumayi imani insha ALLAH kece zaki sauyamin yaro daga k'uncin dayake ciki zuwa farin ciki, tamkar yanda Na fad'a miki tun farko karki ta6ama Muh'd sanya ko nuna tsoronsa, lokacin dazaki kwantar masa dakai kizama kowacce irin mace a agidan mijinta har yanzu baiyiba, kada ciwonsa yasakaki fargabar fad'a masa gaskiya, rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne, ko ayanzu Muh'd yabar duniya bazanyi bak'in cikiba, domin ya nuna musu shi jarumine, kuma ya haifi wad'anda zasu iya zama magadansa su sauya komai koda ba'aso, nanda kwanaki biyu komai ya gama lafawa ki tabbatar kin masa maganar tafiya wanka gida, wannan shine target d'inmu Na k'arshe akan rayuwar zaman aure na dindin, kowacce irin birkicewa zai miki akan bazaki jeba, kema ki birkice masa, dan nasan abinda yafaru zaisashi dagewa akan yaran bazasuyi nesa dashiba, idan kuma har aka cigaba da tafiya a haka, kowane irin dana Sani zai iya biyo baya”. Momma ta share hawaye dake kwarara a idanunta, taci gaba da fad'in “ALLAH yayi miki albarka Munaya, dake da abinda kika haifa, yanda kikamin biyya wajen k'autata kar6ar Abu mai wahala (duk da bani na haifekiba) kema ALLAH yasa y'ay'anki sumiki biyyaya fiye da wannan, ALLAH yasaka hannu adukkan lamarinki keda mijinki da sauran y'an uwansa, nusar dashi abinda duk baki gamsu dashiba shine zai rage ma zuciyarsa baraza, dan tarawar yagani a lokaci d'aya shine mafi had'ari Munaya, zuciyarsa zata iya bugawa a lokacin, kiyi hak'uri nasan bak'yajin dad'in zama da Muh'd ko kad'an, domin ni kaina mahaifiyarsa wataran gaza gane kansa nakeyi, amma inaji a jikina akwai sauyi maiban mamaki dazai zo ya rusa komai, ki sameshi fiyema da yanda kikeso, ALLAH yayi muku albarka, idan ya tashi ki kirani naji ya jikin nasa”. Bata jira nayi magana ba ta yanke wayar, da alama kukane yaci k'arfinta. nima saina fashe da kukan ina kallon Galadima, insha ALLAH zan cikama baiwar ALLAHr nan burinta, koda ace mun rabu dashine, dan maganar gaskiya bazan iya rayuwa da mutum murd'ad'd'e mara yarda irin Galadima ba, labarinsa kawai kukeji, amma halinsa saika zuna dashi, Mara hak'uri zai iya gundurarsa ne cikin awanni biyu kawai, dan zaka dinga kallonsa a matsayin mai wulak'anci ko dizgi, girmankai da sauransu. Na sauke ajiyar zuciyarsa ina maida kallona ga Abdurrahman dake motsin tashi, nasan dukansu saisun tashi inhar d'aya ya tashi, saina lalla6a na kwanta kusa dashi na saka masa nono a baki. ******************** Har akayi la'asar Galadima bai farkaba, Nuren yazo shida Sauban, da Saleem har sau biyu suka iske yana barci, hakama Mom da inno da mama Fulani. Gashi su inno 4:30pm zasu wuce ma, laraba tazo tama yaran wanka, dan tuni sun farka, Nima nakumayi sannan naci abinci, kaina ciwo yakemin sosai, dan haka Sauban yafita ya samomin Magani nasha na kwanta, munyi sallama dasu Mom, zasu dawone kawai idan Galadima ya farka kafin su tafi. yaran kam duk d'insu suna can an kaima papi su tun d'azun. Nidai barci yay awon gaba dani, daga nankuma bansan wainar da aka cigaba da toyawa ba a gidan. ******************* Bayan la'asar kad'an Galadima ya farka, ganin shi kad'aine a d'akin ya tashi zaune bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci, jin k'irjinsa yayi sakayau yasaki babu nauyin kamar d'azun, saidai abinda ba'a rasaba, yatashi zuwa bathroom yay wanka da alwala. Sallan zuhur da la'asar ya rama, tareda addu'ar neman sauk'i akan wannan lamari da samun k'arfin zuciya, dolene saiyayi yak'i da dukkan abinda zai zama makamin barazana a agaresa inhar da gaske aikin zaiyi, falo ya fito bayan ya kimtsa, zamansa da mintuna baifi 2 ba saigasu inno. Basu jira isoba suka shigo, a zatonsu yana bedroom yana barci, sunsan Munaya kuma tana d'akinta tana barci tunda daga can suke. ganinsa a zaune ya saka fuskar kowannensu fad'ad'a da murmushi. Shidai kallonsu kawai yake d'ai-d'ai. Inno ta mangari kansa tana fad'in “ja'iri baka sanmu bane halan?”. Hannunta ya rik'e yana kallonta, cikin maganarnan tasa ta k'asaita yace, “Inno wai ina zakuje ne?”. “inda muka fito mana”. Inno tafad'a tana zama kujerar kusa dashi. “saikace wad'anda ake kora?”. “A'a wazai koremu nida gidanmu, komawar dai ne yafi cancanta, dan takawa ma yace a gaisheka basai ya shigoba, zakuyi waya, idan ka murmure kaje yana nemanka”. “To shikenan ALLAH ya tsare hanya, mun gode sosai da sosai”. “Amin” inno tafad'a tana shafa kansa ta ciga da kwararo masa addu'oi shida matarsa da yaransu, falon kowa tana amsawa da amin, itama mom tayi nata. Yace, “mom hada ke wai?”. “eh mana Sameer, zaman mi zanyi to? tunda ALLAH ya iyakance komai cikin sauk'i, nanda y'an kwanaki kuma basai na zagayo naga masu jego ba da jikin naka, a dai dunga kulawa sosai, gasu laraba nan da bayi 2 anbar muku, dukdai wata kulawa insha ALLAH zasu taimaka wajen badata akan yaran, dan yakamata dukkan bayi da kuyangin sashen nan naka ka sallamesu kawai”. Kansa ya jinjina mata alamar amsawa. A gurguje sukad'an kuma tattaunawa da kwantar masa da hankali suka fito, dukda yaso musu rakkiya suka dakatar dashi. Abincin da mom ta zuba masa takumace yamata alk'awarin zaici ya dage yaci sosai, sannan Sauban daya dawo rakkiyarsu d'auke da y'an uku shida bayinnan biyu yabashi magani yasha, kar6ar Amaturrahman yayi, Sauban kuma na zaune dasu Abdurraheem yana musu wasa wai dole sai sunyi dariya, (nace, “aiki jaa kenan, inba dariyar k'udaba ta jarirai idan suna barci keyi aiko ka dad'e baka ganiba Uncle triplets😂). Galadima ma madai yatsansa d'aya ya saka cikin hannun Amaturrahman yana wasa dashi, dukda idonsa a lumshe yake ya jingina kansa da kujera, maganganun Munaya na d'azun kawai yake nazari dalla-dalla. Ana cikin haka Samha tayi Knocking, Sauban yace ta shigo, saida ta gaida Galadima damasa ya jiki. Ya amsa mata batareda ya kalleta ba, tareda tambayarta Khaleel fa?. Tace, “yana 6angaren Ummu hasheem”. Baice komaiba, itama ta k'araso ta d'auki Ammaurrahman data rik'e yatsansa gam tak'i saki.. d'agowa Galadima yay yana kallon yarinyar, Samha dai dariya takeyi, har Sauban shima ya farga da abinda ke faruwa ya shiga tayata. Galadima ya zare yatsansa yana murmuahin gefen baki da lakatar hancin Amaturrahman. Har Magriba suna nan sun shashance akan yaran, yayinda Galadima ke zaune yanata cud'awa da tantancewa, lokaci-lokaci yakan kallesu dagasu har yaran. Tunda ya tambayesu Munaya sukace tasha Magani tana barci bai sake tambaya ba. ******** Ban tashiba saida suka fara kuka, a time d'in har magrib tama wuce, nagama shayar dasu na lek'a Galadima, na iske doctor jalal tareda Dr Yaseen da Akash Wanda yake shirin komawa gobe, sai Muftahu da Nuren. Muka gaisa dasu suka kuma tambayata jikinsa? na Amsa musu da Alhmdllh. fitowa nayi na barsu, da aka kawo mana abinci ma can nace akai musu, Sauban yazo ya kwashi yaran bisa Umarnin Galadima, doctors zasu kuma duba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92