Chapter 15
Chapter 15
“to sannu yalla6iya”. Ba Munaya ba har Sauban saida yayi dariya da wannan suna, daganan motar ta d'auki shiru, har suka Isa masarautar. Muftahu dake binsu abaya ya sauke ajiyar zuciya, sannan shima ya shigo masarautar, tunda Galadima ya fito daga sashensa akan idonsane, Dan haka yay saurin bin bayansa da mota shima Dan yaga inda zaije. (Humm Muftahu😏). Sosai Munaya kejin barci da farinciki, yau gata tadawo k'asarta ta haihuwa, sun shiga sashen komai need tagansa, sai k'amshi dake tashi kamar kullum. d'akinta ta shige, Sauban da Galadima suka nufi nasa. Sauban ya zube a kujera yana kiran “wash!”. Galadima ya d'an hararesa, “amma idan yawonkane aibaka gajiya”. “yaya wlhy bazaka ganeba, nidai kawai bani wajen kwana na kwanta wlhy”. “Saidai ka kwana anan falo kuwa, kafin da safe a gyara sashenku ka koma can”. 6ata fuska Sauban yayi, “haba Yaya da gatana na kwana saman kujera, kadai katafi d'akin Aunty gimbiya ka kwana gaskiya kabani gadonka”. Galadima zaiyi magana Sauban yatashi da gudu ya shige bedroom d'insa ya saka key. Da sauri Galadima yace, “zan 6ata maka rai fa Sauban”. Ina, baima sauraresa ba, dafe kai Galadima yayi kawai, wlhy baisan lokacin da Sauban yafara rainashiba, kodan yaga tsawonsu kusan d'aya yanzu?. babu yanda ya iya dole yafita zuwa d'akin Munaya🤫.................✍🏼 Ho Sauban aikinka yay k'yau🤣, su Galadima dole a tafi😝, ba ruwana karya jini🤭⛹🏻♀ Readers kuma kuyi dariya a hankali fa🤫😝. Barkanku da juma'a🙋🏻. Musha weekend lafiya sisters😁🙋🏻⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀. *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_* [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ~Book 2~ 👉🏻6⃣ ............Har ya fita ya dawo, laptop da wasu takardu ya d'auka a falonsa ya fita, zai zauna a falonta saikuma wata dabara ta fad'o masa, bedroom d'inta ya nufa yana wani ciccijewa (kaida zaka karoro, miye na fuska to yalla6ai?🤔😂). Munaya Na tsaye tana ninke hijjab d'in data rama sallolin dasuka risketa a hanya sai kawai shigowarsa tagani da sallama ciki-ciki. k'ok'arin warware hijjabin tafarayi tana masifa ita kad'ai a zuciya, haka kawai aita shigoma mutum d'aki babu izini, wannan wane irin rayuwane. Shikam Galadima kallo d'aya yamata ya d'auke kansa, Dan daga ita sai zani d'aurin k'irji. Laptop d'in hannunsa da takardu ya ajiye a bakin gadon, sannan shima ya zauna, batare da ya kuma kalllon Munaya ba yace, “kinajin yunwa ne?”. Ba yunwar takeji ba, amma dan Neman magana kawai tace “eh”. Kallonta ya sakeyi, bata yarda sun had'a idoba, yace “Saidai kisha fresh milk kuwa, dan bani da abinci”. Manyan idanunta ta waro masa waje, kamar wadda akace tasha wuta, cikin dafe k'irji tace “yalla6ai fresh milk?”. Da mamaki ya kalleta, danshi bai fahimci ma'anar razanar tataba, yace, “uhmmm”.... “Na yafe wlhy”. Tafad'a da saurinta. “To mine nawani birkicewa haka? fresh milk d'in wani abune dashi?”. “Humm”. Munaya tafad'a tana ta6e baki, tace “yalla6ai nikam idan kaga nasha fresh milk d'in data fito daga d'akinka saidai idan bana a hayyacina”. Da tsantsar mamakin furucinta yake kallonta, da yake basuda nisa saiya mik'a hannu ya rik'o nata, zatayi magana ya fizgota ta zauna kusadashi, kad'an ya rage ta hau masa laptop, amma yay saurin janyewa da d'ayan hannunsa. “wash hannuna”. Munaya tafad'a tana matse baki. Banza yamata, yakuma matsa hannun da mugunta. tasaki k'aramar k'ara tana fad'awa gefen kafad'arsa. Ya d'an kalleta ya janye yana ta6e baki “ban fahimci zancenki daga nesa ba, maimaitamin”.. Cikin tunzuro masa baki tace, “yoni babu abinda nake nufi fa, nidai bazan sha fresh milk d'in data fito daga d'akinka ba wlhy. haka kawai aje asakama mutum abinda zai halakashi”. ‘k'asa-k'asa ta k'arasa maganar, amma yajita sarai’. Shifa saima yanzu yagane inda zancenta ya nufa, wani miskilin murmushi yasaki yana danne dariyarsa datake shirin kufcewa, amma dukda haka saida taji sautin fitar murmushin nasa. Munaya dake satar kallonsa idonta harya cika da kwalla, a zuciyarta tace mugu d'an masa, dole fa kamin dariya. Saida yayi dariyarsa a zuciya ya gama ya kalleta, itakuma saiwani mar-mar takeyi da idanu wai zatayi kuka. Murmushi ya kumayi, sannan yace, “wannan bakin dakike tunzuromin ko, hummm.....”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi’. Yunk'urawa tayi zata mik'e, tace, “yalla6ai ni wlhy barci nakeji fa”. Dawo da ita yayi ta fad'o jikinsa shima yana fad'in “nikuma gadinki zanyi ko? yalla6iya!”. Tace “wayyo innarmu kice ya fitarmin a d'aki please”. “ko waya zan baki ki kiratane”. ‘yay maganar cikin d'age gira d'aya’. Munaya tai saurin janye idanunta daga Kansa ga k'amshin turarensa ya gallabeta, barci takeji, amma takula mugunnan soyake ya hanata ma. Kamar zatayi kuka tace, “yalla6ai wai mikazo nemane please? Wlhy barci na keson yi?”. Shiru yamata, saida ya mula dan kansa sannan yace “jikina fa”. ‘yay maganar yana kallon k'ugunta’. Da sauri Munaya ta sauka daga jikinsa tana k'unk'uni da tura baki. Medical glasses d'insa ya d'auka ya saka, tareda cigaba da aikinsa a laptop, a zuciyarsa yana fad'in yarinyarnan akwai ruwan tsiwa, amma duk randa Na kama bakin tsiwarcan sai yamin bayani dalla-dalla kuwa. Ganin ya shareni ya cigaba da sabgarsa a System, nima sai ban kuma bi ta kansa ba Na d'auki kayan barcina nashiga bayi domin Na sanya. Sai dai zuciyata cike take da fargabar miya kawoshi d'akina?. haka na fito kamar wata munafuka ina lallak'ewa jikin bango. Duk yana kallona ta gefen idanu, amma yay kamar baima San dani a d'akinba. Sai zuwa can ya d'ago yana kallona, yana wasa da pen d'in hannunsa kan la66ansa, “idan bak'yajin barci zokimin wani d'an aiki nan”. Saida gabana ya fad'i, a raina nace aikin mi kuma?, a fili saina aro jarumta na yafama kaina, Dan nakula tsoron daya fara gani a idona ne yake neman fara rainani da samin fargaba (🤣ho munayan shagali). Takowa nayi inda yake, ina niyar zama bakin gadon sai ya nunamin tsakiyar gadon, shima laptop d'in ya tura sosai kan gadon ya haye tsakkiya yana gyara zamansa. kuma had'e fuska nayi ina wani dojewa na hau nima na zauna, cigaba yayi da danna laptop d'in, kusan mintuna 3 ya jehomin tambaya. “shin kinsan minene aikin Abba?”. Da mamaki na kallesa, nace “wai Abbana kake magana?”. “uhmm”. ‘yafad'a batare da ya d'agoba’. Shiru nayi alamar tunani, harya d'ago ya kalleni bance komaiba, maida kansa yayi ga laptop d'in yacigaba da aikinsa, zuwa can nace, “ma'aikacin gwamnati ne kawai tawani fanin kuma aikinsa yanada Nasaba da jarida”. Tunda nafara magana ya tsuramin idanu, bakina kawai yake kallo yana taune lips nashi, saida nakai aya sannan yace, “jarida?”. Nace, “eh, wani abune ya faru?”. Kansa ya girgizamin, “innalillahi” yashiga maimaitawa a zuciyarsa, baya fatan zarginsa yazama gaskiya, cikin dakiya yakuma cemin “kokin san abokansa? ina nufin cikin manyan mutane haka?”. “eh to, akwai senator halluru garba, sai kuma wani anacemasa Alhaji Mamman k'afur, last year yafito takarar shugaban k'asa......” Caraf ya kama hannuna, “kina nufin Alhaji Mamman k'afur abokin Abban kune?”. Ni tsoroma yabani, yanda yay maganar cikin rawar jiki, na jinjina masa kaina a hankali. Gani nai ya taune lips nashi da masifar k'arfi, ya kaima iska naushi. da sauri na matsa baya Dan karya nausheni, ganin kamar na tsorata sai yay murmushi, cikin k'asaitacciyar muryar nan tasa yace “my Friend! Yanzu ne zamu fara aiki tare da gaske ni da ke”. “kamar ya yalla6ai? wane irin aiki kuma?”.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92