Chapter 83
Chapter 83
damuwar rashin amsawar tasaba a fuskar Harun, dan yariga ya saba da halinsa. Saidai idonsa k'uri akan Abdurraheem dake cinyar Galadima d'in yana barci, mik'ewa yay yana fad'in, “my son zo mu gaisa ko?”. Ganin haka nima nayi azamar mik'ewa nakai ga Galadima kafin shi ya isa, na d'auke Abdurraheem d'in ina fad'in “ai barcima yake ranka ya dad'e”. Ba Harun ba hatta da Galadima saida yaymin kallon mamaki, nakoyi cid'in-cid'in da fuska yandama bazaice nabama Harun d'inba. Baki ya bud'e kamar zaice wani Abu saikuma yay shiru yana kauda kansa daga kallona, nima saina ta6e baki ina barin falon da harar Harun ta gefen ido. Gaban Harun ya fad'i, mi yarinyarnan take nufi?...... Kafin ya lalubo amsar ya tsinkayi maganar galadima yana cewa, “sorry Harun, kasan har yanzu a tsorace take, duk wani motsinsu akan idontane”. Murmushin basarwa harun yayi, yace, “ai dolene hakan ranka ya dad'e, abinne akwai tsoratarwa, wlhy jiya tashin hankalinnan ne yasaka azababben ciwon kai rufeni, shiyyasa ko ganina ba'ayiba, yanzu police d'in ina suka samosu?”. “humm” Galadima ya fad'a cikin tsananin taune lips da k'unar zuciya, ya bud'e baki a hankali zaiyi magana nida ke bayansu basu saniba nai saurin tareshi da fad'in “a hannun wasu munafukaine ranka ya dad'e, ai koni daza'a bani baiwar nan da aka kama da yaran wlhy saina tsoma kanta cikin drum d'in ruwa harsaita daina Numfashi zan barta, kafin sannan kuma nagamajin labarin Wanda ya sakata, amma shi my boss ai a station suka zauna har aka kawo yaran, badasu akaje farautarba”. Tsuramin ido Galadima yayi cikin tsagwaron mamaki, miyasa to zanzo na kasa na tsare dukkan wani motsin Harun d'in? ya kula satar yaran tana Neman ta6a tunaninta takasa banbance Wanda zata zarga, ai Harun yawuce ya 6oye masa wani sirri na sashen rayuwarsa, tun da babu abinda bai saniba na baya, saidai abinda ba'a rasaba kam, danne ransa yayi ya nuna hakane, yabari har Harun d'in ya tafi sannan yaji dalilinta. Ina kallon Sassanyar ajiyar zuciya da Harun ya sauke a 6oye, sannan yace, “ai police d'in sun cancanci Babar k'yauta, shiyyasama na shirya musu ita, sunyi aiki irinnan jaruman masu tsaro”. “hakane wlhy ranka ya dad'e ”. Na fad'a cikin murmushi. Dukfa yanda Harun yaso bugar cikin Galadima yaji yanda abun yake, na kafa na tsare, dayayi tambaya nike bashi amsa, saiya d'auka kodan Galadima bashida lafiyarne shiyyasa bai iya amsawa, tun da tunda ya shigo baice k'ala ba, kuma yasan yanayin ciwonsa, a baya ma shikan bashi taimako, baidai tsinci komai ba yay mana sallama ya fita, da k'udirin anjima ma zai dawo ne. A sace na raka bayansa da harara, sannan na kalli Galadima na basar, dukda kallon tuhuma dayake jifana dashi kuwa. Wani farfesun na sake zuba masa na mik'a masa. Batare da ya kar6aba cikin k'ank'ance idon bala'i yace, “mikikayi haka? kinsan waye Harun a wajena?”. Kaina na girgiza masa. Yaja tagwayen tsaki yana hararata, “halan satar yaranki yafara shafar tunaninki ne? kina tunanin akwai abinda Harun zai iya gazaji daga sirrina?”. Na d'an ta6e baki ina jawo teble d'in gabansa, na d'ora bowl d'in dana zuba farfesun, baki ya bud'e kamar zaiyi magana saikuma yay shiru. nima bance uffanba na ajiye masa sannan na koma k'asa Na zauna na zuba sabon kunu nahau sha. Kwafa yayi, yace, kinma maidani d'an iska ko?”. “Hummm” na fad'a kawai, naimasa kallo d'aya “yalla6ai wani karatun akan barsane a yanda yazo, sai idan lokacin fasaarashi yayi amasa fashin bak'i, nasan darajar alak'ata dakai batakai koda rabin tsakaninka da Harun ba, domin ni alak'ar wucin gadice ta had'amu, k'iris ma ya rage ta k'are, saidai inason nabama y'ay'ana kamar yanda ka fad'a kariya koda sau d'ayane a rayuwarsu kafin na barsu, dan haka maida wuk'arka a kube, lokacin zareta baiyiba, sometimes kalmar Mahangi da mai hange takanyi kamanceceniya, dan bakowa ke iya rarrabata wajen fasaara ba, amma kalmomine duka masu harshen damo, wani k'alubalen saida tunanin mai zurfi, wata k'oramar ruwan mutanen dake zagaye da ita sukanyi imani bazata balle harta cisu ba, saboda sun yarda sud'in masuntane da kullum suke rayuwa cikin wannan k'oramar, abin mamaki saikaga wataran an wayi gari da mutanen da muhalansu duk wannan ruwan ya had'iyesu, abinda basu ganeba bakowacce irin alak'a bace ake kulla amana da ita, wani farin idan yashiga cikin fari banbance k'arkonsa saidai ALLAH”. Tashi nayi nai shigewata bedroom d'insa. A fusace shima ya mik'e zai bini, kad'an yarage ya zubda farfesun dana ajiye masa, ALLAH dai ya kiyaye ya shallakesa ya wuce. Hucin mutum kawai naji a bayana, hakan yasani waigowa da sauri, hannu ya dunk'ule zai kaimin naushi, nai azamar fad'awa saman gadon ina zaro ido waje, a lallai Abu ya girmama, nikuma miye nawa da zai sauke fushinsa a kaina? nai maganar a zuciyata. Janye hannunsa yayi yana ciza lips d'in sa da k'arfi, idonsa dukya kuma rinewa, ya dunk'ule hannun ya daki d'ayan dashi, muryarsa har rawa take yace, “Miyasa zaki kuma hargitsan tunani ne? Minene laifin Harun shikuma? kuna nufin duk Wanda na yarda dashi shine mak'iyina? Kai impossible wlhy, Munaya wakikema aiki a kaina? ya rankwafo kaina, kaikace cinyeni d'anya zaiyi, saikace zaki yaga bandar nama, da k'arfi yace, “bazaki sanarmin ba saina k'arar da numfashinki ne waishin Ubanwa ke fad'a miki wad'annan maganganun da kike d'aureni dasu a ko yaushe?!!!”. Ya k'are maganar cikin tsananin tsawa da k'araji. Ba k'aramin firgita nayiba, badan karnayi k'arya ba danace har wutar bala'i Nagano a idonsa tana ci, wannan bawa akwai zuciyar tsiya, idan zai zama jami'in tsaro da k'asarmu ta amfanu da yawa......... Da k'arfi ya girgizani, saboda ganin saboda rainin wayo tunanima na tafi.......... A firgice nace “yi hak'uri zauna zan fad'a maka”. na fad'i hakanne dan kawai ina ganin itace mafitar dazan nema ya fasa had'iyeni. a mamakina kuwa saiya tashin ya zauna yana dafe k'irji hawaye nabin kumatunsa. Tsantsar tausayinsa ce ta kamani, na tashi na d'akko ruwa na dawo kusa dashi na zauna, addu'oi na shiga tofawa a ruwan, yana zaune dafe da kansa, da alama kuka ma yakeyi, dan ajiyar zuciyar da yakeyi ta yawaita. Saida na gama na dafa ka fad'arsa, tamkar bazai d'agoba saikuma ya kalleni, ruwan addu'ar na basa, babu musu ya kar6a ya shanye, duk da baima san mita bashiba, idanma poison ne dai gara ma yasha ya mutu ya huta. Mintunansa biyu zuwa uku dasha yafara sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske, saiya zame kuma ya kwanta, kafin kacemi barci ya saceshi a haka. nima ajiyar zuciyar nayi ina girgiza kai da share hawayen dake silalomin, ina rok'on ALLAH ya kawoma wannan bawan nasa sauk'i da rangwame cikin gaggawa da warwarewar al'amura. Dagashi har yaran tausayi suke bani, nayi zurfi a tunani wayarsa tayi ring, kamar zan share saikuma Na tuna maybe Momma ce, tashi nayi zuwa inda wayar take, aikam dai itace, nayi picking jiki a sanyaye, dan tunanina kota gamajin komai, amma sainaji sa6anin haka, da y'ar raharta ma tace, “Muh'd duk hidimar sunance haka?”. “Uhm Momma bashi bane nice”. “a'a d'iyata kece?”. “eh Momma, kuna lafiya? ya jikin Abie?”. “Alhmdllh d'iyata, ya k'arfin jikinki kema? ina yaran?”. Gabana ya fad'i, Na had'iye wani yawu da k'yar, cikin in ina nace, “lafiyar kowa k'alau Momma, shima y... yana barcine”.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92