Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saida yaga ta kwalin ta k'are sannan ya sakarmin hannu na tashi zaune. Bansan kawai na fara kaima k'urjinsa k'ananun dukaba, ina fad'in wlhy sai ALLAH ya sakamin, kai bama zan yarda ba fa, saboda k'azanta kaita had'a yawunka da fresh milk kana d'uramin, ni bazan yardaba”. Shagala kawai yayi yana kallona, yakasa kare kanshi balle yunk'urin hanani, saida nayi mai isata sannan na fad'a k'irjin nasa ina raira kuka. Lumshe idanunsa yayi yasaka hannayemsa ya zagayeni sosai yana kuma sakani jikinsa sosai. Nima sainayi luf Ina shak'ar k'amshinsa da yariga ya mannema fatarsa. Munja wasu times a haka, ni ina kuka shi kuma idonsa a lumshe yana shafa kaina da saurarena. Jiyay kawai jikinta ya saki, alamar barci ya d'auketa, sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, bud'e idonsa yayi, sannan yakai bakinsa a hankali ya sumbaci sumar kanta dake tare da danshin ruwa har yanzu. zafin zazza6inta dake ratsa 6argon jikinsa ya sakashi fidda huci yana kuma sumbatar kanta. Dr Farida ta sanar masa babu abinda zai hanata wannan zazza6in, koda tasha magani ya sauka saiya dawo, sai idan cikin yayi kwarine maybe ta daina ma gaba d'aya, amma mai juna biyu ba'a rabata da k'ananun ciwo makamantan haka. jiyay ya kuma k'aunar Momma d'insa a ransa, a hankali ya furta I love you my Momma”. Tashi yay d'auke da Munaya a hannu, ya kwantar da ita sannan yaja bargo ya lullu6a mata. tare da sunkuya wa ya sumbaci goshinta ya shafa cikinta da hannunsa sannan ya mik'e ya koma inda yake. Ya cigaba da aikin dayake a laptop Wanda ban fahimci komaiba a ciki, tsawon lokacin yana aikin, saida ya fara hamma sannan ya kashe. bayi ya shiga ya d'auro alwala, ya gabatar da nafila kafin yay shafa'i da wutiri yaja doguwar addu'a da kirari wa Ubangijin talikai, harda hawayensa sannan ya mik'e. Ya kuma daidaita hasken fitilar d'akin sannan ya hau gadon shima ya kwanta, yay musu addu'a ya shafe cikin munaya (😂Galadima saboda tsaro ba tsoroba ko🥺). a zatona zai rungumeta, sai naga ya gyara kwanciyarsa kawai a gefenta yaja bargo shima. Galadima asuba ta gari, (ni dai rungume nawa mijin zanyi aradu🤫🙈⛹🏻‍♀). Ga bannin asubahi zazza6in munaya ya sauka, hakanne ya sakata samun dad'in barci sosai, ta kuma kanainaye Galadima, wanda shi da kansa ya mirgino har inda take cikin barci ya rungumeta, dukda zafin zazza6inta nata ratsa nashi jikin yakasa barinta. ahaka kiran sallar farko ya riski kunnuwansu. Kusan a tare suka farka, ganinsu manne da juna yasaka kowa barin jikin d'an uwansa da sauri, munaya dai kunya ta sakata juya baya, amma boss ko a kwalar rigarsa, saima tashi da yayi yana wani ciccin Magani ya shiga toilet. Alwala ya yo, baiyi mata magana ba ya fice abinsa. Munaya ta raka bayansa da harara tana fad'in Girman kai dai rawanin tsiya wlhy. tashi tayi itama ta shiga bayin, amma sa6anin shi ita harda wankan gasa jiki (lallai kinji basawa Munaya🤭, wannan gasa jiki dabaya k'arewa haka🤥😂). Fitowa tayi tanata kumbura fuska, ni dai na lalla6a na shige bayinta danna dandalo arzik'i😝 lol (koya kukace fans🤷🏻‍♀😂?). **************************** Ban sake jin d'uriyarsa ba sai around 9:30am. Tashina a barci kenan na rarrafa zuwa bayi da k'yar nayo wanka, dan banajin dad'in jikina gaba d'aya, danan ya saki sai nan ya kama ciwo. Motsin mutum naji a bayana dan haka na waiga, Galadima ne cikin Farin wando da t-shirt itam fara tas, ya d'aure k'ungunsa da Navy blue d'in belt, sannan ya kawo jacket navy blue itama ya saka, babu takalma a k'afarsa, sai dai k'afar fes tamkar ba'a takata a k'asa, sai agogon azurfa mai k'yau d'aure a tsintsiyar hannunsa. hummm dan k'yau kam dai yayishi, sai dai ni bawai ya birgeni bane😏 (ho Munaya banda zuk'i ta malli dai🤥🤣😝🙆🏻). Janye idona nayi na maida kan gyaran gashina da nakeyi. Shima baice uffanba ya wuce wajen frigate, fresh milk ya d'akko yatako gaban mirror inda nake zaune. a saman mirror ya ajiye kwalin madarar ya jingina bayansa shima, idonsa a kan gashina danake gyarawa. ya d'au madarar ya zuba a cup d'in daya d'akko tare da mik'omin. “ni ba ita zan shaba”. na fad'a ba tare da na kalleshi ba. “mikenan?”. shima yafad'a cikeda k'asaita. Yanzunma ban kalleshi ba nace “tea”. Kofin ya dire saman mirror yana tattare hannun rigarsa, “salon ki k'onamin idon abin cikin kwan kenan, to za6i ya rage naki, sha da arzik'i ko kuma d'ura”. Babu shiri na d'auki kofin na kwankwad'e, dama iyayine inajin yunwar. Kofin na mik'a masa ina 6ata fuska tamkar zan fasa ihu. Ya d'agamin gira yana fad'in “taimakon kai my friend”. Gefe nayi da fuskata ina fad'in “kai duk salon mugunta ka sani ai”. “martabar gudan jinina nake karewa”. yay maganar yana k'ok'arin ficewa. Baki na na ta6e ina harar bayansa, su gudan jini anji jiki kuwa. Ganin zai fice nai saurin cewa “nifa inason zuwa kitso, kuma zan koma school”.. Tsayawa yay cak daga yunk'urin fitar da yakeyi, Batare daya juyoba yace “babu wannan tsarin a masarautar gagara badau”. Yana gama fad'a ya ida ficewarsa. Tamkar zan fasa kuka nayi jifa da cumb d'in hannu na ina fad'in “ina ruwana dawani tsarinku ni, makaranta ta nakeson komawa ehe”. Yana jiyota amma ko'a jikinsa yaci gaba da k'ok'arin fitarsa hankali kwance. ★★★★★★★★★ Tunda Aryaan ya shigo da gudu inna ta tareshi tana fad'in “kai lafiya? minene na gudu?”. “innarmu wlhy Uncle ne yace ki shirya mana kayanmu ni da Aiyaan zai aiko gobe a kaimu wajen Auntynmu”. Inna tayi d'an murmushi kawai, dan ita bata d'auki maganarma serious ba. Su dai su Aiyaan sunata murnarsu, sun tafi d'aki sun hau had'a kaya. Babu dad'ewa da yin haka saiga daddy ya shigo da sallama, inna ta amsa masa tana gyara zama, shima zama yay kujerar dake kusada k'ofa, ganin haka inna ta fahimci da magana yazo, dan haka ta maida dukkan hankalinta Kansa. Bayani yamata dalla-dalla akan zancen da su Galadima sukazo dashi, ya d'ora da fad'in “saiki shirya dan zamuje ai miki passport”. Inna tace, “amma dadynsu nake ganin ai da kud'in kukaje kamar zaifi”. Murmushi Dady yayi, yace “Ai'sha nasan miyasa kikeso zamewa, to ai kaf cikin matan yayan kece ya cancanta kije koda ace bawai Galadima ne ya biyaba, maganar ciwo Muke bawai jin dad'i ko gutsiri tsomar wasu ba, ki shirya dan zai turo wanda zamuje immigration office d'in”. daga haka ya tashi ya fice. Shiru kawai inna tayi, itadai inda ta itace da antafi da ko innaro, dan tasan wannan tafiyar dukda ta ciwoce sai ta janyo 6acin rai a gidan. Aiko tamkar inna tasani, dan ana fad'ama innaro tace “bata amince ba, ita ta haifi auwalu kuma da ita za'aje tayi jiyyar yaronta, bazata bama kowacce mace acikinsu wannan ragamarba. Shiru baba k'arami da daddy sukayi, taci masifarta ta gama tayi shiru. Baba k'arami yace, “amma dai inna kinsan jinyar Yaya sai da matarsa a kusa, kekuma k'arfinki ya k'are ya za'a d'ora miki d'awainiyar da matansa ne keda hakki a kai?”.. “yo d'awainiya ba tare da kai za'a tafiba? Kai basai kamasa ba. ni dai fa ban amince Ai'sha tajeba, dan wlhy bazan ta6a son Ai'sha ba komi zata zama, tunda dai ta silar jikokinane balle amin ilimi. k'ilama

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});