Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

[7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ____________________________ *_Dolene page d'in farko yazama sadaukarwa agareki MAMAN JUNIOR😭, ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari, ALLAH ya k'addara bazakiga k'arshen wannan littafiba. (Masoyan Raina kama kusaka wannan baiwa a addu'arku, ta rasu cikin azumi, kusanma k'arshe, member ce a group d'in raina kama, ALLAY ya yafe mata🙏🏻😭._* _INA fata kunyi salla lafiya gaba d'ayanku, ALLAH ya kar6i ibadunmu. Ya yafe mana, yasa kar6a66iyar ibada mukayi🙏🏻😭._ Sai dai banci naman salla ba sosai, gashi banida d'inkin dallah🤦🏻‍♀🤥. ______________________________ ~Book 2~ 👉🏻1⃣ .............Tunda mukayi maganar nan dashi banyi k'asa a gyuwa ba wajen dagewa da addu'oi wa mahaifinsa, ina buk'atar ruwan zam-zam, dan haka yau nashirya fad'a masa ya nemomin. tunda safe ya fice, dan haka bamuga juna ba. Yauma dai haka Na tashi banida wata isashshiyar lafiya, Na tak'ark'ara nayi gyaran d'akin har zuwa falo, sannan Na had'a ruwa mai zafi nayi wanka dashi. Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a k'ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k'arasa, sannan nace ta shigo. “humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a mirror kuwa?”. Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli jikina, nace, “kamarya?”. Zama tayi a sofa tana 'yar dariya, sannan tace, “wlhy kinyi k'iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata madam”. Nad'an fiddo idanu waje, sannan Na harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”. “tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na fad'a, halan Uncle Sam bai ta6a fad'a mi ki ba........” Ta k'arasa Maganarta da d'ai-d'ai saboda shigowarasa d'akin da sallama ciki-ciki. Suna had'a idanu ya watsa mata harara, hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik'e ta fita, Nikuma najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa. Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo d'aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid'e bisa fuskarsa. “yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad'a cikin tausayawa’. Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka a hankali zuwa gabansa, durk'usawa nayi a gaban nasa, a d'arare nasa hannu Na najanye nasa dayay tagumi dashi. Ya d'ago idanunsa da sukai jaa yana kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar zuciya nakuma fad'in “bakada lafiya yalla6ai?”. Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji yakamata ya fad'amin, kodan nuna damuwar danayi akansa...... Ganin yamin shiru nikuma saina yink'ura natashi ina fad'in “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawab......” Bankai k'arshen maganarba naji tattausan tafin hannunsa cikin nawa. Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare hannun kawai ya fisgoni na fad'a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera. Bansan nawani lumshe idanuba saboda daddad'an k'amshin turarensa d'aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma ya sauk'e 6oyayyiyar ajiyar zuciya. Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a gefen kafad'arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d'ina, mayun idanun nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k'ok'arin cire kannawa daga kafad'arsa. Hannunsa na dama da nake jiki ya sak'alo ta bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad'ar tasa, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi barciba gaba d'aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..” ‘yak'are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara maganar’. Wani matsanancin tausayinsa ne ya ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya, nima hawayen suka fara gudun fanfalak'e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai, cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda hard'e hannayensa a k'irji. duk da kujerar tama tsawonsa kad'an, dan ma Love's chair ce. Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye na zirara daga idona har yanzun. Shikam idanunsa a lumshe suke. Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace, “Yalla6ai kayi hak'uri, Abie d'inmu yana buk'ar addu'armu ne fiye da kukanmu, sannan itace jarabawarsa, wad'anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu'oi Dana Sani, Nina kakanmu ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya gagaresa, kuma shine yace mu rok'esa zai amsa mana”. Tunda nafara maganar bai bud'e idonsa ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k'arshen zancen sannan ya bud'e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru. Nima shirun nayi ban sake yink'urin yin magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci ya d'aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali. Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da Momma gsky, duniyar tunani nafad'a batare dana fargaba, tausayin Galadima da families nashi yana cukurkud'ar ruhina, insha ALLAH nayi alk'awarin bada gudun mawa a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k'are. kaina na jingina da jikin kujera, nima sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad'in jikina nakeyiba. ******** Bayan anma Abie allurar datake temaka masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami nutsuwa, dan yayi barci. Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan Galadiman ba. Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d'an uwanki?”. Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta yadawo ta farga babu Galadima d'in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya fita, bara na duba”. Bata jira cewar Momma ba tafito daga d'akin da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak'ara tashi, fitowa tayi harabar asibitin tana tambayar securitys d'in wajen. d'aya ya sanar mata ya fita a rikice gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba. Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen Momma ba tashiga mota tanufo gidan. Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d'inku?”. Samha tace, “yana sama Mummy”. Da sassarfa ta haye step's d'in, itadai Samha da mamaki taringa binta da kallo. Ko knocking bata tsaya musuba ta turo k'ofar ta shigo. Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d'aya na bisa Kansa, yayinda shikuma yarik'o d'ayan hannun munaya ya had'e da nasa ya d'ora kan kirjinsa, suduka barci ya kwashesu a haka. cikin sand'a ta juya ta fita taja musu k'ofar tana share hawaye dayima ALLAH godiya d'aya bama d'an uwanta mace tagari wadda take kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai. Momma ta kira ta fad'amawa dan hankalinta itama ya kwanta. Momma harda hawayen farinciki, tana godema ALLAH. Aunty Mimi

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});