Chapter 61
Chapter 61
zatayiba, ita yanzu babbar damuwarta ma 'ya'yanta su sauka lafiya, dansu Safara'u duksun haihu sukam, kuma dab da dab sukaita kancamo 'ya'yan, ayanzu haka sunan d'an Fauziyyane kawai yarage gobe idan ALLAH ya kaimu, dan itace k'arshen haihuwa.. Su fiddausi duk suna gida sunzo wanka, iyayensu kowa ta zuba k'arya a hidimar sunan 'yarta, yanzu maman Fauziyya da innarsu munaya kawai aka zubama ido aga yanda zasuyi nasu. Inna dai bata d'ad'ara kanta da k'asaba, iya abinda ALLAH ya hore mata iya shine tai k'udiri yi a hidamar sunansu Munubiya idan sun haihu. Fatantama su sauka lafiyar, dan gasu suna neman share watanni na goma haihuwa babu amo babu labari. Mama Rabi'a cema kawai keta k'ok'arin ta na ganin sun tanadi dukkan abin fita kunya, sai Aunty Salamah dake taimaka musu, wadda a yanzu tazama 'Yar uwa agaresu makusanciya, dan komai nasu tana tsaye a akai tsakaninta ga ALLAH. WASHE GARI akasha sunan d'an Fauziyya. Wanda mijinta da mamarta suka bada mamaki, masu shirin asha kunya sai aka barsu su dajin kunyar da shak'ar bak'inciki irinna masu hassada. Itama tamkar su Haleematu gida ta taho wankan jego. ************************** A wata ranar talata datai dai-dai da cikar cikunanmu wata goma da sati biyu natashi da matsanancin ciwo, Wanda ya rikita Galadima da ahalinsa, nan take doctors sukace haihuwace, aka fara shirin kar6arta amma ina, gadai haihuwar gadan-gadan da gaske amma kuma nagagara haihuwar har washe garin laraba. Nayi masifar galabaita, Galadima yace sumin cs idan bazan iya haihuwa da kaina ba. Amma sukace zan iya haihuwa. Ranar laraba da daddare Galadima da Momma na kusadani suna ta tofamin addu'a saboda zufar danakeyi, nace su kiramin munubiya, babu musu Galadima ya kira Yaa marwan. Shima dakaji muryarsa zakasan a rikice yake, hakan yasaka Galadima tambayarsa ko lafiya?. Yaa Marwan yace, “dadai sauki ranka ya dad'e, tun daren jiya Munubiya ke nak'uda amma haihuwa shiru, sai sunan Munaya kawai taketa kira”. Mik'ewa Galadima yayi tsaye, yace, “muma ai halin da ake ciki kenan, yanzuma itace tace akira mata ita, please kakai mata wayar”. “ok”. Yaa marwan ya amsa yana nufar d'akinda Munubiya take...............✍🏻 Barkanmu da dawowa.🤩✋🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [7/9, 2:53 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _________________________ *_HASKE WRITERS...._* _gaisuwarku ta musammance, alkairin ALLAH ya baibayeku aminan kwarai abokan tafiya👍🏻😽._ I love you manya-manya fa🥰🥰🥰🥰🤩🤸🏻♀ ________________________ ~book 2~👉🏻2⃣2⃣ ................Cikin kuka Munubiya tace, “y'ar uwata ki taho gida please”. Munaya dake saurarenta ta share nata hawayen itama, “insha ALLAH zan taho, ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe ko yaushe zaki iya ganina sweetheart”. Daga haka munaya ta mik'ama Galadima wayar tana cigaba da share hawaye. Hankalinsa atashe yace, “miyasa zakimata alk'awarin zuwa? bayan kinsan ga halin da kike a ciki”. “kayi hak'uri yalla6ai, gara ka barni Na tafi shine mafi a'ala, tun farko y'ar uwata bata 6oyeminba ta sanarmin naje gida Na haihu, idanma baka kainiba to wahala kawai zanta sha anan d'in tunda hakan take buk'ata”. Galadima jiyay tamkar ya make Munaya, ya haukace mata da masifa kaikace zai cinyeta d'anya, “wannan ai canfin banzane da wofi, ALLAH shine kawai maiyi ai bawani alk'awarinku ba, shin Ku bazaku tausayama kanku baneba? yaufa kwannanki biyu kina wahalarnan, wane irin taurinkai ne wannan.......?”. Dakatar dashi Momma tayi ta hanyar d'aga masa hannu, ta dafa k'afad'ar munaya dake kuka tana fad'in “y'ata dama kinmata alk'awarin zakije Nigeria ki haihu ne?”. “Momma ba alk'awari namataba, amma kusan 2months kenan tacemin gida zanzo Na haihu ko? nikuma bance mata komaiba”. Murmushi Momma tayi, ta kalli Galadima dake tsaye yanata kumbura dan haushi. “Muh'd anemi ticket d'in Nigeria yanzunnan”. Da sauri yace “Momma amma......” Hannu ta d'aga masa alamar bata buk'atar jin komai. ya had'iye wani k'ullutu daya tsaya masa a mak'oshi, shifa ba tafiyar tata bace matsalarsa, shima akwai tashi manufar da dalili, amma bashida ikon yin jayayya da Momma, waya ya zaro a aljihu. Ya lalubo wata number yay kira, ficewa yay daga d'akin. Momma tacigaba da lallashin Munaya daketa hawaye, ga zufa Na cigaba da jik'eta dukda AC dake aiki a d'akin. Kusan mintuna talatin Galadima yashigo shida doctor, dannan aka shirya Munaya, nurses biyu suka kaita mota. Wannan karon harda Momma rakkiya Airport, tanata jerama Munaya addu'oi har suka isa. Haka sukai wannan tafiya babu shiri, Galadima kayan tun safenema a jikinsa bai ko koma gida ya canjaba, hakama aunty Mimi. A jirgi yana rungume da ita tanata murk'ususu idan abin ya motsa, wai danma waje Na musamman aka basu dankarta takura. idan nak'udar ta lafa sai barci mai dad'i ya kwasheta, da abin yamotsa kuma tata kuka kenan tana k'ank'amesa, dukta jimasa ciwo da farce, shikam tausayinta dukya cika zuciyarsa. Yaa marwan ma cikin haushi yakira inna ya gaya mata abinda Munubiya tayi, inna taita fad'a tamkar zata ari baki, itada ta haifi su munaya ita tasan halin kowa acikinsu, tabbas a fili Munaya tafi Munubiya fad'a, amma a bad'ini Munubiya tanada ak'idar tsiya da tsatstsauran ra'ayi, lokuta da dama idan takafe akan Abu bata tankwaruwa, kuma dolene Munaya ta amince ayi kokuwa tasha wahala, dan idan Munubiya ta murd'e abin bazai ta6a ya yuwuba saidai idan Ubangiji ya juna mata ikonsa, to amma bata ta6a zaton shirmen nasu zai iya ta6a har lafiyarsu irin hakaba. Dole inna tashirya zuwa asibitin da kanta, taita zubama Munubiya dake fama da kanta fad'a, su mama Rabi'a da Maman Fauziyya sunata bata hak'uri, tunda dai anrigada an aikata, saidai kuma a kiyaye nagaba. Su Munaya sun iso Nigeria lokacin tsakkiyar ranane anan, dan irin 1pm d'innan ne, dayake yakira su sarkin mota ya sanar dasu time d'in dazasu iya isowa, tun wajen 11am ma suna airport d'in.. Tunda Galadima yafara sakkowa daga matakalar jirgin rungume da Munaya akan idonsune, hakanne yasaka sarkin mota matso da motar bisa alfarmar ma'aikatan wajen, suna gama sakkowa k'afarta ta rik'e, dole ya d'auketa daga ita har nauyin cikin ya k'arasa da ita motar, mutane duk tausayinta yakamasu. Tunfa a mota labari yafara canjawa, dan Munaya tafita hayyacinta sosai, Galadima sai tsawa yakema sarkin mota, ALLAH daine kawai ya kaisu asibitin lafiya, aiko suna shiga dogarai suka shiga da gudu cikin asibitin kiran doctors. Tunima Galadima ya kuma sunkutarta yayi ciki, a hanya yagamu da nurses da gadon d'aukar marasa lafiya, bai d'orataba, yawucesu abinsa, doctor Farida ta nuna masa d'akin da aka canjama Munubiya. Gadon da aka tanada dan Munaya ya d'orata, Munubiya tashiga mik'o mata hannu tana kuka, itama a wahalce tamik'a mata nata, dan gadon kusa da kusa aka sakasu.... A tare suka dinga Neman yafiyar junansu suna kuka, sai tausayinsu ya kamasu Galadima. Da k'yar doctor Farida tasamu Galadima ya fita suyi aikinsu, dama haka tasha dagama da Yaa marwan shima, saida ma Abbansu yamasa magana, Dan shima yana asibitin. Munubiya da Munaya Haka suke rik'e hannun juna kowa nashan azabar nak'uda, (wannan k'auna dabance gaskiya, nak'uda ba abun wasaba amma suna son jin junansu a kusa, wato koma mutuwace tazo musu a tare?😽). Haihuwar Munubiya ce tafara gadan-gadan, Dan haka Munaya ta k'ank'ame hannun y'ar uwarta tana kuka da kiran sunanta a galabaice, itama sai labarin yafara canjawa, Nurse da doctor Farida and doctor Zainab dake Kansu duk suka maida hankali ga Munubiya, cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92