Chapter 24
Chapter 24
katashi da riba biyu kenan, nikuma babu ko d'aya sai bak'incikin danakema iyayena tanadi da kaina, Galadima ko a matanma ai _AKWAI BANBANCI?_ wlhy. gaskiyane Munaya, rik'e darajarki shine 'yancinki😄👍🏻. ******* Bayan sun fito massalaci sukejin labarin wai an rasa inda Muftahu yake, a safiyar yau aka samu motarsa a bud'e, sai kuma agogonsa da takalminsa d'aya a k'asa alamar da k'arfin tsiya aka saceshi. Hakan yasaka aka kama dogaran dake tsaron k'ofa ta uku, dan anga alamun tanan aka fita dashi. Dukda Galadima najin haushinsa saida hankalinsa ya tashi, dan haka suna shigowa ya d'au waya ya kira Nuren. Nuren na d'aga wayar Galadima yace, “Nuren Muftahu, kaine ko?”. “Muftahu kuma? nine naimi?”. “A daren jiya an rasa Wanda ya bar masarauta dashi”. “humm brother, dukda muna ganin Muftahu cikin masu mana zagon k'asa banta6a tunanin saina d'aukeshi zan gane hakaba, wlhy bani bane”. “ya salam”. ‘galadima ya fad'a cikin dafe kai da cije lips, wayar ya yanke ya Shiga safa da marwa, yarasa wazai hararo. Yana cikin wannan halin saiga harun shima a rikice, kowa yasan su ukunnan abokan junane, kuma akwai shak'uwa tsakaninsu, matawalle ne dama bai cika shiga cikinsu ba, saboda mama Fulani Na hanashi tun yana yaro, a cewarta shine d'an Sarki mai mulki, kuma shine mai jiran gado, darajarsa datasu Galadima ba dai-dai takeba, wannan hud'ubar ce tamasa tasiri sosai, amma yanason 'yan uwansa har zuciyarsa. “galadima shin kaji kuwa mike faruwa a masarautarnan?”. Cikin damuwa Galadima yace, “Harun su waye da wannan aikin?”. “kowa abinda yake tambaya kenan Sameer, Muftahu bashida wani abokin fad'a”. Hankalin Galadima kuma tashi yayi, shi duk damuwarsa karda a cutar da Muftahu ta dalilinsa, tunda ya kula duk wani makusancinsu shine abin harin mak'iyansa. shifa baima yarda ba Nuren bane da wannan aikin, dan yasan halinsa sarai, dolene kuwa yafita wajensa yanzunnan. Harun yace bara yaje, suna son akai report gidan radio da television. Jin jina kai Galadima kawai yayi, shima ya shige ciki danya shirya. Tun safe an sanarda jami'an tsaro 6atan Muftahu n, kuma suna a kan aikinsu. ★★★ Yunwar da yakeji tasashi bayan yayi shiri ya samu fresh milk yasha kawai, sannan yafito, d'akin Munaya ya lek'a, saiya isketa baje a gado tana shak'ar barci, baiyi yunk'urin tashinta ba yafito. Har dogaransa sun taso yace suyi zamansu su huta, zai fita shida Sauban, cikin damuwa sarkin mota yace, “kayi hak'uri ranka ya dad'e, koda nine kawai mu fita, Mai martaba ya sanar yau a fada kar'a sake barin wani d'an gidannan yafita wani waje shi kad'ai”. Kallonsa Galadima yayi, kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya bud'e mortar da kansa ya shiga, batare da ya jira an bud'e masa ba. Da hannu sarkin mota yayma sauran dogaran nuni da su biyosu a baya idan sun tafi. A wani waje suka had'u da Nuren, Nuren ya fito daga motarsa yadawo inda Galadima yake, sai sarkin mota yafita yabasu waje kawai. Galadima yace “please idan kaine ka sakeshi”. Da mamaki Nuren yace, “wai Muftahu n dai? am telling you banida alak'a da d'aukarsa. yarinyar Minister ce kawai a hannuna”. “innalillahi, wlhy Nuren inajin tsoro, karsuje su cutar dashi”. “Sameer! nifa ina zargin kawai ya had'a baki da wasune suka kamashi dan yayi wasa da hankalinmu”. Idanu Galadima ya tsurama Nuren tamkar yana hango gaskiyar maganarsa, ya saki wani guntun murmushi, sannan ya gyara zamansa yana fad'in “well, koma minene dai zai fito ai”. Nuren yace “ni kaga dama kabar zancen wani Muftahu n banza can, way note mu wuce gidan sirikanka kozamu samu wasu evidence daga canma akan Accident d'innan”. Agogon hannunsa ya kalla, sannan ya kalli Nuren d'in alamar suje. Anan Nuren yabar motarsa suka tafi ata Galadima, saida suka fara tafiya Galadima ya lura da mototin dogaransa a bayansu. d'an murmushi yayi yana kallon Sarkin mota, yace “sarkin mota an karya min doka kenan?”. Sarkin mota daya fahimci Galadima yagane dogarai Na binsu sai yayi 'yar dariya, yace “ka gafarceni ranka ya dad'e, bazai yuwu mu barka ka fita kai kad'aiba ai, dan fitarka babu kowa tafi ta kowa had'ari a masarautarnan, mai martaba ma nasan saboda kaine ya saka dokar ai”. Galadima baice komaiba sai murmushi dayayi, Nuren ma murmushin yayi, sannan yace “amma kamar bayan motar dogaranka akwai wata bak'ar mota Na bin tasu?”. Galadima ya juya shima, tabbas anabin motar dogaran a baya, “sarkin mota su wucemu, karsu tsaya”. “To ranka ya dad'e”. Bayan sarkin mota ya sanar musu suka wuce su Galadima, motarma ta wuce, da kallo Nuren da Galadima suka bita, Nuren yay hanzarin d'aukar motar hoto a wayarsa. “humm da alama suna zaton kana d'aya daga cikin motocin canne”. Murmushi Galadima yayi, a k'asaitarsa yace, “kokuma suna son wasa da hankalinmu ba”. Da mamaki Nuren yace “kamar ya?”. Murmusawa Galadima ya kuma yi, ya kwantar da kansa jikin seat yana lumshe idanu, “Nuriddeen! Sameer ya wuce tunanin dukkan mai tunani, kai tsaye ba'a gane manufar zuciya, kwanji ko dama basu ke nuna k'arfin ikon mai ikoba, nazarin komai daki-daki da iya sarrafa duniya a yanda tazo shike nuna k'arfin gwarzan taka, mazantaka ba'a shaidata a fuskar namiji, duk lokacinda kai gamo da nama, kud'i, mata bisa hanya, karkayi rawarkan d'auka ko murnar ALLAH ne ya baka, zata iya yuwuwa tarko aka d'ana maka, shi k'yawu had'arine, 6oyeshi kuma nagartace, maiyi baya fad'an zaiyi, sai dai aga aikinsa a k'asa, tasowar iskar hadari bashi ke nufin ruwan zai zuba ba, watak'il sunan wannan iskar gyara kayanka. Dalili da dalilai basa ta6a saka zuciyar Wanda yake nema ta raunana, time d'in da zan nunama mak'iyan mahaifina d'an zaki ya girma yayi, sun durk'usar da shi a k'asa batareda tunaninsu yabasu ya haifi Raina kama ba, Su cigaba da raina aikin Muhammad Sameer daga k'arshe kuma saisuga gayya, tafiyar hawainiya bashike nufin gazawar kuzarinta bane, lokuta da dama hanzari kan katse igiyar cikar buri, a sannu kowa zai fahimci wanene *_RAINA KAMA....._*👎🏻 Ba Nuren ba hatta da sarkin mota maganganun Galadima ya shigeshi, tabbas mutane dayawa sunama Galadima kallon mutum mai yawan sakaci da rashin ho66asa, koshi yana d'aya daga ciki, amma wannan zantukan nasa sai suka sakasu a rud'ani, kenan akwai abinda sud'in basu saniba........... Dole tunaninsu ya katse saboda isowarsu gidansu Munaya. Fita sarkin mota yayi yanema musu iso, babu dad'ewa saiga baba k'arami ya fito, sarkin mota ya bud'ema Galadima, yayinda Nuren ya bud'e da kansa, zuciyarsa sai jujjuya hannunka mai sandar Galadima yakeyi. Dukda baba k'arami yayi mamakin zuwan Galadima haka ya danne, yaymusu k'ar6a ta girma, sannan suka shiga cikin gidan. Gidan tsitt tamkar babu mutane, saikace ba gidannan bane mai kama Dana 'yan dambe😂, (yo kowa Na tsoron a korashi gidansu🤣😝). A falon daddy aka musu masauki, dan danan aka cika musu gaba da kayayyaki, baba k'arami ya fita domin basu damar cin wani Abu. Babu abinda suka ta6a, dukda kuma Galadima ma yunwa yakeji, a haka daddy da baba k'arami suka dawo. Daddy yace “anya kuwa wannan d'an namu yana d'aukar gidannan matsayin nasu?”. Murmushi Galadima da Nuren sukayi, Galadima yace “sosaima daddy”. Baba k'arami yace “ta INA zamu amince da haka kuwa, bayan inada tabbacin ko ruwan gidannan Baka ta6a sha ba”. Kunya Ce ta kama Galadima, sai kuma yaga bai k'yautaba, ya rissinar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92