Chapter 33
Chapter 33
fuskantata, ina yunk'urin tambayar lafiya naji la66ana cikin bakinsa. Ya salam, na fad'a a zuciyata, saida ya shanye janbakin la66ana tas sannan ya sakeni. yanda kukasan gunki haka na koma masa, ya buga yatsunsa biyu saitin fuskata suna bada k'arar d'as d'as yace “gargad'i, first and last dazanganshi abakinki yayin fita”. Harya fita ban iya motsawa ba, saida aka bud'e murfin 6angaren danake sannan na iya sauke numfashi, na kasa fahimtar damuwar guy d'innan kwata-kwata. fita nayi nima, yana tsaye yana jiran fitowata. a tare muka jera muna tafiya, yayinda dogaransa ke take mana baya. ya wani miskile fuska tamkar bashine yagama ta6argaza ba a mota yanzun. Mutane sai kallonmu suke, masu gulma nayi masu nunamu nayi, ni dai duk sainaji wani iri, shima tsaki yayi danya tsani kallo. A mamaki na duk sai naga 'yan gidanmu ma a wajen, gaggaisawa muka shigayi, muka rik'e hannun juna nida munubiya muka k'arasa inda innarmu take, gaisheta nayi, nace “su Aiyaan fa?”. “suna gida zasu zauna da mamanku mana”. “kai innarmu, ya zaki barsu wajen muguwarnan, bama gara Maman fauziyya ba komu suzo wajenmu”. Murmushi kawai innarmu tayi, tace, “ashe bazaki canjaba Munaya?”. 6ata fuska nayi, ina fad'in “kai inna, duk canjawarnan danayi”. Murmushi sukayi itada Munubiya. akuma dai-dai time d'in Ambulance ta shigo airport d'in, sai mota biyu a bayanta sai motar police guda d'aya. Gaba d'ayanmu hankalinmu saiya koma can, Galadima ya k'arasa wajen Ambulance d'in, yayinda sauran motocin biyu Sauban da Nuren baba k'arami Dady ya Shafi'u da yaa Naseer yaa hameed suka fito. Zuwansu baifi da mintuna 15 ba aka fara kiran sunan wad'anda zasu tashi a jirgin. Sai kuma ma'aikatan wajen mutum uku suka iso wajen Ambulance d'in aka fara k'ok'arin fidda Abba. Hankalin jama'a da yawa ya tashi a airport d'in nan saboda tausayin Abba, mukam kuka ma wasunmu sukeyi ai, muna kallo aka gungura gadon da aka d'oroshi har zuwa ga jirgin. Suma su innarmu suka shiga itada baba k'arami da Sauban. Rungume juna mukayi nida munubiya muma muna kuka. Galadima bai fito cikin jirginba saida yaga komai ya dai-daita. yana fitowa babu dad'ewa jirgin ya d'aga zuwa sararin samaniya, yayinda mukuma muke binsu da addu'oin fatan alkairi da samun sauk'i.................✍🏼 🤥kutt harda na gobe nayi🙄⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻1⃣2⃣ ...............Maman Fauziyya tamatso ta kama hannunmu ni da Munubiya tana lallashinmu, da fad'a mana mu bisa da addu'a, insha ALLAHU da k'afarsa zai dawo. Ganin mun fara shirin tafiya na taka inda Galadima yake tsaye da Nuren suna magana, tun d'anzun ina lura dashi ya kafeni da idanu, yanzunma suna maganar amma idonsa na kaina na k'araso garesu. Nuren daketa fara'a yace, “gimbiyarmu barka da hantsi”. Murmushi nayi sannan na gaisheshi, ya amsa yana tambayata yaya jikina?. Nace “Alhmdllh na warke ai”. “to ALLAH ya k'ara afuwa gimbiya”. ‘yafad'a yana matsawa gefe domin bamu waje. Galadima dake kallona hannunsa duk biyu cikin wandon sky blue d'in shaddarsa da tsawon rigar iyakarsa rabin cinyarsa, yace, “Lafiya?”. Dakewa nima nayi, cike da jan ajina nace “k'alau. Dan ALLAH zanbi Munubiya please yalla6ai”. Janye idanunsa yayi daga kaina yana fad'in “awane farashi?”. “kamarya farashi? ciniki mukeyi?”. Hannunsa d'aya ya fiddo daga aljihu ya shafa sajensa zuwa gemu, cikin kafeni da idanu yace “kusan haka, kinsan rayuwar bani gishiri in baka manda akeyi yanzun”. Cikin son tura masa haushi nace “Ai ni bana gane Hausa cikin hausa”. “really? lallai kin fad'o kuwa, kuma saiki ce ke bahaushiyace?”. Baki na tunzura masa saboda haushin rainin wayon da yake min, gasu Munubiya kuma shirin tafiya sukeyi. “Kinsan wannan bakin kika bari na kamashi a airport d'innan....., hummm”. Idanuna na waro, “mi kake tunanin zakayi kenan?”. “kuma turowa saina nuna miki”. ‘yafad'a yana matsowa’.. Baya na matsa da sauri zuciyata na harbawa, anya kan Galadima d'aya kuwa?. Kwafa yayi yana kallon agogon hannunsa yana k'ok'arin zaro waya daga aljihun gaban rigar datake ring. Nikuma na hararesa a zuciyata ina fad'in mara kunya ai nasan zaka iya. A fili kuma nace “please yalla6ai nidai badan halina ba”. Bai bani amsaba, sai sallamar danaji yayi wayarsa akan kunne. Jinai kawai yace, “Harun kana inane?”. Bansan wace amsa ya bashiba, naji yana fad'in “ok idan ka tashi saimu had'u”. daga haka ya yanke wayar sannan ya kalleni. “uhm mikike cewa?” Haushi tamkar zai karni nace “please mana autan Momma”. Murmushi yayi yana cije lips, “wlhy yarinyarnan kin gama rainani, ninema Autan?”. “lah nama manta ashe kaifa na tsakkiyar momma ne, karma Yaa Sauban ya jini”. “kinsan ALLAH na damk'eki a airport d'innan saikin fad'amin dawa kike”. Dariya nayi ina d'aga masa yatsu biyu, “karka damu yalla6ai zanyo maka tsarabar sweet and biscuit yeah”. Da sauri yay yunk'urin damk'o hannuna ganin zan gudu. yana rik'owa mukaji ance “hallo”. A bayanmu. Batareda ya saki hannuna ba duk muka waiga ni da shi. Matashiyar budurwa fara k'al, kuma k'yak'yk'yawa masha ALLAH. Dan danan ya tsuke fuska, tamkar ba shine yagama murmushiba yanzun. Nima bansan murmushi ya gushema tawa fuskarba, baiyi magana ba, sai nice nace “lafiya kuwa?”. yanda nayi maganar cikin rainin hankali yasaka yarinyar rik'e ha6a tana ta6e baki tana fad'in “ke kuma fa?”. Kamar zanyi magana saikuma Na shareta kawai, galadima Na kalla fuskata a cunkushe alamar fushi, d'ayan hannunsa ya d'agamin yana ta6e fuska alamar shifa babu ruwansa. Na tura baki tareda juyawa zan bar wajen. Hannuna dake cikin nasa ya kuma damk'ewa da k'yau, hakan yasani dawowa baya tamkar zan fad'a jikinsa, amma nayi jarumtar tirjewa kodan jama'ar gidanmu. Dama ajikin wasu motoci muke, sai kawai ya fisgi hannuna muka shige tsakkiyarsu ya mannani jikin mota shikuma yamin rumfa. ban ankaraba naji bawan ALLAHnnan ya ha.......🤥. Jikina kawai rawa yakamayi saboda tsoro, wlhy ban ta6a tunanin da gaske yake zai iya hukunta bakin nawa a airport d'inba. Ita kanta budurwarnan idanu ta zaro waje cikin wangale baki. Nuren dashi kad'ai yake saitin dazai iya ganinmu saikuma wasu tsirarun mutane dake nesa damu, wad'anda ba lallaine ma su fahimci abinda akeba, kaucewa kawai yay daga wajen yana tuntsura dariya. 'Yan gidanmu sunga lokacin da Galadima yaja hannuna muka shige tsakkiyar motocin, amma basa hangomu. tsabar gulma irinta mamansu Yaa Hameed da Momy da Maman Safara'u sai suna shiga k'ok'arin son ganin mi mukeyi a wajen?😱 su duk tunaninsu wata maganar banza nama budurwarnan yake shukamin rashin mutunci Dan duk agaban idonsu tazo wajen har rik'omin hannu da yayi, dukda basa jin mi Muke fad'a Dan muna nesa dasune. Yaa Sabi'u dabasu lura da abinda ke faruwa ba suka Shiga musu maganar INA zasuje? suzo su ajiyesu gida sufa wajen aiki zasuje. Ina basu saurareshiba saida sukazo saitin dazasu iya ganinmu. A tare suka zaro idanu, Baki da hanci, duk sun shiga mamakin ganin Galadima Na kissing d'ina, ai babu shirin suka koma baya zukatansu Na tukuk'i da jifanmu da kalmar 'yan iska fitsararru. (🤣Yo wayace kuje gani? kazantar dabaka ganiba sunanta tsafta😏😜). Yana Sakina kunya tasakani fad'awa k'irjinsa Na 6oye fuskata, hannayensa yasaka ya zagaye bayana yana dallama yarinyarnan wata muguwar harara data saka hanjin cikinta kad'awa, babu shirin tabar wajen tana mak'yark'yata da tunanin Galadima ko dai kurmane da gaske. Driver d'inta dake kallon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92