Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bakinsa saman idona, dole nafara marmar da idanu, dainawa yayi, na bud'e idon ahankali a kansa, kuma matsoni yayi muka Zuba juna ido ko k'yaftawa bamayi, gashin dake neman shigarmin ido ya saka d'an yatsa ya matsar, na maida idanun na lumshe ina sauke k'aramar ajiyar zuciya. Shima nannauyan numfashi ya sauke kafin yaja da baya, wardrobe d'insa ya nufa, jin yabar wajen saina bud'e idona, duk jikina ya saki, kallo d'aya namasa na d'auke kaina na juya ga mirror Dan naga yanda ya maidani, murmushi nayi ina saka hannu na gyara gashina, nima na yarda da gaske nayi kyau. Nakuma d'ago ido da nufin sake kallon kaina sainaganshi a bayana, sark'a ya ziro a ya sakamin tareda gyara zamanta ta zauna sosai a k'irjina, ya janye gashina ta baya yana sak'ala sark'ar, nidai nawa idone, ya gama ya cire d'an kunen dake kunnena ya sakamin na sark'ar, sannan ya mannani da jikinsa yana zagayo hannunsa duk biyu saman matashin cikina, hannuna ya kama yana sakamin bangles, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa yake magana cikin kunnena, “haka dama sari kema Afirikawa k'yau?”. Murmushi nayi, na d'ago idona muna kallon juna ta cikin mirror, haryanzu hannayena na cikin nasa yana saka bangles d'in da guda d'ai-d'ai. Ya lumshe idanu yana shanshanar wuyana, jikina yafara rawa, babu shiri na saka hannuna d'aya daya gama saka bangles d'in na shafo gefen kumatunsa, cikin rawar murya nace “please kabari yalla6ai”. Batareda ya dainaba cikin sark'ewar harshe yace “mizaisa na daina? yalla6iya”. Yanda yake min akan dokin wiya da yanda hannunsa d'aya ke canja salo a jikina sainayi k'ok'arin juyowa garesa, ko hakan zaisa yabari d'in. Ashe dama ma na sake bashi, gaba d'aya yawani rikice kamar ba Galadiman Dana saniba. Hannunsa ya sak'alo kuguna yana kuma matsoni jikinsa sosai, yasaka d'ayan hannun ya tallafo kaina tareda d'ora la66ansa akan nawa. Kasa jurewa nayi, na mik'a masa wuya kawai, harda bada gunmawa nima........ Tofa munga idi, daga gyaran sari🙆🏽😹. Samha tataho da karsashinta dantaga ko Munaya ta saka, daga nan ta nuna mata yanda zata nad'a zanin sarin, tunda tasan bata iyaba, ko kad'an babu Wanda yaga shigowar Galadima, Dan babu kowa a falon, jakadiya ta tafi asibiti itada Sauban da innarsu munaya, aunty Mimi kuma barci takeyi, Dady kam yanacan baya inda ya maida lambun tunaninsa, itako Samha tana bama Munaya sari takoma d'aki danta bata lokaci ta shirya a tsanake. Sallama d'aya kawai tayi ta turo k'ofar tana kwala kiran “Aunty gimbiyarmu kin saka?”. Galadima dayake Neman fara zirmawa yay hanzarin sakin Munaya, da sauri naja baya nima, dan kamar a sama mukaji muryar Samha. Itama Samha baya ta koma da sauri gabanta na fad'uwa, Dan ganin Wanda batayi zatoba a d'akin. ALLAH ma yaso bataga komaiba, lokacin datake sako k'afarta a d'akin Galadima ya janye bakinsa yana k'ok'arin matsawane baya. Wata uwar harara mai kad'a hanji da hanta ya zubama Samha, hakanne yasakata yin baya da sauri ta koma. Nikam kasama d'aga ido nayi balle na kalleshi dagashi har Samhar, saima wani yaam nakejin jikina tamkar zan fad'i. Lura da hakan da yayine yasakashi azamar rik'o hannuna, na shige jikinsa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, dagani harshi idanu kowa ya lumshe, tsawon lokaci muna a haka munkasa sakin juna, ahankali na shiga k'ok'arin janye jikina, bai hananiba yabani damar barin jikinsa, ra6awa nayi ta gefensa na wuce, na koma saman sofa na zauna ina dafe kai, juyowa yayi yana kallona, kafin yatako shima zuwa bakin gado ya kwanta, k'afafunsa na k'asa duka, yayinda yay filo da hannayensa yana lumshe idanu. Duk munyi shiru d'akin tamkar babu wata halitta mai numfashi a cikinsa, kowannenmu shiyasan mi yake sak'ama zuciyarsa. K'arar wayarsace ta sakamu d'an firgita mu duka, duk sai muka zubama wayar ido tamkar wani ojuju. harta tsinke bai d'aukaba, saida aka sake kira sannan ya cirota daga aljihun wandonsa yay picking. Muryarsa vary low yace, “Nuren Yaya dai?”. Mamaki da al'ajabi ya cika Nuren, yakuma Ciro wayar daga kunnensa ya duba Dan tabbatar da Galadima ne kuwa?, lallai shine, maida wayar yayi a kunne yana fad'in “brother lafiyarka kuwa?”. Taune lips nashi yayi, ya yanke wayar, dan indai ahaka zasuyi wayarnan bazai fahimci komaiba, ajiye wayar yayi yatashi ya shige bathroom. Da kallo k'asa-k'asa kawai na iya binsa, amma nakasa ko kwakwkwaran numfashi. Daga can kuwa Nuren kwashewa yayi da dariya saboda tuno wani Abu, (to su Nuren dai dama bariki sune manyanta🤣), dariya yakeyi iya iyawa yana dukan kansa, daya fara tsagaitawa saiya kuma saka wata, saida yayi ta ishesa sannan ya daina, ya rik'e ha6a yana fad'in “oh ni su brother ansan takan tsiya, ina ganinsa lab-lab Ashe d'anba sauk'ine, toma uwar miye na d'agamin wayar tunda yasan yafara sauka a network🤣, yakuma saka dariya saikace wani sabon kamu.😬 Galadima kam ruwa ya sakarma kansa kawai, ya dafe bango da hannu biyu ruwan na kwarara saman kansa, sai faman taune lips yakeyi shi kad'ai, yayi da zuciyarsa ke sak'awa da kwancewa, saida ya ji k'arfi-k'arfi sannan ya kashe shower d'in yaja bathrobe d'in ya saka yana faman sauke 6oyayyar ajiyar zuciya. Inda yabarta anan ya fito ya isketa, kallo d'aya yamata ya d'aukekai, bakin gadon ya zauna yana goge kansa da k'aramin towel, yajawo wayar da d'ayan hannun ya danna kiran Nuren. Bugu d'aya Nuren d'in ya d'aga, da k'yar yasamu ya danne dariyarsa, “brother wai miya farune naji muryarka haka? nifa ka tadamin hankali”. “Ba komai, shin kajene?”. Nuren ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa, Sameer d'an rainin wayone ALLAH, wai babu komai, to naji babu komai aje a haka. “wai kana jina kuwa?”. Galadima yafad'a. “Oh sorry brother network nayin wasa, gani a gidan, amma bankai ga shiga inda takebane”. “ok tom kaje, amma kabar wayar a kunne, inason naji komai”. Nuren yace “to”. Da sallama ya shiga d'akin, sai wani ciccin magani yake. Farhat dake zaune bakin gadon d'akin ta zabga tagumi ta d'ago kai tana kallonsa, yayin da wasu hawaye ke shirin zubo mata. Kujera guda d'aya dake d'akin ya jawo ya zauna. Farhat ta share hawayen kumatunta, murya a sanyaye tace, “yayana dan ALLAH kayi hak'uri, wlhy ina missing d'in families d'ina da karatuna, dan ALLAH idan kasheni zakayi ka kasheni kawai na hutama rayuwa ma ni gaba d'aya”. Murmushi Nuren yayi, idonsa a kanta yace, “bazan kashekiba Farhat, dan bakimin komaiba, kamar yanda na sanarmiki mahaifinkine yaja miki, ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zaki koma gidanku kwana kusa, yanzuma dukba wannanba, wata tambaya nazo yimiki, ALLAH yasa zaki bani had'in kai?”. Kanta ta jinjina masa tana kuma share sauran hawayen, “insha ALLAH inhar nasani zan fad'a maka”. “good girl ”. ‘cewar Nuren yana gyara zama’. “Farhat nasan kinsan duk yaran Abbanki ko?, ina nufin masu masa hidima a office ko a gida?”. “Eh nasan mafi yawansu, dan ina zuwa wajensa a Office, kuma wasu acikinsu sukanzo gidanma”. “Masha ALLAH, kokin san SD?”. “SD!?”. “eh shi”. “gaskiya a yaran Abbana dana sani babu wani mai suna SD”. “okay, amma ko wani mai Something sunan dazai iya kasancewa full name bazaki iya hasasowa ba?”. Shiru tayi ta lula duniyar nazari, shidai Nuren ya zauna mata idanu yana kuma jinjina ma ubangiji akan yin k'yak'yk'yawar hallita, dan Farhat black beauty ce masha ALLAH. A

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});