Chapter 58
Chapter 58
ya d'ago yanamin sannu da zuwa. Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda gaishesa. A tsararren falon gidan muka yada zango, komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandanan Akash ya tara mana kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d'ora da barkwancinsu irin Na abokan da suka shak'u. A firar tasune nakejin Auren Akash d'in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna da fatan kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne. Bayanin yawan cin abincina Galadima yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda da, karka manta yanzu ba ita kad'ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu shima, kunk'i yarda ayi scanning muga adadin 'ya'yan namu ko jinsun su”. galadima ya murmusa kawai, karka damu, miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”. “no babu wata Matsala, abindama yasa zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak'ara girma abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a cikin, idan da zaka kalli cikin a time d'in datakejin yunwar sosai har yanda yake wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”. Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran naci abincin sai a nutsu”. Akash yay dariya, “Alamun yana cikin k'oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk'atarsa”. Galadima ya juyo muka kalli juna, gira ya d'agamin nikuma nayi murmushi ina kauda idona gefe. Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad'in doctor Johnson yabama Abba glasses d'in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad'esa karyayi wasa dashi saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d'in yazama riga kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima. Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai. A raina nace mikuma Galadima ya shiryama Abban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum. Muna niyyar tashi Akash yace bamu isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane. Badan munsoba mukad'anci abinda zamu iya, sannan yayo mana rakiya har wajen mota. Saida munaya tashiga mota sannan Galadima ke fad'ama Akash yayi mantuwa. Akash yace “tami?”. Babu kunya Galadima yad'an ciza lips yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?. Akash yabashi amsa da maybe salon cikine, danshi babu yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha'awa wani kuma akasin hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya. Tunda muka fara tafiya saina kasa jurewa, na jeho masa tambaya muryata a sanyaye. Kad'an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga tuk'i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk'atar fashin bak'i, akan karantashine a barsa a yanda yazo”. Murmushi nayi ina maida hankalina gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”. “Humm” yafad'a yana rage gudun motar, yanzunma bai kalleniba, yad'an zakud'a jikin sitiyarin sosai, “sometimes akanyi burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk'atar cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”. “to amma yalla6ai karka manta Hasashefa ba shi bane yak'ini”. “wannan gaskiyane yalla6iya. Saidai yak'ini kuma baya amsa sunan tabbaci, daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi nakan rok'i ubangiji nasara Kafin yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad'aituwar samun wannan abin, lokuta da dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a filinda ba muhallin saukarsaba, kiringa zama mai yak'ini saikiga kin tabbata a jerin masu samu”. Murmushi nayi har hak'orana na bayya, nace, “dakai kanarine danace kafi dukkan halittar kanari iya raira zance, dakuwa mawak'ine saina saka a jerin masu zak'ak'an murya, inkuwa a Marubuci kazo to tabbas kai Kanada yawan fik'ira, domin hikayarka zata yawaita saye zukatan mabiyanka ne”. Gefen hanya ya gangara, ya kashe motarma baki d'aya ya maido hankalisa gareni. “Munaaya!” yakirani cikin wani yanayi kuma murya ahankali. nima saina amsa masa a sanyaye. Hannuna ya kamo cikin nasa yana mirza yatsun a hankali, yaci gaba da fad'in “A shekarun baya ni mutumne mai ra'ayin Kansa, ma'ana murd'ad'd'e mai wahalar sha'ani, sannan mai zama a bisa tsarinsa, kece mutum ta farko dana fara doguwar magana da ita koda bana so, nakanyi mamaki a duk lokacin da kika taya nazamo mai sallama miki, anya kuwa bakizo da wani Siddabaru ba?”. Idanu nad'an fiddo waje, nace “siddabaru kuma yalla6ai? to ai awajena ni har gobe kana akan wad'annan ra'ayoyin naka, dan banga canjin dakake hasashen kasamu ba, amma miyasa kace hakan?”. Numfashi ya sauke ahankali, kafin ya ciji gefen lips nashi yana Sosa girarsa d'aya da d'an yatsa “wannan sak'on zuciyane, kibata dama, zata tabbatar miki da cewar wannan Muhammad Sameer d'in yasha banban dana shekarun baya”. “sak'on zuciya kuma?”. nafad'a cikin hasashe, dan nikam Yakuma dilmiyar dani. Mortar ya tada yana fad'in “well basai kin zurfafa ba, dan haryanzu akwai sauran dama”. Baki na d'an ta6e ina gyara zama, “har walau zancen “dama! dama! dai again?, bana son saka baki a hurumin daba nawaba, amma abinda nasani dama dai duk damace, sannan mai ita yakan tanadar mata dukkan muhalin daya tadace da ita, damarmu ce mu damata takowane hanya mukaso”. Idanunsa ya lumshe yana sakin wani k'asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba. Jin Sautin murmushin ya sakani juyawa na kallesa, ya d'agamin gira yana maida hankalinsa ga tuk'insa. Babu Wanda yasake yin magana har muka Isa gida. har yanzu babu Wanda ya dawo, dan haka muka haye sama kai tsaye. dama na k'agara na cire rigar jikina saboda azababbiyar zufar danakeji, danma ya tausaya min yad'an saka AC a mota, ban iya zama ba saida na watsa ruwa, nifa abubuwan sunmin yawa, nice jin zafi nice ci kamar gara, harda alwala nayo, Dan magriba tayi. Ina fitowa shima yashiga yayo alwala. Koda yafito saiya wuce masallaci. Ina jiyo hayaniyar su Samha dasuka dawo amma nakasa sauka, ina kwance abina, hawa da saukarnan bak'aramin wahal dani yakeba yanzu, ahaka Galadima yadawo ya iskeni, sallamarsa kawai na amsa, amma ban iya d'agowa na kalleshiba. Saida ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi kafin yazo ya zauna kan sofa yana fad'in “lafiya dai?”. d'ago ido nai namasa d'an murmushi, nace, “babu komai, gajiya ce kawai”. Shima murmushin yamin, cikin lumshe ido yace, “Sorry friend, saura k'iris insha ALLAH”. “Humm” kawai nafad'a batare da nace masa komaiba. Daga nan muka d'anyi shiru, kusan mintuna 3 yanata latse-latsen wayarsa, batareda ya kalleni ba yace, “Abba kuwa yana saka zobe?”. Kallonsa nayi, amma hakan baisa ya kalleniba, a d'arare nace, “eh yana sakawa amma miyasa kamin wannan tambayar?”. Wayar ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, ya saka d'an yatsansa yana bubbuga la66ansa ahankali, yayinda idonsa yake a kaina tamkar mai nazari, “kina ganin idan kika bashi zai saka?”. Yunk'urawa nai na tashi zaune sosai, “dan sakawa zai saka, amma kana ganin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92