Chapter 74
Chapter 74
a wajen Galadima😜. Lallai, fans sannunkufa, lallai kunma munubiya da Munaya kara, ko Galadima nasan kun gama birgesa aradu, irin wannan anko da kukasha, ko a UK albarka y'ay'an baba buhari😝. ____________________ Isowar Sarki Jalaluddeen da Sarki Abdul-fatah da tawagar wasu amintattun sarakunan abokan Abie ya saka kowa ya mik'e cikin girmamawa, saida suka zauna sannan kowa ya koma ya zauna, an fara bud'e taro da addu'oi ga jarirai da kuma kakansu sannan aka fara gudanar da abinda ya Tara jama'a cikin nutsuwa. Kusan dai lamari Na manya, mudai Fans d'in raina kama sai zuba salfe muke, karkaje kabada labari ace k'arya ka zula bakajeba😆, shiyyasa muka kafa hujja koya kukace my sweet fans🤷🏻♀😂?. Masu 6oyayyen shiri a zuciyaa fa sunata k'iyasata yanda abubuwan da suka shirya zasu gudana, saidai kuma idan sunsan wata basusan wataba, dan eyeglasses d'in idon Galadima Google ne😏, (wato camera ne) tundaga Inda yake yanayo zooming d'in wad'anda suka k'arshen hall d'in ma, duk Wanda zuciyarsa ta saka masa alamar tambaya akansa yana tantancesu ne d'aya bayan d'aya. Nidai Galadima ka kula banda fans d'in raina kama😨🙆🏽. Anyi nisa da taro harma Anfara zubama cikin maik'o da mask'i, ga mai zak'i da sanyi muna korawa, Galadima ya kalli agogon azurfa dake hannunsa sannan ya d'ago ya kalli Muftahu suka had'a ido, lips ya ciza, Muftahu daya fahimci yaren ya gyad'a masa kai, ya kuma kallon Saleem da Nuren da Aunty mimi Mom and Sauban Samha Ayusher, kowannensu Kansa ya gyad'a alamar fahimta.................✍🏻 Turk'ashi, tofa masu karatu, shin mike shirin faruwane haka? Wannan amsa tana page 26 da zaizo ranar Monday insha ALLAH. musha weekend lafiya sisters and brothers.🙋🏻🙋🏻🙋🏻 Barkanku da juma'at😁🤝🏻 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [7/15, 2:13 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ___________________ _Writer's namu ina mik'o gaisuwa da babbar murya_.🙋🏻 *_(takwara) Bily s Fari, (mamana) Maryam IG, (mamana) Ummu hanan, Hauwa'u A Usman (jidda😘) Rufaida Umor, Qurratul ayn, Ai'sha Alto, Leemat, gwoggo😜 Asykhaleel, miss Xakss, Jameela Janaf, (takwara) Ummie Garkuwa, Khadeeja Candy, Billy Sarki, Sister Naja'atu, Reefat yahya, Sad-Naf, Maryam wasagu, Maman Shaheed, classic Feedo, Mzzdady._* 🙆🏽 _Yawane da kufa. Alkairin ALLAH ya kai gareku aduk inda kuke, bilyn Abdull na nayinku wujiga-wujiga🥰😘😘👍🏻_ ___________________ ~Book 2~ 👉🏻2⃣6⃣ ...................MC yafara shelanta cewa wannan bikin sunafa an had'ashi da bikin birthdays ne, domin ranar haihuwar yaran tai dai-dai da ranar haihuwar iyayensu, dan haka suka had'e wannan biki a yau guri d'aya, dan a waccan ranar murnar haihuwar bata basu damar yanka cake ba😂. Dariya aka sanya, saboda a yanayin barkwanci mc yayi maganar, Galadima kam ai kod'an murmushin ma baiyiba, garama Yaa marwan ya murmusa. Galadima ya kalli munaya, cikin maganar nan tasa mai kamada an masa tilas yace, “Kina da sa'a”. “Sa'a kuma?”. ‘Munaya ta fad'a cikin yanayin mamaki’. Harya bud'e baki zaiyi magana sai kuma ya basar. ganin haka itama Munaya saita sharesa, dan takula yau y'an mulkin ne a kansa. Saida ya gama shan k'amshinsa sannan yace, “wannan ne karon farko da Sameer yata6a bikin birthday”. Baki munaya ta d'an ta6e, tana fad'in “Humm, kodai y'ay'anka suna da sa'a?, domin dai a dalilin haihuwarsu ne kayi”. “ko kina jealous ne?”. ‘yay maganar cikeda basarwa’. tura baki tai gaba. Idonsa akan yaransa yace “idan kika bari na kama wannan bakin a wajennan humm.” ya cije lips d'insa. Sanin k'aramin aikinsane ya akaita abinda ya fad'a d'in ya sata saurin gyara bakinta , tad'an saci kallonsa, ya wani Fiske tamkar ba shine yay maganar ba ma. ita dai tana mamakin kasaita da izza irinna bawan ALLAH n nan, jinin mulki yana da matuk'ar k'arfi a jikinsa. tunaninta ya katse lokacin da hankalinta ya koma kan abinda ke faruwa a hall d'in Khaleel da Aiyaan, Aryaan ne suka turo cake mai k'yau da tsari, Wanda yasha kwalliyar White and Golden, an saka sunan Galadima da shekarunsa 31years a sama, a jikinsa kuma daga can k'asa ansa Muhammad Sameer (Dadyn Triples), an d'ora candlestick🕯guda uku, Sai hotonsa da yay k'yau sosai cikin shigar sarauta. Galadima ya kalli Sauban da Samha, yasan dai wannan aikinsu ne, k'in kallonsa sukayi sukam ballema suyi gamo da tsarabar harara😅. Ita Munaya ma sai yanzu taga Su Aiyaan, batayi zaton anzo da suba, tunda bataga yaran gidansu k'anana ba a waje, sai manya maza da matan Na ma'auri. MC ya taso k'eyar su Khaleel har inda su Galadima suke zaune, kowanne aka d'ora masa yaro d'aya, suma mik'ewa sukayi bisa umarnin MC d'in, a tare suke takawa ita da shi, sai k'yastu ake zuba musu, masuyi a waya da masu cameras, sai gidajen TVs d'in da aka gayyata suna nuna live. Sun Isa gaban cake d'in hannunsa rik'e da sandarsa, kaikace sarkine da kansa (gaskiyar Munaya Galadima akwai k'asaita, Kodai sarkin da Kansa ya shafa masa lafiya🤭). Bayan anmasa wak'ar happy birthday yayma munaya nuni waita hura candles d'in. Cikin k'asa da murya tace, “yalla6ai bafa haka akeyiba, ka hura abinka da kanka”. Hannunta ya kama ya matsa yanda zataji zafi, yace, “zakiyi?”. Ai baima kai k'arshen maganarba ta risina ta hure wutar, hall d'in ya d'auki tafi. cake d'inma dan rigima wai saidai su yanka tare. “haba yalla6ai, saikace Na wani aure?”. Cikin ta6e Baku yace, “wama ya sani kona auren ne”. Shiru tayi bata tanka ba, dan itadai fatanta a rabu lafiya, hannunta ta d'ora kan nasa dake rik'e da wuk'ar suka yanka taren. nanma dai tafin akayi. Ya lakata a d'an yatsa ya duk'o gasu Aiyaan ya daddan gwalama yaransa a hanci da kumatu, sannan ya juyo ga Munaya da haushi ya kamata, ai ita yakamata ma yafara sawa ba yaranba. Itama akan hanci ya shafa mata yana fad'in “yalla6iya haushi kikajine?”. Kafin tabashi amsa yakuma lakata ya shafama Aryaan Khaleel da Aiyaan suma. Dole munaya ta had'iye maganarta. Amma ta kudiri saita rama. Itama itada Munubiya k'aton cake nasu aka kawo kalar pink and White , Munu da Yaa marwan suka taso a tare. Munaya da Munubiya suka rungume juna suna maijin dad'in tunawa da ranar haihuwar su, shekaru 20 cif da kwana 7. Sun yanka cake atare suka sakama juna abaki kad'an-kad'an, sannan kowacce cikin son tsokana ta lakatama y'ar uwarta a fuska suka rungume juna suna dariya da k'ananun hawaye, suncika shekaru 20 ranarda yaransu sukazo duniya suma. Abin ya birge mutane, Munubiya ta matsa ga mijinta ta saka masa a baki kad'an, cikin murmushi yace, “happy birthday my heartbeat ”. Tace, “Thanks you my luv” k'arasawa tayi ta sakama yaran munaya dasu Aryaan a kumatu, sannan ta sakama nata yaran. Munaya danta rama abinda Galadima yamata, takai cake bakinsa kamar zata bashi, saida ya bud'e baki saita juya ta shafama yaran Munubiya a kumatu, sannan nata. Yanda Galadima yay shock akan abinda Munaya tamasa sai mutane suka sanya dariya suna tafa mata, mai martaba da papi ma dai saida suka Murmusa. Munaya ta dawo ta dangwalama Galadima akan hanci tana masa gwalo. Shi kansa baisan k'asaitaccen murmushin ya kufce masaba, ya saka handkerchief ya goge yana dawowa mazauninsu ya zauna. Daga nan aka fara gudanar da wasa, Comedian's sukazo sukad'an saka mutane dariya, saikuma mawak'a da suka bada nasu salon. Tun da Galadima ya fara yawaita kallon agogon hannunsa su Muftahu duk suka sake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92