Chapter 87
Chapter 87
komai a wajemsa. Bayan na warke nadawo gida kuka saka aka saceni kaida Muftahu, na koma gida mangariba ta rufa a ranar, ashe wai baba mai kanwa yaga sanda na shiga gida a firgice, sai'a washe gari ya aiko a kirani, innarmu da Munubiya sunyi mamakin kiran, dan cayay Hussaina taje, (shi dama baya kiranmu Munubiya da Munaya, sai Hassana da Hussaina). Haka na saka hijjab naje, a yau baiyi wasan daya sabayi da niba, kai tsaye yafara maganarsa”. _“Hussaina jiya daga ina kika dawo a firgice?”._ “A tsorace na kallesa, dan lallai tsohonnan yafara bani tsoro, dama tun muna yara mukanji ana cewa tsoronsa akeji, saidai bamusan manufar tsoronba, murmushi yayi yana gyara zama da cigaba da gyaran wasu takarsu Dana tarar yanayi, yace___”. _“karkiji tsoro, nimai taimakonki ne gwargwadon abinda ALLAH yabani ikon sani, dan haka ki fad'amin gaskiya_”. “dak'yar na iya had'iye yawu, sannan na fad'a masa abinda yafaru tsakanina daku. Murmuahi yay mai matuk'ar sauti, wanda ya bayyana fararen hak'oransa da basu wuce goma sha ba da suka rage, wad'anda a kullum zaka sameshi da ashuwaki yana d'abbak'a sunna, yace___”. _“Hussaina ni bazance ki amince ko karki aminceba, saidai nabaki dama kije ki duk'ufa rok'on ALLAH, a cikin kwana ki biyu rak ALLAH zai nuna miki mafita da abinda zai zama alkairi a gareki, sannan karki sanarma Hasaanar ki, danna kula bazata amince ba tacikin sauk'i, tashi kije”._ “A wannan ranarma haka baba mai kanwa ya sakani cikin rud'ani, nazo dukna hana kaina nutsuwa da kwanciyar hankali, saidai nabi shawararsa ta mik'a kukana ga Ubangijin al'arshi, dan shine gatana kuma fitilata, a kwana na biyu kuwa saiga dalilin dayasani amincewa da buk'atarka ya faru, na amince maka badan hankali na ya kwantaba. tunda kuma lokacin baba mai kanwa bai kuma min maganar data shafi auren ba, harma na d'auka duk mafarki nayi, har maganar da mukayi d'in dakai. Saida ana gobe d'aurin aurenmu da safe na fita yin wani Abu na gamu da baba mai kanwa, shine yace na biyoshi gida. Mun Isa gida a d'akin zaurensa, yabani wasu abubuwa dabansan mineneba na sha, sannan yabani turare kashi biyu, yace ni 1 Munubiya 1, yace____” _“Hussaina kimin wata alfarma mana?”._ “A sanyaye nace kabani Umarni akwai baba. Yay murmushi da fad'in___”. _“ALLAH ya yimiki Albarka Hussaina, ina tausayinki ta wani fannin, ta wani fannin kuma murna nake tayaki, duk abinda nake hasashe a kanki nasan zaki iya, dan kinfi y'ar uwarki wayo, ni dake zamu had'a kaine wajen fidda mahaifinku a sark'ak'iya, su a gangancinsu sun tozarta kune domin tunzura mahaifinku da karyar masa da zuciya, amma basusan Ubangiji mai hikima baneba, yafisu sanin akan abinda su bai basu damar saniba, kiyi hak'uri inata miki magana a cirkud'e, zaki fahimci komai anan gaba kema, alfarmar da zakimin shine dukkan abinda kikaci karo dashi a rayuwar aurenki ki sanar min shi, insha ALLAH Zan miki fashin bak'i gwargwadon abinda na fahimtar nikuma, maganar zaman aurenku da yanda kuka ginashi kuma ya rage naku bayan warwarewar komai, wannan ba hurumina baneba, tashi kije, daga nan dai zamu dinga tayaku da du'ai”._ “Dukda banida tabbacin mijin dazan aura wannan magana tashi tamin nauyi da wahalar fasaara, da y'an gidanku suka kai lefena kuma saina kuma tsintar kaina a rud'ani da firgici, ban kuma fita daga wannan firgicinba har aka kawoni wannan masarautar. Saka pills da Muftahu yayi mana shine k'alubale na farko dana fara cin karo dashi Wanda nake k'yautata zaton baba mai kanwa ya hangomin, hakanne kuma ya sakani tada hankali nace nafasa auren, dan a zatona kun had'a bakine da Muftahu, amma sai maganar tafiya India ta datse dukkan hanzarina, ko kad'an banyi yunk'urin sanarma baba mai kanwa wannan batunba, dan aganina baya cikin abinda shima zaiso Sani. Idan baka mantaba a lokacin da ka kaini sallama gida da kuma gidansu Munubiya ka barni a can?”. Kansa ya jinjina mata idonsa a lumahe ya jingina da gado, kai kace ba saurarenna yakeba barci yakeyi. Ajiyar zuciya na sauke, na cigaba da fad'in “Aunty Salamah tazo gidan ta sameni ai, saboda Munubiya ta sanar mata zaka tafi dani, wannan itace damar farko dana samu na rok'onta yimin bincike akan Muftahu da Saleem yaronka na plaza, (abinda yasa Saleem yashiga Layin zargina saboda randa abinnan ya faru bayan fitowarmu shikuma naga ya fito daga tsakanin wasu motoci a firgice, dayake a time d'in bamusan mizai faruba ban kawo komai a rainaba sai washe gari, danayi bincike a kansa saina gane yaronkane na shago kuma amintacce) daga ita har Munubiya a lokacin basusan dalilina nason amin bincikenba, saidaga baya Munubiya ta fiskanci komai, dayake tanada kaifin basira, amma batasan tsakanina da baba mai kanwa ba. mun tafi India nabar Aunty salamah da wannan aikin”. Knocking k'ofa da akayine ya saka Munaya yin shiru bata cigaba ba, na kalli Galadima da har yanzu idonsa a lumshe, batareda ya bud'eba yabada izinin shigowa, yasan dai bazai wuce Sauban ba. Samha ce ta shigo, ta risina tana gaidashi, sannan tace, “Aunty Amaturrahman ta tashi itada Abduraheem”. Yunk'urawa nayi zan mik'e galadima ya katseni ta hanyar fad'in “jeki kawosu”. Na kallesa da mamaki, yayinda Samha ta fice abinta, “amma yalla6ai darefa yayi, mubari mu k'arasa zuwa gobe mana?”. “uhm-uhm”. Kawai ya fad'a. Shiru nayi nakasa cewa uffan, har Samha da Sauban suka shigo d'auke da yaran duka uku, kar6ar Abdurraheem nayi, dan yaron tausayi yake bani saboda rashin kuzarinsa (karku manta har Yanzu Munaya batasan yaron yanada irin ciwon mahaifinsa ba), su kuma Sauran ya kar6esu. Sauban da Samha suka fice sudai suna tunanin wannan zaman nasu, komi suke tattaunawa oho. Bayan fitarsu a cikin gyale na fara shayar da yaron, Galadima dai baice dani uffanba, sai kallon yaransa kawai yakeyi, na cigaba da fad'in “Abu na biyu dana fara cin karo dashi shine ganin Abie a halin daya tsinci kansa, wannan lamari ya d'aga hankali na, amma a lokacin banida wayar kiran baba mai kanwa na sanar masa, ina tsoron na saka a wayarka kuma ka gano wataran, sai kuma tarihin masarautar nan da Momma ta bani.......” Cikeda mamaki Galadima ya kalleta, dak'yar ya bud'e baki cikin yamutse fuska yace, “Momma!?”. Nace, “eh lallai Momma da kanta, dukkan rayuwar dakasha ta gwagwarmaya ta sanar min, tundaga yarinta zuwa girmanka, ta sanarmin hakanne danna lura da abinda ban saniba a masarautar, kar wani yayi amfani dani wajen cutar dakai. Bayan nan babu dad'ewa kabani waya, daga nan nasamu damar sanarma baba mai kanwa sirrinan guda biyu, ciwon Abie da tarinku. shine yabani dukkan addu'oin da maganin daza'a nema arink'ama Abie, kuma Alhmdllh munakan ganin haske. daga nan kuma na cigaba da samun haske game da dukkan Motsin Muftahu, amma kuma babu wani abinda bai daceba ko cin amana tattare dashi, damukaga mun shiga kokwanto saimuka saka Sarkin Mota da Saleem suka sace manashi a randa kaje d'akkomu a airport ni da Sauban lokacin da Abba yay accident ”. “ya salam! Kina nufin kece?”. Murmushi na masa, nace, “kwarai nice, hakan shine kawai mafita agareka damu kanmu, dan satar nashi ya zame mana haske, aunty salamah taje masa a amatsayin d'aya daga cikin matan Abie, ta hakanne kuma muka ji sunan Harun a bakinsa. daga nan muka sakama Harun ayar tambaya, su Ameer suka cigaba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92