Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 71

Chapter 71

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya bashi hannu sukayi musabaha, k'aramar takardar dake mak'ale a hannunsa ya sakarma galadima a hannu. Kallonsa galadima yayi, sai yay masa murmushi yana signal da ido alamar ya duba. Galadima bai ce komaiba ya cigaba da abinda yake ya basar da takardar. Muftahu kuma ya koma cikin su Harun aka d'ora hira, tamkar babu abinda ke damunsa. Galadima baibi takan takardar da Muftahu ya basaba har tsawon wasu adadin mintuna, sannan ya bud'e ya duba. _Ranka ya dad'e ina buk'atar muyi magana kafin a zauna wajen walima, magana mai muhimmanci please._ Iya abinda ke jikin takardar kenan. Galadima ya d'an ja eyeglasses d'insa k'asan ido ya kalli Muftahu, cije lips nashi yayi yana janye idonsa. Ya sauke k'afafunsa yana d'ora laptop d'in saman kujerar, ya d'auki ruwan gabansa yana sha da maida hankali garesu. jin hirar tasu ta y'ammata ce sai ya zuba musu ido kawai bai saka bakiba, dan shi dama ba'a wannan hirar dashi tun can da, suma duk sunsan haka, shiyyasa ko suna shirmensu basa sakoshi. Ganin zasu saka masa cinwon kai saboda hayaniyarsu Na Neman yin yawa saiya mik'e d'auke da Laptop d'insa. Duk kallonsa sukayi, Zayyan yace, “ina zuwa daddyn Triple's?”. K'aramin tsaki yaja, da k'yar ya bud'e baki yace, “zaku samin ciwon kaine, zanje nad'an huta kafin time yayi”. ya k'are maganar da kallon agogon hannunsa. Matawalle yay murmushi yana salute nashi, shima murmushin ya masa yana kaimasa rankwashi, ya kauce gefe yana murmushi, (dayake shima bai cika hayaniya ba). Wuce warsa yay cikin takun nan nasa Na izza da k'asaita, da sauri wasu yaran masarautar dasuka had'a tasu dabar agefe biyu aciki suka taso suka k'ar6i laptop d'in hannunsa saboda girmamawa, ya mik'a musu yana murmushi, yana gaba suna binsa a baya, sai zuba masa surutu suke akan shagalin daza'a sha yau, shidai murmushi kawai yake musu babu magana, basu damuba, dan kowa yasan halin galadima a masarautar nan, haihuwar nan ma wasu da yawa zasu iya cewa sunga hak'oransa a waje. duk inda suka gitta ana kwasar gaisuwa, bayi kam zubewa suke domin girmamawa a garesa. Har sashensa suka masa rakkiya, sarkin mota ya kar6a laptop d'in ya k'arasa masa da ita zuwa ciki.. Baibi ta ainahin k'ofar da zata kaishi babban falonsu ba, saiyabi wata k'aramar k'ofa da kai tsaye nasa sashen zai shige basai mata y'an suna sun gansa ba. A falo ya iske Sauban kwance yana barci, da alama yagama yawonsa ne gajiya ta makesa, da kallo Galadima ya bisa, amma dan ya tabbatar da lafiyarsa saiya d'ora yatsunsa biyu a wuyan Sauban d'in, babu zafi, ya maida goshinsa saiyaji zafi sosai, Galadima ya girgiza kai, yasan dama ba lafiyace zata saka Sauban barci a irin wannan lokacin ba ana wannan hidimar. Bai tasheshi ba ya shige cikin bedroom, zama yay a bakin gadon yana cire bottom d'in rigar guda uku, ya huro isaka daga bakinsa yana zamewa ya kwanta batareda ya cire rigarba, zuciyarsa tana ta jujjuya mi Muftahu yake nufi ne? wace magana zasu tattauna?. waya ya jawo da nufin kiransa, sai kuma ya fasa, jefar da wayar yayi yamik'e yana ida cire kayan gaba d'aya. ya shige wanka. ya ja adadin wasu mintuna masu tsayi kafin ya fito sanye da bathrobe fara sol, sai k'aramin towel a hannunsa yana goge fuskarsa zuwa wuyansa. Yana tsaye gaban mirror zai fara shafa mai ya jiyo ana knocking d'in k'ofar falonsa, Computer d'in daya ajiye wadda yake kallon kowane 6angare na sashen daga cctvs cameras d'in daya zagaye ko ina, tun zuwan dayayi Na k'arshe ya saka akayi masa wannan aikin, sannan ya d'auki mataki akan waccan cctv d'in da Munaya tamasa hannunka mai sanda da ita. Sarkin k'ofa ya gani, sai kuma Muftahu daga can waje alamar yana jiran iso ne. Guntun tsaki Galadima yayi, ya fito zuwa falo, Sauban dake barci ko motsi baiyiba balle yasan ana knocking d'in. yana daga tsaye yabama sarkin k'ofa izinin shigowa. Cikin girmamawa yace, “ranka yadad'e yalla6ai Muftahu ne ke Neman iso”. Da hannu Galadima ya masa nuni da ya shigo. Sarkin k'ofa ya amsa da to sannan ya fice. Komawa Galadima yay ciki yacigaba da shafa mansa, saida ya gama tsaf sannan ya zira jallabiya Brown ya fito. A falo ya iske Muftahu zaune yana control d'in television da remote. Galadima ya zauna a kujera mai zaman mutum d'aya, sai wani d'aure fuska yake. Muftahu bai wani damuba, dan yariga ya saba da wannan ai. Kallonsa Galadima yayi cikin lumshe ido yana fad'in “Mike faruwane?”. Ajiye remote d'in Muftahu yayi, ya kalli Sauban dake barci. d'an ta6e baki Galadima yayi, yace, “karka damu, kayi maganarka kai tsaye kawai”. Cikin jinjina kai Muftahu yace, “Ok, babu abinda ke faruwa saidai shirin faruwar kam, Ranka ya dad'e bamuda isashen lokacin wata magana mai tsawo yanzu, saidai ga wannan takardar ka duba, so yanzu wannan ne akan ga6a, shine yakamata mu d'au mataki akansa, daga baya komi kenan namaka alk'awarin warware makashi, fatana dai ka fahimci wannan d'in saboda had'arinsa”. Kar6ar takardar Galadima yayi, ya d'auki medical glasses d'insa daya ajiye a teble glass d'in dake gefen haggunsa ya saka, duba takardar yay a tsanake, cikin wani yanayi dake nuna tsantsar tashin hanki yace, “Muftahu wannan maganar gaskiya ce kokuwa? karkamin wasa da hankali a wannan karon dan bazan d'aga maka k'afa ba a wannan ga6ar alwashi nane”. Murmushi Muftahu yayi, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in “Nabaka wannan damar, inhar kayi gamo da sa6anin hakan karka barni da numfashi ranka ya dad'e”. Wani shegen Murmushi Galadima yayi, yamik'e d'auke da takardar ya koma bedroom batare da kuma kallon Muftahu ba. Tausayin Galadima ya kama Muftahu, mik'ewa yay shima ya fice. Jefar da takardar Galadima yayi akan gado yana taune lips nashi tamkar zai huhhudashi, wata irin suya zuciyarsa ke masa, lallai dolene ya jinjinama Munaya, dan ta taka rawa wajen shagaltar dashi wanene shi? minene burinsa?, ganin tunani bazai masaba yatashi jikinsa Na rawa yafara wasu had'e-had'en abubuwa, waya ya d'auka ya kira Ayusher, ta d'aga cikin hanzari tana mik'ama Munaya dake shayar da Amaturrahman data tashi daga barci tana kuka. Kallonta tayi da mamaki tace, “wace Ayusher?.......”. Galadima ya katseta da fad'in “ki kawomin kayanda su Abdurraheem zasu saka”. iyakar maganar da yay kenan ya yanke wayar yana cigaba da latse-latse, zuwa can kuma ya ajiye ya mik'e yana cire jallabiyar jikinsa. Baki sake Munaya tabi wayar da kallo, mike damun galadima haka? Muryarshi irin wadda tasan asalin galadima ce, hakan na nufin akwai matsala kenan? to mine zaiyi da kayan da yara zasu saka?. batada mai bata wad'an nan amsoshin dan haka ta mike tana ajiye Amaturrahman d'in, aiko ta fashe da kuka an cireta bata k'oshiba, tsaki Munaya tayi tana fad'in “ai saikiyi tayi, ku matsala ubanku matsala mutum yarasa wazai kama. Ayusher da Aunty Salamah suka kalli juna suna gumtse dariya. Gyale taja ta lullu6a, dama tasaka doguwar rigar matirial kafin dai time ya k'arasa. ganin zata wuce yarinya na kuka Auntu Salamah tace, “dawo ki d'auketa mana, idan kinje can saiki bata nonon”. Tamkar Munaya zata saka kuka haka ta dawo ta kwashi Amaturrahman ta fice tana k'unk'uni. A falo ta iske Sauban Na barci, wucewa tayi cikin bedroom d'in kanta tsaye, amma saida tayi sallama

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});